*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*Maimaici
Start on 28/5/2020
End on 23/6/2020
Tuesday, 2:50pm*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*Episode 50
"Wannan wanne irin rainin wayo ne haka? ke kullum cikin uzuri bakya ma gajiya da kwakwalo karya kullu yaumin kina fada , toni gaskiya bazan daukar maki wannan ba dan haka, kuma idan kinga dama ki sanar da Daddy cewa gobe Insha Allah idan Allah ya kaimu bayan ansha ruwa magabatana zasu zo neman aure a saka rana saboda ayi komai a gama nan da d'an wani lokaci, Ina fatar kinfahimta.!"
Bai ma tsaya jin ta bakin ta ba, Kit ya yanke kiran.
Kai tsaye taji wani irin hadadden farin ciki ya yi mata zuwan ba zata, cikin tsantsar farin ciki ta mike zaune daga kwanciyar da take tare da mugun jin dad'in zancen da take jin shi tamkar albishir a wajenta.
Kai tsaye ta tashi tsaye a saman gadon ta hira sama ta buga wani irin mahaukacin tsalle kamar wata tsuntsuwa, tare da yin wata irin arniyar shewa ta farin ciki sannan ta shiga sharb'ar rawa, dik a saman gadon.
Sai da ta kusan b'ata wani lokaci mai tsawo tana haukatuttan ta najin dadi masu cike da farin ciki, sannan ta samu damar tsaida abin, ta sauko daga saman gadon, ta zauna
kereriyar gado saiti da mudubin dake cikin d'akin tana ta famar zuba maganganu barkatai kamar wadda ta kamu da lalurar tabin hankali sannan ta gyara fuskarta cikin wani salo marar misiltuwa ta ce, "Shegiya Balkisu lallai ke 'yar macijiya ce a cikin rame, kin sake baya kin kama gaba, kin take manya kin zauna lafiya, kinzarce maza balantana matan, ke daya ce tilo a cikin zuciyar Mukhtar, ki kwantar da hankalin ki tunda yanzu kin fara cimma nasara a tattare dake, burin ki a yanzu yana daf da cika, musamman a lokacin dâ zaki tarar da kanki tsunbulbul a cikin gidan Mukhtar a matsayin Amarya kuma Uwar gidan sauratar mata, Hmm a lokacin da nake tunanin wasar zata fara aiki, hunhunhumm, Hajiya'Lamrat kenan! ki kuka da kanki tun yanzu kafin lokacin da zan shigo gidan d'anki domin farautar ki, sabida haka nayi maki alk'awarin zan zamo tamkar annoba a cikin rayuwar ki, Sannan zan zama tamkar haki a mokogoro a gare ki da dik wani wanda yake tunanin zai iya karawa dani, wlhy! wlhy!! sai kin gwanmace barin duniya a gare ki bisaga zama cikin ta,domin na dauki alwashin dawo dake a cikin hayyacin ki har sai na tabbatar da kin gama raina kanki da kanki sannan in aika ki k'iyama domin ni Balkisu ban shirya zama da uwar miji ba a halin yanzu sai dai ayi biyu babu k'unar bak'in wake kenan, inji masu iya magana, cikin tsalle ta tashi tare da mugun bawa kanta lambar yabo dari bisa dari, ta mike tsaye afujajun Ta nufi b'angaren Ammie, sai dai kuma tayi rashin sa'a domin bata sameta anan ba, cikin mugunjin haushin abin Ta ce yanzu haka tana can wajen tsohon ta suna sheke ayar su su ko cikin Azumin ma ba zasu iya daukar hutu ba.Nan dai ta fiddo wayar ta ta lalabo number Ammie ta kara a kunnen ta.
———«»«»«»———
_Kwance suke a saman gado cikin wani zuzurutun shauki ita da Mai gidan na ya suna sharholiyar su irin nasu na ma'aurata cikin wani irin yanayi mai cike da daukar hankali
