*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*EPISODE>>>38
Nan da nan Ammie ta zame jiki ta fadi kwance a k'asa reram kamar wata matacciya, sai dai kuma wani abin ban haushin Suma take son tayi amma ta kasa, sai jin tayi ya sake cewa "Ayyaaa Madam aiko da kin rufama kanki assiri kin tashi domin nan ba wajen kwanciya ba ne.!"
Balkisu kam da tun dazu ta riga da ta gama sank'arewa a waje guda, domin k'afafuwan ta da dikkan ilahirin jikin ta sun riga da sunyi sanyi kamar wadda bata da lakka haka take jin kanta.
Batasan lokacin da ta ce "Ashe Zaz...Zazz...Zakara yana..magana...?.!"
Kan ta kaiga rufe bakin ta, a take taji an bata amsar tambayar ta cikin ruwan sanyi kamar haka.
"BA GASHI YANZU KIN GANI BA.!"
Acewar Malam Zakara_ Ita dai kam Ammie kwance kawai take, ta kasa Suma kuma ta kasa tashi...a halin ma yanzu ta gwammace da ace mutuwa ce tayi da ta futa bisa ga ta ci gaba da fuskantar wannan bak'ar WAHALA'r akan abin da bai taka kara ya karya ba.
Boka Mintsinkyu da tun dazu haushi😡ya riga da ya gama turmuk'e shi sai Jin suka yi ya ce "ki tashi.!"
cikin wata kalar murya, aiko ba tare da bata lokaci ba Ammie ta mik'e zaune, Ita ma mamakin da take yi kenan ya akayi ta mik'e zaunen!Sai ganin wannan bakin Zakaran tayi kwance kamar Jinjiri a saman hannayen ta, Nan da nan taji hannayen ta sun fara makarkata gashi kuma ta kasa yadashi k'asa.
Nan dai ta danyi k'arfin halin tambayar boka Mintsinkyu da cewa "A INANE WAJEN?." Kai tsaye ba ko wata lankwasa domin ita a halin yanzu tadan fara jin jarumta tana d'an tsokalota.Sai da ya yi kamar baiji ta ba, Sai can cikin wata irin Arniyar murya suka ji ya kira wani Aljani mai suna LUDOS, tin kafin su Ammie su kaiga cewa HA sai ganin wata Mummunan halitta su kayi mai kama da Jab'a, saidai kuma ita wata irin basa mudiyar halitta ce dake tsangal, kan su kaiga cewa wani abu tini sukaji Boka Mintsinkyu ya soma ce masu "Wannan shine abokin tafiyarku da zarar ya'aza ku ga hanyar zai da wo, wannan bak'in zakaran dake saman hannun ki shi zai ida k'arasar daku.!"
Ammie na kallon wannan makeken Zakaran, taga sai sharb'ar kuka yake harda su kwalla, daga bisani kuma sai ya b'arke da wata irin dariya mai saurin kod'a zuciya sannan ya ce " Idan kuma kuka kauce hanya kuma fa za'a kauce maku.!"
Wanda aka kira da LUDOS yadan rusunar da kan shi k'asa a gaban Boka Mintsinkyu da alamun girmamawa ne a gare shi.
kafin su Ammie su ce "Ha" sai tsintar kansu su kayi a cikin wani Mahaukacin Jeji wanda yafi wanda suka baro bala'i, Sai dai dik yawan duhun da ke cike a cikin wannan Jejin bai hana su hango wani duhu-duhu ba ya nata famar tunkaro su kamar Kurwar mutum, amma da an kusa kawowa kusa da su kuma sai suga ya b'ace .
Haka dai suka ci gaba da tafiya tare da c dube duben da suke ko da suka halkanta ba suga LUDOS ba, nan da nan hankalin su ya yi mummunan tashi, Ammie sai famar b'are bakinnan take kamar hanta-botso tana kwalawa Ludos kira kamar mai kiran sallah, sai dai shiru babu shi babu labarin sa.
_Balkisu ce ta d'anyi k'arfin halin cewa "Wallahi Ammie kin kashe mu wallahi nayi Nadamar biyewa son zuciyar ki da nayi.!"
Nan da nan kwalla masu zafin gaske na wahala suka fara wanke mata fuskar sharkaf, sannan tak'ara da cewa "Ni gashi tun ban kai ga aikata komai ba tun yanzu nafara ganin ishara, Wallahi Ammie kin cuce ni!"
Daganan sai ga wani azabebben kuka mai rad'ad'i bak'in ciki ya gwabce mata nan take, maganar da taso yi ma taji ta kasa k'arasawa.Sosai Oga Ammie ta yi bala'in yin nadama kuma ta tausayawa halin da diyar ta ta take ciki domin tasan wannan ne karo na farko da ta tab'a zuwa da ita wajen wani boka domin cikar burinta, ita ko wannan ba shi ne karonta na farko ba domin ta riga da ta saba daman sai dai dik biyar bokayen da take yi bata tab'a haduwa da irin wannan tantirin Bokan ba a dik tsayon lokuttan da ta dauka tana biyar ko wanne irin boka Idan ta samu labarin kwarewar shi ta wajen aikin sa, tana cikin yin wannan tunanin ne taji alamun fitowar muryar Zakaran yana cewa "MUTAFI KARKU K'ARA B'ATA MANA LOKACI!"
Ya datse wannnan maganar ne tare da Jan wani mahaukacin tsaki_Kafin su kaiga cewa wani abun domin a halin yanzu ji suke kamar su shake wuyan wannan dakaten Zakaran har sai ya mutu su futa akan haushi, sai dai kuma suna bala'in tsoron aikata hakan ne domin gudun abin da zai iya biyowa baya dan shi kanshi Zakaran kallon shi kadai idan kayi abin tsoro ne a gare ka.
kafin suyi wani yunkurin cewa abu, tini su kaga an dalla masu wata kafurtacciyar fitila a saman idanuwan su kamar ta mota ana k'ok'arin kashe masu idanuwa da wannan uban hasken.
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
