011

169 14 0
                                        

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
_{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

➡️011

Ta bangaren Uncle Muhammad kuwa yana isa a cikin Office d'in sa  ya zauna ya dinga tunane-tunanen yanda yaga Mahaifiyar shi d'ogogo-d'ogogo a saman cikin ruwan Cikin Fatim kamar wata Jaririyar yarinya kuma dik da ta ga halin da take ciki amma bata raga mata ba  ko kuma taji wani abu a ran ta wai shi tausayi, yana cikin wannan tunanin bai san lokacin da ya fidda maganar a fili ba ta fito cikin wani salo na tambayar kan shi da cewa
       "Anya kuwa Hajiya ta nada imani kuwa?." kafin ya ankare sai Jin ya yi an amsa mashi amsar tambayar shi kamar yanda Ya yi ta, da cewa " tabbas kuwa Hajiya ke da Imani fiye da yanda kake tunani.!"

Cikin hanzari da firgicin jin wannan amsar domin shi dai a tunanin shi babu kowa a cikin office dinsa sannan kuma da ya shigo ya kulle shi tsaf  balantana yaji alamun shigowar wani a cikin d'akin,

Nan take ya yi k'arfin halin maida hankalin shi a wajen da yaji fotowar wannan  domin ya ida tabbatar da sautin muryar a cikin office dinsa ne take tashi ko kuma a wani wajen dai na daban dan ya naji a jikin shi  yasan wannan muryar sai dai kuma bai ida tabbatar da itadin ce ba, sabida yana da tabbacin mai irin wannan muryar  yanzu haka yana can nashi bangaren

Sai dai da mamakinsa maimakon  ganin wata bakuwar fuska kuma sai yaga sananniyar fuska a gare shi

Da hanzari Ya sauke kansa kasa domin ganin wanda ya hango ba karamin tashi hankalinsa yayi ba, cikin sauri-sauri gaban shi ya shiga duka ukku-ukku kamar ya tsage ga kuma wani zazzafan gumi dake saukowa a saman fuskar shi dik da kasancewar  sanyin AC da ya gama karad'e wajen  Sai dai hakan bai amfane shi da komai ba illa ma gumin da ke  taso ma gabadai ilahirim jikin shi,

Uncle Mustapha ne Yayan shi  dake Kwance a saman doguwar kujera wadda ke cikin office din kasancewar dik su nada key's din office din junan su yasa ya baro nashi office din yadawo cikin na Uncle Muhammad yazauna jiran shi domin akwai wata muhimammiyar maganar da yake son su tattauna a tsakanin su akai,

Cikin wata kasalalliyar murya yake mai magana kamar haka,

"Wato Muhammad dik abin da kaga Hajiya  nayi ma Fatima ta nayi ne domin ta san  dan ta isa da ita ne karka dauke shi a matsayin zalinci domin Hajiya ta fika sanin ko wanne irin hali na Fatima ciki da waje domin a hannunta ta tashi tun tana 'yar kankanuwar ta, sannan kuma bawai ba wai tsana ce ke saka ta yin dik wadannan abubuwan ba sai dan karin tarbiya sabida haka bai kamata ace ka damu kanka akan wannan abin ba, Idan ma har kana tunanin wani abu ne to muma kan mu wani irin duka ne bamu sha ba a lokacin mu na yarinta agurin Hajiya ba, so ya kamata ace ka duba wannan al'amarin sosai da fuskar fahimta, sannan Nima dazu bayan fitowa ta Al-Amin ya kira ni  ya gayaman komai sannan ya ce ya gyara wannan jimuwar ta kafarta ya bata magani ta sha sannan umma, wato (Hajiya Saudat) ta dauke ta izuwa dakin ta.

Uncle Muhammad sosai ya gamsu da maganar Yayan shi sai dai ta wani bangaren kuma yana maijin haushin shi  akan abin da yake yi ma Fatima  sabida suna ganin kamar bai damu da ita ba ne shi ya sa suke yi mata wannan danyen hukunci domin wani lokaci da shi ake taruwa ana dukan ta ba bisa ga wani dalili kwakkwara ba Ko tsoron Allah baya ji, shi da diyan shi baya son yaga ko Sauro baya son yaga ya tab'a mashi su, wanda hakan  yasa ya hana masu shiga cikin gidan kakannin su dik dan sabida Hajiya Kaka  sai idan har aiken su akayi amma kaji yanzu dan ba diyar shi ba ce yazo yana wad'an su maganganu maras dalili."  yana cikin yin wannan tunanin ne Uncle mustapha ya katse mashi hanzari wajen cewa "Dama ni maganar da ta kawo ni wajen ka ba komai  bane illa naji wani k'ishin-k'ishin ne da yake ta yawo  dangane da Fatima shiyasa to ina son daukar mataki da kaina ne shiyasa na ce sai na gayamaka tukunna naji komai ka ce?."

Uncle Muhammad ya ce "Ai ba komai ba ne dik abin da ka yanke daidai ne ai kaima ka isa da ita."

"Eh haka ne kam, dama yanzu wani hali ne marar kyau da ta dauko nabin k'awayen banza suna son su lalata mata rayuwa a banza, tunda yaro dama tun yana d'an k'ank'anen shi yake koyon iskanci."

Cikin sauri Uncle Muhammad ya kallo shi da yanayi na rashin fahimta domin a halin da yake ciki yana matuk'ar buk'atar k'arin haske, sannan Ya ce "kamarya kenan?."

"Sai da Uncle Mustapha  ya d'an sake wani murmushin shi na gefen baki sannan ya k'ara gyara muryar shi ya ce "Kana nufin kace man  dik abin da yake faruwa baka sani ba? hmn to shekaranjiya Malam Sa'idu yazo ya same ni har office dina yake gayaman ya ganta tare da yaran gidan Alhaji Muttak'a (wato wani makwabcin su) kuma kasan yaran gidan muggan 'yan iska ne banda  zance a kofar gida da samari da kuma shashanci da su ba abin da suka aje kuma iyayen su na sane suka kyale su,"
       Uncle Muhammad ya ce "Yaya wai wanne Sa'idu kake nufi ne?."
             ya ce "Malam Sa'idu mai shayi mana! makwabcin mu ko baka gane shi ba ne, wanda ga gida ga gida da shi da gidan Alhaji Muttak'a."

Sai a sannan Uncle Muhammad Yaji ya sauke wata lafiyayyar ajiyar  zuciya, domin kuwa babu wanda bai san  Sa'idu mai shayi k'asungumin babban munafuki ba ne, wanda yariga da ya shahara wajen haddasa fitina, sannan  Ya dawo yin tunanin yanzu kuma wanne irin shairi ne Sa'idu yake son kullawa tunda yanzu  har ya gane zuwa wajen Uncle Mustapha da wannan zancen k'aryar ta shi marar Yaji, cikin zuciyar shi ya k'ara cewa "hmm Allah dai ya yi muna maganin wannan abin,"

Jin wajen ya yi shiru ya saka Uncle Mustapha cewa "Ai nariga da na saka shi aiki akan ya saka man ido sosai akan ta dan dik na gano gaskiyar wannan al-amarin wallahi har koto sai mun shiga Ni da Alhaji Muttak'a wallahi dan ba zan taba yarda su bata tarbiyar nasu ba muma su bata mana namu.!  Ka dai ji abin da ya kawo ni, ni zan koma office na barka lafiya."
            Bai ma tsaya jin abin da Uncle Muhammad zai ce mashi ba ya fice fiwww abin shi.

*******

A bangaren Hajiya Kaka kuwa,

Aunty Zahra'u har ta so itama ta kama jidalin domin ayi ta ta k'are ita da Hajiya Kaka yau dan ta gaji da wad'annan bak'ak'en maganganun domin ita yanzu ashirye take da ko gidan ya kama tabar shi tana iya barin shi dan ba dole ne zaman shi gare ta ba, har takai ga tunanin cewa, da wannan cin mutuncin ai gara komai wuyar zaman gidan ku kadaure da shi hakanan,    Tana cikin yin wannan tunanin sai wata zuciyar ta ce mata ai gara tayi hakuri tarik'e uban diyanta idan da sabo ai ta saba da irin wannan, yanzu me yayi saura......

Cikin bacinrai ta dauko kulolin gabadai ta juye mata kifin gami da na Uncle Uzaifa.

Hajiya Kaka ta ce,  "wallahi ni  ko a jiki na dan dai Ni nafi k'arfin bugu ga kowacce 'yar'iska."
       Aunty Zahra'u dai bata ce da ita komai ba domin ta san dik maganar da ta fito mata a baki zata iya furta mata ita komai munin ta.

Hajiya Kaka kam ta saita hanyar ta ta fice daganan zuk'ai-zuk'ai  ta fita daga cikin gidan ko kunya babu ta nufi bangaren ta amma da mamakin ta  sai jin sautin kukan Aunty Rukayya tayi cikin daga murya take fad'in "wallahi ni kuma ko zaka kashe ni sai naci ubanta."
  Sautin  da take ta jiyowa kenan a bakin Aunty Rukayya cikin murya ta  mai cike da matsanancin kuka, dan hayaniyar mutanen gidan ta cika ko ina "da dikkan alamu fad'a ne ake yi." A cewar Hajiya Kaka, Ai ko cikin tsananin bala'i ta nufi hanyar shiga cikin gidan,
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere

WAHALA DA GATA season1Where stories live. Discover now