029

116 11 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ>>>29

_ᏴᎪᏞKᏆᏚᏌ d'iya ce ga wani babban Attajirin mai kudi wato ALHAJI USMAN.
Ya kasance shahartaccen dan kasuwar ne wanda ko wanne dan kasuwa ke burim zama irin shi.
Tun yana k'aramin Yaro ya rasa iyayen shi, wanda hakan yasa ya taso cikin WAHALA inda ba mai taimakon shi sai Allah.
A haka a haka dai har ya girma ya yi karatun shi gwargwadon iko rashin kid'in makaranta ya hana mashi ci gaba da karatu, Inda ba irin kasuwancin da baya yi na WAHALA ne ko na DAƊI ko wanne Ya samu baya rainawa, har Allah ya hada shi da wani Alhaji MU'AZU tun daga nan ne ya fara koya mai sana'ar da yake yi, yana ba shi danyar Zinare akan sari yana saidawa ,,har Allah ya azurta shi da samun na kanshi ,,,,har yakai ga buda nashi company's wajen guda hudu biyu a cikin garin Abuja biyu kuma a cikin garin Sokoto sannan kuma yana da yara samada 100peolpe's wad'anda ke cin abinci a k'ark'ashin shi.

_Alhaji Usman ya nada mata kusan guda hudu, ZAINAB Ita ce babba a cikin suna kiran ta da AMMIE sannan SADIYA wadda Ita ce ta biyu sannan KARIMA Ita ce ta ukku sannan UMMUSSALMA itace ta hudu_

Hajiya Zainab ta kasance makirar macce marar imani marar tausayi sannan kuma miskilar macece 'yar'bala'i amma akwai sai shegen tsoron tsiya, ta nada yara guda ukku wad'anda ku san dik rabin halayyarta ba wanda suka baro sabida sunyo gadon wasu daga cikin munanen halayyanta, rashin mutumci da rashin kunya wannan kan wajen su ya yanke sak'a.

_BALKISU itace ta farko a wajenta sannan NADIYA da ZUHRIYYA.

—«•»—

_Balkisu yarinya ce yar kimanin shekara ashirin, sai dai wulak'antattar yarinya ce bata kallon kowa da daraja ga shegen girman kan tsiya sannan gata da yawan alfaharii da son abin duniya, kusan dik Shekara bibbiyu ne a tsakanin su, tun suna 'yan k'ananun su basa ganin kowa da daraja musamman tsohon mutum da kuma talaka.









_Mahaifiyar su ta kasance mace ce mai tsananin kishin tsiya wanda hakan ne yasa dik matar da Alhaji Usman ya aura basu wani jimawa tare sun'rabu walau mutuwa walau ciyon hauka wanda ba aikin kowa ba ne illa aikin Ammie, tun daga kan Hajiya Sadiya har izuwa sauran hakan ne yake kefaruwa da su.

Wanda ita ce sanadiyyar haukwacewar Hajiya Sadiya sannan ta zuba ma Hajiya Karima da Hajiya Salma magani a cikin abinci sukaci suka mutu, domin tayi alwashin ko zata rasa rayuwarta sai ta hallaka dik wata maccen da taga tana son shiga tsakaninta da uban 'Ya'yan ta,,wanda hakan ba komai ba ne Sai dan dukiyar da taga ya tara wadda take burin ganin ta mallake.
Wanda hakan ya yi sanadiyyar raba tsakanin su da tayi k'ok'arin yi shi da 'yan'uwanshi, Inda taje wajen d'ai daga cikin bokayan ta mai suna FINTINKAU ya asirce mata su suka kasance masu kyamatar junan su ya kasance ko kadan basa shan inuwa waje guda, dik da mutane da dama suna zargin wanna abin ba komai ba ne illa shairin assiri wanda ba kowa ba ne ke da alhakin yin hakan ba sai ita, sai dai koda hakan bamai iya tunkarar wani ya gaya mashi domin a tashi tsaye da rok'on Allah,,sabida dik lokacin da suka furta wannan zancen to babu su babu sake kwana a cikin duniya domin koga k'aramin yaro ne wanda bai ida mallakar halkalin kanshi ba ta samu wannan labarin to zata he ne wajen bokan ta Fintinkau domin ayi mashi Ije wanda zai zamo sanadiyyar rasa Rayuwar shi.

_Haka dai rayuwa taci gaba da gudana a gidan Alhaji Usman cikin zamba cikin aminci da kuma cin amana,
Kwatsam labarin ya same ta akan aljannai sun yi gaba da Bokan ta, sunyi wani wajen da shi, wasu suce ya mutu wasu kuma suce yana raye, haka dai Ammie tayi zaune-zaune kamar wata k'aramar yarinya ta dank'are dan-neman kukan ta son ran ta. domin a cewarta tayi babban rashin shahartaccen kafurin bokan ta marar imani, k'ari da k'arau tashin hankalin ta guda kar assirin da tayi ya karye.

Bayan wasu lokutta masu tsawo ta samu labarin wani shahartaccen Boka wanda ya shahara wajen iya sihiri sannan kuma ko kadan baya wasa da aikin shi, a wajen wata k'awar ta LUBANCY sabida Ita ma dik rayuwar su guda ta wajen biye-biyen Bokaye, wanda wannan Bokan kuma ba kowa ba ne illa BOka MINSINKYU.

'''''''''''''

Ta b'angaren Fatima kuwa tana mai da dubanta ga wanda yarik'e mata hannu sai dai ga mamakin ta wa zata gani?.
Uncle Mukhtar ne wanda shigowar shi kenan ya hango abin da ke faruwa, kai tsaya ya shiga tambayar ta abin da ke faruwa, cikin rawar murya mai cike da wani matsanancin kuka ta ce

"Uncle babu komai Kaina ne ke man ciwo"
Sosai Ya san ta b'oye mashi gaskiyar ne domin tana tsoron kar Hajiya Kaka ta mata d'an banzan duka.

Kai tsaye ya maida duban shi ga su Hajiya Kaka da tin dazu hakince take a saman doguwa kujera ta'aza k'afa d'aya saman d'aya tana karkad'awa cikin isa da tak'ama kamar wata tsohuwar Karuwa,
Ita kuma Aunty Rukayya ta wani tamke fuskarnan ba yabo ba fallasa wanda ita ma bata san tayi ba.
Sai da Uncle Mukhtar Ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya domin yasan tunda yaga Jakar Fatima yashe ak'asa a wulak'ance sannan ga kayanta dik a wawwatse ya san dik yanda aka yi amshe kayan ne su kayi, Sai dai bai tsaya naci wajen tambayar abin da ke faruwa ba Ya ce,
"Teema kin shigo kuwa da ledar kayan da Mummy'nki ta bada abawa Hajiya?."

Ai ko Hajiya Kaka najin anyi maganar Ledar kaya ta sake Ran ta tare da bada aron kunnayen ta a wajen su kamar ba ita ba.
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Donde viven las historias. Descúbrelo ahora