010

200 15 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             _{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

*➡️010*

"Sabida billahillazi da naci maki wannan abincin gwanda na mutu da yunwa, kinga da sai ki zuba ruwa a k'asa ki sha mak'iyiyar ki tabar duniya tunda dama hakan ne burin ki."

Aunty Zahra'u  dai aikin ta kawai saurare  bata ce da ita ko uffan ba illa dai kawai tana tsaya tana sauraren ikon Allah 

Ita kuma Hajiya Kaka kamar wadda ake saka ma man fetur  haka take ta satato maganganu babu K'ak'k'autawa kuma ko alumun gajiya babu a tattare da ita balantana a samu damar futawa hakanan,

"Ai dole ki kama baki kiyi  shiru sabida kinga yanzu Allah ya ida tona kingin assirinki, sai kuma gashi  abin da kika so Allah bai nufa ba, dan haka sai a sake wani sabon salon dan dai wannan kinga tun ba aje ko ina ba kinga ishara dan yanzu gashi asiri ya tonu b'uru-b'uru babu wajen togewa ace bada gangan ba ne, Wai dan ma  tsabar rashin mutumci kifi kwaya d'aya! kwaya d'aya fa dan kin maida ni mage wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan  gidannan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar makirar banza, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi  jikin ki, haka kika zo daga gidan ubanki?, shin ko kin manta ne in tuna maki yanda kika zo kamar wadda ta kwana dubu bata saka Lomar Tuwo a bakin ta ba,  Wuya kamar Marik'ar Lema gabadai ilahirin jinkin ki haka ya ke kamar na wata Tambad'ad'd'iyar Akuya, shin wai Zahra'u ko kin manta ne?. Ina jiran amsar tambaya ta.!"

Banda sharb'ar kuka babu abin da Aunty Zahra'u keyi, domin baqin cikin da Hajiya Kaka ke kunsa mata ya yi yawa,

Ita kam Oga bala'i  ko a jikin ta,  yanzu ma aka bud'a wani sabon shafin,

Ta kara da cewa.....

"Dubi yanzu sai cika kike kina batsewa,  kina yanda ki kaga dama ki taka wanda kike so ki wuce hankalin ki kwance dan kinga ba'a ce maki ko k'ala, ke a  tunanin ki tsoron ki ake yi ko?  shiyasa  kike yanda ran ki yake so, to ba wanda kejin tsoron ki dan ba wanda kika fi wallahi,   dand'e wulak'ancin banza, yamzu duba ki gani dik bayan Sati d'aya sai an jibge maki wani sabon Buhun Shimkafa, ajima ajima an kwashe Masai Ke wai ko gajiya bakya yi da hawan Masai'n, dik  kinfi kowa hawan masai ko dik a tunanin ki ba wanda bai sani ba, ke in banda imani ma da yazzamana  ni ina da shi da kina ganin dik wannan abin da kike yi da tuni ban saka anyi waje dake ba, to ki kiyaye ni wlhy, kuma wallahi kin dai ji rantsuwar cikakken musulmi ko dik ba'a k'araman wannan kaifin ba narantse da Allah bazan raba ki dashi ba mayya kawai."

A sannan Aunty Zahra'u ta samu damar yin magana ta ce, "wallahi Hajiya Kifin dika dika Ganwo ukku ne aka kawo,  sabida ko da aka je sayen Kifin ya k'are shi ya sa na saka maki guda d'aya sannan na sakawa Daddyn Abdullah d'aya,(Uzaifa) sannan na sakawa yarannan wallahi Hajiya nima yanzu haka koga baki na ban saka shi ba wallahi."
 
         "Wai Iskancin banza,  wallahi ko limamen gidan ku  zaki had'iye man ba zan taba yarda  dake ba, cikin halayen ki wanne iri ne bansani ba algumguma muje kitchen dik wani abu da kika san kin dafa abincin da shi da kuma abin da kika zuba abincin muje ki dauko man na gani tsohuwar munafuka, ai ni wallahi ko Qur'ani zaki shekara kina  rantse man dashi hmm,

Aunty Zahra'u dai ta ce "To  Allah Ya baki hakuri,  muje kitchen d'in ki duba."
 
        Suna shiga cikin kitchen d'in, ta shiga bude mata ko wacce tukunyar da tayi anfani dai ta domin ta gani da idonta kamar yanda ta buk'ata  dan ta sheda ta gani da idon ta, sai dai ko da hakanan bata tsira ba.

Daga Hajiya Kaka  me ta ce,  "Hmm wai dan tsabar rashin mutumci cikin wadannan  tukanen Yau aka dafa abinci  dand'e ana sane da dole ne Yau sai an ganni  sabida dama haka ake so shi ya sa aka dafa Shimkafar a cikin tukunyar da bata wuce  lamba 5 ba ga kuma ta Miya wadda ita ma bata wucee lamba biyu ba, Ke da dori ma lamba ashirin ma kina iya cika ta da abinci kuma ko kwana baya yi balantana a samu nayin d'imame gabadai kin cinye, Yau kuma dan munafurci da wad'annan aka yi?, munafuka muje ki dauko man kulolinku na abinci na gani."

Bayan ta dauko mata, har ta fara bud'e mata ko wacce kula tana ganin abin da ke cikin ta sannan bud'e mata kulolin yaran, nan fa Hajiya Kaka ta hango wata 'yar  guntuwar tsoka wadda ko rabin girman kan kifin bata kai ba, 
         ta ce "Dama  na sani shiyasa Rukayya ta ce inzo da kai na in duba dan ta san halinki  tsaf zaki iya rantsuwa ki ce shikenan ne dan baki san muhimmancinta ba ko?, to yanzu miye wannan? kika ce ganwo ukku ne ko? to wannan fa da ya yi kusan  rabin kan Marak'i fa, shin ko daga sama ne ya fad'o banda labari?   Ko kuma haka kawai ya shigo cikin dan yaji ana maganar shi?."

Ni kuma Hajiya sai naga kamar ba wani babba ba ne wanda zaisa har a damu a kan shi,  kuma ban zata abin zai bata maki rai haka ba  da na game maki da shi ai."

       "Kazat-ubaaaaa, akan wannan bak'in kifin har zai sa Rai na Ya b'ace,  Allah ya kiyaye ni wallahi, ai ni ba irin ki ba ce,  dan haka yanada kyau ki sake tunani bak'ar munafuka."

"Ni ba haka nake nufi ba Hajiya Allah ya baki hakuri, kawo kular sai in zube maki kifin,"

         "Awww yanzu dan kin raina ni  har sai na mik'o maki kullar zaki zube man kifin? lalle Zahra'u wuyanki Ya yi kauri,  to bari kiji in gaya maki wallahi wannan jikin naki ba zai tab'a bani tsoro ba yanzunnan wallahi sai in ciraki sama-sama in buga ga k'asa, idan kuma kina tantama sai yanzu akafta ki gani."

  Hak'urin Aunty Zahra'u kam tuni ya gama k'arewa kai tsaye ta ce.........
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere

WAHALA DA GATA season1Donde viven las historias. Descúbrelo ahora