036

113 9 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

EPISODE>>>36

_Cikin wani matsanancin tashin hankali ko wannen su ya dubi wani Suna mai nadamar biyewa son zuciya irin ta su, cikin rawar murya Ammie ta soma magana ta ce
"Ya kai shahartaccen Aljanin Boka muna mai neman afuwarka tare da neman mafita a cikin wannan al'amarin, munyi alk'awarin yi maka ko wanne iri abu da kake k'ok'arin gindaya mu akai! Sannan kuma Ya kai boka kayi mana rai a cikin tafarfakin ka, ka biya muna buk'atar mu cikin ruwan sanyi ba sai ka cutar damu ba wallahi munyi alk'awarin ba zamu tab'a Sab'a maka alk'awarin ka ba zamu zamo masu cikawa ako wanne irin hali na rayuwar yau da kullum.!"
nan da nan kukan WAHALA ya yi gaggawar sub'ce mata, a cikin kukan ne ta sake cewa, "Wlhy mu ko a hakan ka barmu mungode dan dai kan mun likkid'u tuburan.!"

_Cikin wata irin arniyar dariya mai cike da ban tsoro su kaji boka Mintsinkyu ya bisu da ita, Sannan daga bisani sai ya k'ara turmuk'e fuskarnan mai kama da kashin Shanu sannan ya ce "Lokacin da kuka fara zuwa nan na fada maku cewa zaku biya! ME KUKA CE?.!"
cikin wata Irin razananniyar murya mai cike da ban firgici ya yi masu wannan Mahaukaciyar tambaya.

Cike da wani irin Matsanancin firgici Ammie ta ce "EH......EH!"

Nan take ya sake Maimaita masu tambayar da ya yi masu cikin tsawa kamar ta d'azun,
Ammie ta ce, "CEWA NAYI A SHIRYE MUKE MU BIYA KO NAWA'NE, amma yauzu idan da son samu ne ayi hakuri abar wannan aikin wlhy mun hak'ura da shi gabadai kuma daga yau wlhy mun daina biyar ko wanne irin Boka dake cikin fad'in duniyar nan, wlhy mu tuba ba zamu sake ba dan Allah ka barmu da rayuwar mu karka Illatar damu.!"

Dik a gigice Ammie keta satato wad'annan kalaman nata wad'anda ba zasu amfane su da komai ba Illa k'arin wahalar da suke ta famar fuskanta,
Ita dai Balkisu ta riga da ta sadak'at da rayuwar ta domin har ta aminta da ba zasu taba fita a cikin wannan tarkon da suka jefa kan su tsunbulbul a cikin sa ba.

*Boka ya sake maimata masu da wata irin tantiriyar dariya wadda tak'ara jefa su cikin wani Matsanin hali da fargabar abin da zai sake fitowa daga cikin bakin sa domin sun san ba maganar alkhairi bace zaiyi masu ba.

_Sannan ya ce "Hakan ma Shawara ce Amma da Sharad'i.!"

Da rawar murya tare da saurin sharb'e zancen Ammie ta ce, "Menene sharadin ya kai fitaccen Aljanin Boka.!"

Ya ce "Zaki sadaukar?."

Ammie kam tun kafin taji abin da zasu sadaukar d'in, ta tsinci kanta cikin wani matsanancin farin ciki harda su hamdala a cikin zuciyar ta ba tare da b'ata lokaci ba ta ce

"Ko ma menene mun amince mun baka wuk'a da Nama.!"

Ya ce "To! Yanzu za'a shanye jinin d'aya daga cikin ku sannan za'a bar d'ayar da rayuwar ta amma sai ankwakwale mata Idanuwa domin dik wanda ya yi kuskuren sakayo kanshi gareni domin biyan wata Buk'ata tashi daga baya kuma ya canza ra'ayi to tukwicin da yake samu a wajen mu kenan Idan kun amince yanzunnan sai a fara aikin.!"

Nan take Ammie ta dubi Balkisu suka had'a ido cikin wata matsananciyar damuwa had'i da nadamar abin da suka aikata ya fito k'arara a fuskokin su,
Sosai Balkisu tayi tir da Allah waddan wannan halin da mahaifiyar ta ta jefa su domin ita ce sillar komai da yake faruwa da su a halin yanzu.

Cikin sauri tare da had'a zantukan su waje guda su kace " Mun aminta aci gaba da yin aikin, sun yi alk'awarin zasu bi dik wasu dokokin shi, annan zasu zamo masu biyayya a gare shi.!"

Suna ida satato maganar cikin mamaki ko waccen su ta kalli d'ayar da mamakin yanda aka yi maganar su tazo iri daya.

A dai dai nan kuma Boka Mintsinkyu ya katse su da cewa "ZAN BAKU SHARUDDA GUDA BIYU 'IDAN KUN TSALLAKE TO KUNTSIRA DA RAYUWAR KU.! IDAN KUMA KUKA KUSKURE DIK ABIN DA YA BIYO BAYA KU KUKA JAMA KAN KU BA NI BA.!"

Gabadayan su suka amsa da "sun aminta da ko wad'anne irin sharud'd'an ne.!
Sun bada amsar ne ba tare da sun tsaya yin tunanin komai ba...
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang