*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
_{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*➡️014
kafin ta'ida waiwayowa bayan ta har ta yanke hukuncin cewa koma wanene tana juyowa zata zube k'asa ta gaida shi sannan dik abin da ya saka ta zata yi k'ok'arin ganin ta aiwatar, dik da da kashi🙊 ya yi ya ce ta wanke mai a shirye take,
Tana ida juyowa cikin hanzari ta tashi duk'awa k'asa domin aiwatar da abin da take da niyya kamar ance mata Ke dan ubanki dago kanki ki kalle ni, cikin hanzari ta daga kanta sama domin duban ko wanene, kafin ta kai ga aiwatar da k'udurin ta tana kallon fuskar shi
Sai dai da mamakin ta wa zata gani?.
Uncle Mukhtar ne wanda shigowar shi kenan a gidan ya tsinkanyo abin da Mahaifiyar shi ke shirin aiwatarwa wanda bai ma san lokacin da ya dank'e mata hannu ba domin ganin ya hana ta aiwatar da abin,
Tin yanda ta lura da ko wanene sai taji kamar an dibi ruwa masu sanyin tsiya an wankada mata a saman kirjinta da tun dazu suraci yake fiddawa aka tsoro, bata san lokacin da ta ambace Alhmdu lillahi ba, amma a cikin zuciyar ta
A fili kuwa sake murtuk'e fuskarta ta k'ara yi takin-takin kamar wadda bata tab'a yin dariya ba a dik tsawon shekarrun ta ba,
Cike da bak'in bala'i tare da d'aga murya ta ce "saunonin banza idan har ba zaku iya ramawa kanwar ku cin amanar da aka yi mata ba, ni ku barni in rama mata d'in matsoratan banza maras kishin junan su 'yan-iskan banza ga ku nan sai famar d'ad'd'ahe masu kuke yi kamar cingan kuna nuna masu so da k'auna amma su ko kadan wallahi basa kaunar ku a cikin rayuwar su Allah dai yawadaran wannan bakar zuciyar taku wallahi, ni wlhy ban san inda ku kayi gadon wannan bakar rayuwar ba."
Ba dai wanda Ya ce da ita ko uffan a cikin su domin mamaki da tsoron Allah dik ya cika zuciyoyin su ganin bata ma tsaya sauraren inda kanun labaran suka nufa ba amma har ta yanke danyen hukunci da kanta
Aunty Rukayya ce tayi qarfin halin gaya
mata abin da ke faruwamagana take tana Shashshekar kuka akan wahala, ta ce "Wallahi Hajiya Yaya Aminu ne dik Ya yi man wannan mugun dukan sai da su Ya Mu'azzam suka anshe ni a hannun shi kamar ya kashe ni wallahi Hajiya." Nan take ta k'ara bazgewa da wani mahaukacin kuka wanda Ya yi bala'in shiga Ran Hajiya Kaka,
Nan take Hajiya Kaka ta maida duban ta ga Uncle Aminu ta ce " kai dan kana bakin mahaukaci sauna wawa har yanzu an kai wannan munzilin da za'a hadaka fada da 'Yar uwarka kuma kanwarka t Jini ciki daya? Ciki d'aya fa ba wasa ba! har zaka i'ya biyewa munafukai irin wad'annan." Ta nuna su Uncle Mu'azzam...ta ce " wad'anda basa son ganin cigaban ku wad'anda yanzu basu da wasu makiya sama da ku, to wallahi ko har abada ba zaku iya
raba anta da Jini ba, wallahi kuma baku isa ba wallahi dan sai na kai kara kotu domin a fidda mana hakkin mu akan ku miyagun banza kawai."A sannan Uncle Aminu ya bude bakin shi ya fara zayyana mata dik abin da ya faru da kuma abin da ya gani da idon shi, har Aunty Rukayya ta bud'e bakin ta da niyar karyata zancen,
Cikin mugun bacin rai Uncle Mukhtar ya dakatar da ita da wata mahaukacciyar tsawa ya ce"Ke yanzu har kinyi wannan matsayin da zaki bud'e bakin ki ki karyata zance dan baki da tarbiya ma manya na magana kina saka baki?, wallahi dik na k'ara Jin kin kara cewa ko uffan wallahi sai jikinki ya gaya maki.!"
Cikin mugun Jin tsoro Aunty Rukayya ta kame bakin ta domin tafi kowa sanin halin Yayan ta sarai shi ma zai iya kara mata wani dukan ga yanda zuciyar shi ta taso sama can kololuwa.
Hajiya Saudat ba ta ce dasu komai ba taja yaran ta suka koma bangaren su.
Cike da mugun Jin haushin abin Hajiya Kaka cikin d'aga murya ta bud'e baki ta ce
"Ai dole a koma daki tunda dama abin da ake son gani an gani." Ta ja tsaki mtsww tare da cewa "munafukai banza kawai".Uncle Mukhtar ya ce
"Dan Allah Hajiya ki daina yin irin wannan abin wallahi wannan bai dace ba ko kad'an, haba Hajiya dan Allah ki daina yin........"
Bai kai ga ida zancen ba ta katse shi ta hanyar cewa
"Awwooo ai dole ka ce haka tunda an tabo k'annen ubanka Mtsww"Shi kam Uncle Aminu tun lokacin da ya gama gaya mata abin da ya haddasa yin dukan da ya yiwa Aunty Rukayya yaga alamun tafi ganin laifin shi afusace ya bar gidan gabaki daya dan kar ran shi ya sake b'aci.
.....
Bayan Uncle Mukhtar ya lallab'ata sun koma daki ya ce dama Fatima ce yazo dauka domin yakai ta gida tunda anyi masu hutu a skull ta yi koda sati biyu ne sannan yaje ya dauko ta.
Hajiya kaka ta ce "gaka gata dama ni ta ishe ni wallahi".
Ya k'ara da cewa ya ce "Dama kuma maganar da nake son yi maki ita ce, Gobe Insha Allah Balkisu zata zo ku gaisa".
( cewa da matar da zai aura)"To Allah ya kawo ta lafiya" haka kad'ai ta iya furta ma shi.
Sannan ya tashi ya kira Fatima ya gaya mata ta shirya yanzu zai kaita gida.
wa"iyazu billah murna awajen Fatima kam ba'a cewa komai sabida dama tana son tafiya gida sai dai tana gudun duka agurin Hajiya Kaka domin zata ma iya cewa ba zata je din ba.***************
Bangaren Uncle Muhammad kuwa tun lokacin da Uncle Almustapha ya fita, ya dinga tunanin yanda al'amarin zaya kasance ma shi idan yace ma Hajiya Kaka zai dauki diya tai sabida shi dama Ya gaji da ganin ta cikin wannan bak'ar wahalar kuma sannan ga bakin labarin da Uncle Almustapha ya zo mashi da shi dangane da diyan Alhaji Muttak'a dan ya san wad'annan Yaran ko kadan basu da kamun-kai ga rashin mutumci sannan ba wanda bai san su ba wajen rashin tarbiya da kuma bad'ala da mazan banza.
Sai dai kuma bai san yanda zaya bullowa wannan al'amarin ba tsakanin shi da Hajiya Kaka ba, dan ya san wannan abin ma ba mai yuwa ba ne agare ta ba.
Haka dai ya dinga tayin tunane-tunane shi har yaji zaman office din ya gagare shi, ya dauke dik wani abin da yake da bukatar tafiya da shi gida ya kulle office din shi yafita, bayan Ya yi reporting akan baya jin dadin jikin shi zaije gida yadan futa dik wanda ya zo neman shi ace bayanan.
Sosai dik wani ma'aikaci dake wajen Ya yi matuk'ar mamakin tashin shi da wuri haka misalin 2pm sai dai ba wanda ya isa ya dakatar da shi a cikin su,
Daganan ya ziyarce Wajen da ya yi parking d'in motar shi ya yi gaba.--------------
Bangaren Aunty Zahra'u
Hajiya kaka na fita daga gidan ta shiga daki bata san lokacin da wani azababben kukan ya kub'ce mata ba domin irin zagin da Hajiya Kaka ke mata ba karamin mugun bakanta mata rai yake ba, daganan kuma bata san lokacin da wani nannauyan bacci yazo Ya yi awon gaba da ita ba,
Ba ta tashi ba sai da aka kira sallar Azzahar a sannan ta falka ko da ta falka yara har sun dawo daga makarantar Boko suna shirin tafiya islamiyya.*****************
Hajiya Kaka sam jidali ya mantar da ita abin da take rik'e da shi kafin ta samu wannan mummunar faduwar, aiko tana tunowa cikin hanzari ta mik'e tsaye ta fita waje domin dauko abin da ta zo da shi dan bata ma san yanda ya Isala ba, sai dai da mamakinta ko da ta fito waje kulolin gabadai a wawware ta gansu dasu da abinda ke cikin su, anan da take tsaye ta hango Maguna (cat's) dik sun gewaye kifafen sai ci kawai suke yi cikin kwanciyar hankali da walwala,
Nan da nan ran ta ya yi mummunan baci har bata san lokacin da ta hira Sama tayo cikin wad'annan Magunan ba sai da......
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere
ESTÁS LEYENDO
WAHALA DA GATA season1
FantasíaSeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...