*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ 20
Matar da Uncle Mukhtar zai aura ce wato Balkisu, tana kawowa daf da kofar shiga Parlour suka tashi yin kabra ita da Hajiya Kaka wanda Ita Oga Hajiya har ta manta da ya gaya mata zai kawo mata ita yau su gaisa, sai gashi wajen gudanar da bak'in jidalin ta ita da gudan jininta Aunty Rukayya dik ya dauke mata hankali,
_Bangaren Balkisu kuwa cikin ranta take ta ayyanawa akan ita ce zata gyara ma Hajiya Kaka da Aunty Rukayya zama muddin ta shigo gidan domin da shirinta zata zo dan dik wani bakin hali na Hajiya Kaka ba wanda shanun talla basu sanar da ita shi ba akan ta fasa auren Uncle Mukhtar, taja wani dan guntun murmushi can cikin k'asan maqogoron ta sannan ta ce "Ni ce zan zamar maki tamkar k'aya a bakin kofa domin da shiri na zan tunkare ki matsiyaciyar tsohuwa kawai ballagaza."
Sai dai a fili sai ta nuna damuwar ta matuka a gare ta tare da cewa "Subhanallahi Hajiya lafiya! me yasame ki ne?.
Bata jira amsar da zata bata ba ta ce ma Uncle Mukhtar "dan Allah mu kaita asibiti dibi jini'fa sai zu ba yake mata". Ta k'arkare maganar ne kamar ta yi kuka daganan saiga wani munafukin guntun kwalla ya fado mata a saman kunce, ita ala dole tausayin ta takeHajiya Kaka ita kuma da tin dazu kame
-kamen kunya take dan bata so Balkisu ta zo ta same ta haka ba amma zancen da taji Balkisu tayi na nuna kulawa a gareta bakara min dadi taji ba a fili, amma a cikin zuciyar ta ta ce "hmm baki san dawa kike zance ba ja'ira."
sai ta danyi murmushi ta dubi Balkisu cikin tsantsar farin ciki da kula ta ce " kar kiji komai wlhy diyarnan dama aljannun Rukayya ne suka tashi kuma dik lokacin da suka ta shi hakanan su keyi tun dazu nake ta fama daga sun kwanta sai kuma su sake ta shi abin dai sai hamdala."
A sannan Balkisu ta ce "Ayyyaa Allah sarki Allah ya bata lafiya."Gajiya Kaka ta ce "Ameen"
Uncle Mukhtar da tun dazu haushi Ya riga da ya gama turmek'e shi domin ya san ba wasu aljanne da ke da Aunty Rukayya dan bai tab'a ganin sun tashi ba, ga kuma yanda suka zo suka sameta kaca-kaca kamar wata mahaukacciya ga kuma Aunty Rukayya da suka hadu da ita aguje kamar ta bangaje su ta fada cikin gidan Uncle Uzaifa ya san dik yanda aka yi fada ne suke yi sannan cikin zuciyar shi ya ce "kaiiii wannan wacce irin rayuwa ce haka"
Sannan ya ce "Ayyaa kenan su ne suka rashi yau ko?."
cikin sosa k'eyar kai Hajiya ta ce "Eh.... eh"
sannan ya ce to bara mu shiga ciki sai na gyara maki goshin dan kamar ya fashe".
a sannan Hajiya Kaka ta ankaro da zafin da take ji tun dazu a goshin cikin tsananin jin kunya ta ce " ayyaa ai dazu ne da ina kakkance-kakkancen gida na buga kaina a saman bango ban san ma ya fashe ba, kasan Fatima batana!"sannan ya ce "eh kuwa Hajiya hakane."
_Sannan tace ku shigo cikin dak'i mana kunyi tsaye kamar baki ta danyi murmushi dan bata son ta fara sai da halin na ta a gaban Balkisu tun yanzu.
Haka dai Balkisu tayita sauraren ikon Allah har aka gyara wajen da ya fashe din, sannan Hajiya Kaka ta ce ma shi "ka shiga d'akin Hajiya Saudat da ita kuwa?."
ya ce " a'a sabida d'azu Uncle Mu'azzan ya kira shi akan zasu je wajen ziyara gidan kakannin su tare da HajiyaSai da Hajiya Kaka ta turmuk'e fuska da jin wadannan kalaman dik da bata so nuna bakin halin nata ba a gaban Balkisu hakan yasa ta sake ran ta kamar ba ita ba sannan ta ce kun shiga d'akin Alhaji kuwa dan yananan."
sai ya ce "A'a"
Daganan taji wani irin mugun farin cikin ya lullub'e ta kamar wadda aka yi ma bushara da gidan aljanna domin dama tana bidar mararraba ne da su, acewar ta domin ta samu ta kimtsa jikin ta.........
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere
