028

114 10 0
                                        

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ>>>28

Can sai taji ta fad'a wata uwa duniyar ta daban, duniyar wani zazzafan mafalki mai cike da ban tsoro da ban firgici wanda gabadai ilahirin ruhimta ya tare a can,
Wani mahaukacin Jeji ne ta tsinci kanta a ciki,, mai cike da abubuwan bantsoro tare da wani mahaukacin duhun da ko tafin hannun ka baka isa ka ganshi ba sannan ba abin da ke cikin wannan Jejin sai mugayen naman Daji,
Ga kuma kukan Kura dana Jakkai dake tashi a wajen wanda ko za'a kashe ka ba zaka ce ga inda suke ba.

Sai famar gudu take babu k'akkautawa wanda har yanzu ta kasa cimma hanyar da zata fidda ta daga cikin wannan Jejin, sai tayi gaba ta dawo kuma baya, ta kauri wannan Iccen ta buge wancen Dutsen ta fad'i ta tashi haka take ta gudanar da gudunta babu ƙaƙƙautawa a cikin wannan bak'in Jejin.
Nan dai ta hango wani k'atoton kogo wanda ke cike da wani mugun haske kamar na wutar murhu, nan take ta k'arama k'afafuwan ta Fetur, nan take ta ce k'afa me naci ban baki ba a gurguje ta saita hanyar ta cikin wani matsiyacin gudun da bata taba tunanin tana dashi ba, sai gata tsan galgal acikin kogon.
Wani abin mamaki kuma tana shiga cikin kogon taga gabadai duwatsuna sun fado daga sama sun rufe hanyar data fito sannan kuma wannan hasken iya kacin shi a waje ne, domin a cikin kogon dulun-dulun yake kamar k'abari ga wanda baiyi aikin alkhairi ba, hankalin ta idan ya yi dubu sai da ya tashi, Sai can ta hango wata hanya wadda da alama Ita kadai ce hanyar fita daga cikin wanna bak'in kogon domin tana d'an tsinkan yo alamun Hasken rana a can ya gauraye ko ina daga wajen.

Nan dai taci gaba da gudun da take babu k'ak'k'autawa, sai dai kuma a yanda take gani sai tayi kusan cimma hanyar sai kuma taga hanyar tak'ara nisa a gare ta,
Daga nan dai ta samu nasarar kawowa daf da wannan hanyar sai dai kai tsaye taga wannan hanyar kamar an saka marfi Galan an kulle ta, nan take wani d'ankaren duhu ya dinga fitowa daga cikin hanyar yana nufato wajen da take, daganan ta fara harmar komawa baya cikin wani matsanancin gudu wanda ya ma fi na d'azun, sa jin tayi ana kwasar wata mahaukacciyar dariya mai cike da ban tsoro wadda gabadaya ilahirin wannan kogon sai da ta gauraye ko ina, sannan kuma daga bisani taji dariyar ta koma mata kamar kukan Jaki, lokaci guda kuma taji komai ya tsaya .wajen ya yi tsit kamar ba abin da ya faru, Daganan taji wata zazzak'ar murya na fad'in "Sannu da gajiyar tsayuwa uwayen gudu.!"
Aiko cikin wani mugun firgici ta juyo ta bayan ta domin ganin wanda ke yi mata maganar domin tana da tabbacin k'ila zai iya taimakon ta....

Sai dai da mamakin ta sai ganin wani ruftumemin maciji tayi bak'ik'irin idanuwan shi Jawur kamar gauta, sannan tsawon shi ma abin tsoro ne ga dik da a nannade yake kamar tayar mota, Cikin karfin hali ta daga fuskarta sama domin tabbatar da macijin ne da gaske ko kuma icce, amma da mamakinta Sai ganin fuskar 👺boka MINSINKYU tayi dahe a jikin macijin kamar photo, ba yabo ba fallasa sannan cikin kwayar idanuwan shi wuta ce jawur ke ci balbalbal a ciki kamar an kunna gas, Nan da nan wani bala'in tsoro ya sake yagauraye afuskar ta, ihu take son ta yi amma ya gagara a gare ta kamar wadda aka ruk'e ma baki.

Sai can taji wata ar'niyar dariya ta bayyana a baya ta sa ta tafi ta dawo, nan take wajen ya gauraye da dariya mai kama da kukan shanu, nan kuma taga bayyanar wasu munanen halittu masu kama da Kunamu wad'anda ke da Ijjiya guda a tsakan kan su ta mik'e tsaye tsangal kamar icce kuma jawur kamar Jini.

_Nan take taga dik suna tunkaro ta, iyakar razana kam tayi ta sannan gashi babu wajen guduwa domin gabadayansu gewaye suke da ita, kuma ga wani kuka da suke yi maicike da ban tsoro da firgici,
Nan take Ta buga wata irin kafurar k'ara wadda sai da ko ina ya amsa tare da bayyanar wani mugun hasken da yake tashi sama kamar walqiya hadari, nan take ta fad'i k'asa kwance sumammiya a wajen.!

Firgigit ta falka tare da wani irin mahaukacin tsoro tafalka, a hanzarce ta mik'a idon ta ga agogon dake make a bangan d'akin taga yanzu misalin 2:30am na dare, nan take cikin zafin nama ta mik'e tsaye tsangalgal a saman gadon ta, nan tayi wani irin kukan kura ta hiranyo a k'asan gadon tuwww sai da ta rashi duraunewa a k'asa.

Aguje tabar dakin ta nufi hanyar da zata sadata da dakin Ammie, tana isa ta banke kofar d'akin da k'arfin Allah kamar ta balle, ta ida k'arasawa ciki da hanzari tare da wani mahaukacin kuka, sai dai da mamakin ta Ko da ta shiga cikin parlour'n bata cimma Ammie anan ba, nan da nan hankalinta yak'ara tashi tsoro ya sake bayyana a fuskarta da k'arfin Allah ta shiga kiran Ammie, sai dai abin da bata sani ba shine Ita ma Ammie irin mafalkin nata ne tayi tun dazu ta tashi ita ma ta kasa komawa bacci, ingizo kofar da taji anyi ne da karfi ya sake tsoratar da ita ta shige cikin Bathroom ta kulle kofar da makulli.

Sai dai tun looacin da taji muryar Balkisu ce ke tashi a cikin dakin ta hankalin ta yadan kwanta cikin wata mugunyar razana ta fito daga cikin bathroom ta nufato wajen da take jin alamun muryar Balkisu ke tashi, amma kuma koda tazo ta cinma Balkisu tsaye sank'are a bango ta lak'e jikin ta sai rawa yake yi, cike da wani irin mugun firgici take fad'in "Ammie kashe mu zayayi wallahi kashe mu zayayi tana mai nuna mata jikin bangon ginar da take saiti da ita, Ammie na ganin abin da ke jikin bangon dakin ta, aiko bata san lokaci da ta zame jiki ta fad'i kwance k'asa sumammiya ba, hankalin Balkisu Ya yi mummunan tashi nan da nan jikinta ya dauki rawa ta dinga kiran Ammie cike da ban tsoro aiko bata san lokacin da Ita ma tabi Ammie ba wajen zame jiki ta fad'i sumammiya a saman jikin Ammie.........,

ᏔᎪᏟᎬᏟᎬ ᏴᎪᏞKᏆᏚᏌ?

Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang