023

124 14 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ >>>23

_Ꮇisalin garfe 5:30pm Hajiya Kaka ta shirya tsafff ta fito palour da niyar ta dan zauna ko Allah zai kawo mata dai daga cikin Su Uncle Mukhtar su kaita Lafai road d'in sabida wayar ta ba caji ballantana ta kira su gashi kuma bata son hawa Machine ko Napep sabida bata son ana gudu da ita sosai.
Tana Ida fitowa a cikin palour sai ta yi kici6us da Aunty Rukayya kwance a saman doguwar gujerar dake cikin dakin tanata jin dadinta sai washe 😆 baki take yi kamar wata tsohuwar mahaukwacciya☹ ta nata kwasar dariyar ta hankalinta kwance.

_Nan da nan taji ran ta ya yi mummunan b'aci dan ta tsane irin wannan banzar dariyar wadda ko cikin bacci taji ana yinta sai taji kamar ta dank'o wuyan mai yin dariyar sannan ta sake Tamke fuskarnan mai kama da kashin Jaki tare da yin bak'ik'irin da rai kamar wani k'atiton bak'in maciji.

Ita kam Aunty Rukayya ko a jikin ta, sabida bata ma san da zuwan ta a wajen ba sabida firar da take yi da k'awayenta a Instagram dik ya dauke mata hankali.

Hajiya Kaka da ta gama cika tamm kamar ta fashe aiko bata san lokacin da taja wani mahaukacin tsaki ba wanda ya yi sanadiyar dawo da hankalin Aunty Rukayya a wajen, sannan ta ce "Rukayya tashi zaune ina son magana dake.!" Aunty Rukayya da hankalin ta dik ya gama tashi domin har a cikin rayuwar ta take jin wannan maganar ta Hajiya kaka sabida tun lokacin da suka huce haushin junan su bakin su bai tab'a haduwa ba waje guda ba kowa kyauce ma wani yake yi.
Aunty Rukayya najin tsoro ita kuma Hajiya najin haushi.

_Ta ce "Kenan ke kinfi son muyita zama a haka ni da ke babu magana ko?. wato ki nuna man cewa lallai ke d'iyar zamani ce ko? ki nuna man idan har bani nayi maki magana ba ke baki isa kiyi man ba, shin ni abin da nake son sani a yanzu shi ne, ni da ke waya haife wani a cikin mu?."

_Sai da Aunty Rukayya ta dan tunzure da bakinnan ya koma tamkar gidan kashin kaza🙊 sannan ta ce "kiyi hak'uri.!"

"A'a ni amsa ta nake nema a wajen ki ba hakurin ki ba."
Ciki-ciki ta ce "ke"
Hajiya Kaka ta ce "Ni waton hmm☹, to me yasa baki dauke ni a wannan matsayin ba da har kike gaba da ni akan banza?."
"Wallahi Hajiya ni ba gaba nake dake ba.!"

"hmm wai iskanci to gaya mini meye sunan abin tunda kin ce ba gaba ba ce?."

Aunty Rukayya ta ce "dan Allah Hajiya kiyi hakuri wallahi shairin shed'an ne."
"shairin shed'an ko kuma dai son zuciya? hmn Allah dai ya shirye ku wlhy diyan zamaninnan, dan mu wallahi ko rabbin abin da kuke mana bamu yi ma iyayen mu ba.!"

Shigowar Uncle Mukhtar ne cikin gidan ya katse mata hanzari, sai dai da mamakin ta ganin kawai tayi ya wuce bangaren Baba ya gaida shi kafin ya shigo bangaren ta. Nan dai ta ce "Alhamdu lillah gama Mukhtar nan Allah ya kawo man sai yakai ni gidan su 'yar iskar can wlhy ayi wadda za'ai."
A sannan Aunty Rukayya ta bud'e baki ta ce " ina zaki yanzu halan Hajiya?."

_Sai da Hajiya Kaka ta danja tsawon wani lokaci kafin ta iya bud'e bakin ta sannan ta ce "wajen' 'yan'iskan can mana yanzu satin ta nawa da tafiya gida har yanzu ba labarin dawowar ta gashi har gobe za'a dauki azumi amma bata dawo gida ba, wallahi nasan ba kicihin kowa ba ne illa na waccan bak'ar munafukar mahaifiyar ta ta"

Aunty Rukayya ta ce "Wallahi kuwa dan ba wanda ke hana ta dawowa gida sai ita dand'e iskanci, Ai barni da 'yar'iska dan na rantse da Allah yau idan naje sai ta gane kuren ta wanda gobe ma ba zata yi marmarin rik'eta ba har ta hana mata dawowa gida.

"Assalamu alaikum."

"wa'alaiku mussalam"

"Hajiya an wuni lafiya?."

"lafiya k'alau! dama kai nake jiran ganin shigowar ka in kai in Aminu domin ku kaini Lafai road wajen 'yan'iskan can na dauko Fatima dakaina domin ina dalili ina mufari tin yaushe taje gidan amma har yanzu babu labarin dawowar ta an kasa maido ta, dan haka wallahi tun wuri tashi muje na dauko ta dakai na na gani idan da akwai wanda ya isa ya hana, wannan ai bak'in iskanci ne ni na raini abu a hanuna Naci kashin ta Naci fitsarin ta amma yanzu dan ta girma bayan na gama shan bak'ar wuya azo a dauke ta daga gare ni, to wallahi karyar su tasha k'arya dan wallahi bazan taba yarda ba.!"

_Dakyar da walahaula, Uncle Mukhtar ya samu ya shawo kanta domin ya san idan har ta tafi da kanta d'in kamar yanda ya san ba za'a sha da kyau ba, sabida shi a salam ya manta da bai dauko Fatima ba sabida yana yin aikin shi dik Ya dauke mashi hankali ya manta da batun Fatima, da hanzari ya mik'e tsaye ya fice da sauri domin ya san halin Hajiya Kaka sarai lokaci guda zata iya canza shawarar ta ta ce sai tabi shi sun je tare.
.....

B'angaren Sa'idu munafuki kuwa, tun lokacin da aka buga mashi wannan gundunbulin k'aton iccen a saman kai, yake kwance rai a hannun Allah, har yanzu da kusan 3hours da yin wannan abin amma bai falka ba, bayan ruwan da aka shatata mashi sunfi k'arfin galon shidda amma ko da hakan motsin kirki ma babu ballantana numfashi wanda hakan yasa kowa a gidan ba wanda bai shiga damuwa ba,
Masu fadan kuwa tuni suka dawo Nadamar da bata da amfani tunda aikin gama ya riga da ya gama.

Koke-koken da suke yi ne su da yaran su babu kakkautawa, Ya yi sanadiyyar janyo hankalin mak'otan su har su kasan abin da ke faruwa a gidan sannan suka yi k'ok'arin kawo masu dauki da taimakon gaggawa, dik wadanda suka zo dubiya sai sun dauke salati domin yanda yake kwance kamar matacce ba wanda ya yi tunani akwai kingin rayuwa a tattare da shi.
Su ma su Alhaji Kabiru, wato Baba shi da Alhaji Inrahim da sauran iyalan su, ko da su kaji labarin abin da ya faru ya yi matuk'ar razanar da su nan take suka zo da kan su domin tabbatar da gaskiyar al'amarin, aiko suma da suka gan shi a hakan sai da suka tausaya mashi,
Da hanzari suka kinkime shi aka saka shi Mota Uncle Musaddiq ne yaja Motar suka nufi hanyar Asibitin su da shi.





*ᏚᎻᏆN ᏔᎪNᎬNᎬ ᎪᏚᎪᏞᏆN ᏚᎪ'ᏆᎠᏌ ᎷᏌNᎪFᏌKᏆ*

Ku dai ku kasan ce tare da ni a next page domin jin asalin labarin Sa'idu munafuki, so much thanks😘😘😘 luve more my fan's
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora