030

126 10 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

EPISODE>>>30

Ita kam Fatima ba abin da take tunani sai ikon Allah domin dai bata ji lokacin da Mummy ta bada wasu kaya a bawa Hajiya Kaka ba, dan lokacin da Mummy na bada sak'o ana kawo mata har Allah Ya isa take mata shi ya sa ta daina aiko mata komai dan shafawa kan ta main lafiya,
A sannan Fatima ta d'ago da abin da yake k'ok'arin lurar da ita, ta ce "Wlhy Uncle na manta ban dauko ba, suna cikin mota."

Ya ce "Ok to bara na koma na dauko kayan.!."
daman ya yi hakanne domin kub'utar mata da kayan ta, sabida ta wannan hanyarce kadai yake ganin zai iya bi domin kwato mata kayanta ba tare da wata matsalaba, domin yasan mahaifiyar shi sarai da tsabar son abi duniya.

Ba tare da b'ata lokaci ba kai tsaye ta kira sunan Fatima,
Fatima ta'ansa cikin mugun tsoro tare da cewa "na'am Hajiya"

Ta ce "To halan wanne shegen ne kike jiran yazo ya kwashe maki wad'annan raggad'ud'an?."

Aiko cikin murna da farin ciki ta k'araso wajen da kayan suke ta dinga dauka guda-guda tana sakawa a cikin jakar ta.

_Haushi duniya dana lahira dik yabi ya dame Aunty Rukayya, dan ji take kamar ta dank'o wannan jakar a hannun Fatima ta jefa ta a wuta tak'one k'urumumus har da kayan da ke cikin ta.
Ita kam Hajiya Kaka gaban ta gad'i, jiran isowar kayan da aka zo mata da su kawai take ba abin da ya dame ta.

Uncle Mukhtar tsaye ya yi yana kallon Fatima,har ta gama kwashe kayan gabad'ai sannan taje ta 'aje su a mazaunin su, a sannan ya samu fita daga cikin gidan.

Direct wata babbar Super Market ya nufa...agurguje ya had'o ma Hajiya kayakki barkatai-barkatai .....kama daga Turmin Atamfa biyu super holland Turarukka kala-kala ,Mayukka, Tokunan wanka iri daban-daban gabadayan su kuma dik tsadaddi ne ..sai da ya cika mata wata babbar leda bak'a sannan ko minti biyar ba'ayi da tafiyarshi ba ya dawo gida.

Wa'iyazu billahi, murna a wajen Hajiya Kaka kan ba'a cewa komai ,,kamar yau ne ta fara ganin irin wad'annan kayan a wajen ta, sai albarka take ta sakawa Mahaifiyar Fatima,
Ita kan Aunty Rukayya haushi dik yariga gabadai ya'ishe ta bata san lokacin da tamik'e tsaye taba su waje ba ta koma daki cikin zafi tayi kwanciyar ta a saman gado.

******

_Washe gari da sassafe Sa'idu muafuki shi da iyalan shi gabadai suka shirya tsaf suka dauki hanyar zuwa gidan su Alhaji Kabiru domin yi masu godiya da abin da suka mashi.
Akan hanyar su ta tafiya ne Sa'idu munafuki ya tsinkanyo Fatima ita da Binta diyar Alhaji Muttak'a, suna tsakar tafiyar da suke suna labari wani matashin saurayi ya tsaida su a hanya yanai masu magana, da alama ma wani wajen ne yake nema sunai mashi kwatanci.

_Nan da nan Sa'idu munafuki Ya yi wani dan guntun murmushi na mugunta ,domin ya dade yana jiran ganin wannan ranar ta zo mashi.
Su dai iyalan shi gaban su gad'i sai famar tafiyar su suke yi babu k'ak'k'autawa domin dik a cikin su ba wanda ya halkanta da abin balantana ma ya tsaya kallo sabida abin da ke gaban su kad'ai suka saka a gaba.

*****

_Abangaren su Balkisu kuwa tun lokacin da suka fad'i a wajen sumammi, ba su suka farfad'o ba sai misalin k'arfe 7am, kowa a cikin su tunanin wannan mummunan abun da suka gani a lik'e ga bangon yake.

Ammie ce ta danyi k'arfin halin tambayar Balkisu da cewa "Anya kuwa abin da na gani jiya a daki na da gaske ne kuwa? Ko dai mafalki ne? skeleton fa!"
Ta karkare maganar ne tana mai zazzare idanuwan ta a waje.

Cikin rawar murya Balkisu ta ce "Wallahi Ammie Nima jiya nayi wani irin mummunan mafalki mai cike da ban tsoro...."
Nan dai ta kwashe komai ta fada mata, sannan ta kara da cewa "Ko da na falka da wani mugun tsoro a gurguje na shek'o da gudu wajen ki daniyyar na gaya maki abin ke faruwa, shi ne Nima na ganshi lak'e a saman bangon dakin ki.!"

Sai da ammie ta d'an numfasa na karfin hali kafin ta ce "Dama Lubancy ta gaya mani komai dangane da wannan Bokan Minsinkyu, kuma Nima exectly jiya irin wannan mafalkinkin ne naki nayi, sannan kuma hakan yana nufin cewa Boka Minsinkyu na neman mu a wajen shi cikin gaggawa.

Nan take Balkisu ta fashe da wani matsanancin kuka ta ce "Ni wlhy Ammie ba inda zanje, wallahi wannan bokan bashi da Imani kuma bashi da tausayi, Ni gaskiya bana son wannan aikin wallahi na fasa ma auren Mukhtar d'in, Ammie dan Allah ki ce ya k'yale mu hakanan.!"
Duk a cikin wannan matsanancin kukan take yin wad'annan maganganun.

Basu ankara ba, suka ji an soma yin magana a bayan su cikin wata 'yar sililuwar murya ta ce,
"Ku ko Ina kuka tab'a ganin inda shahartaccen Boka a wajen tsafi ya yi Imani?, dan haka maganar a fasa ma bata taso ba, tunda har kuka kawo kukan ku a wajen shi, to ko fa sai an kai k'arshe.!"
Cikin wani irin mugun firgici, ko waccen su ta waiwayo ta bayanta tare da mai da duban su a wajen da sautin wannan muryar ke fitowa
Sai dai da mamakin su me zasu gani?.

Wata irin b'ullumar mage ce bak'i-k'irin a bayan su Idanuwan ta bulaluwa sharkaf, tana washi masu bakin ta alamun ita taga maiko a wajen, wanda hakan yasa suka tsinkanyo hakoran ta zago-zago kamar na Damisa sannan gashi tana ta famar tunkaro wajen da suke,
Aiko cikin zafin nama ..ko waccen su ta mik'e tsaye ta neme hanyar fita daga cikin d'akin aguje,

Sai dai wani abin ban haushi, sai da suka kusan kawowa daf da kofar fita daga cikin d'akin, su kaji an ja kofar da k'arfi an rufe ta gamm......
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Where stories live. Discover now