049

135 9 0
                                        

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

Start on 28/5/2020

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM

Ina rok'on Allah Ubangiji ya gafarta maki Mom Hadiza Allah ya yi maki rahma Allah yasa Aljanna ta zamo makoma a gare ki Allah ya haskaka k'abarinki da rahmar sa tare da dikkanin al'umman musulmi wada'anda suka riga mu gidan gaskiya😭😭😭Allah ya kyautata tamu idan tazo, Ameen yarabbi
_______

Episode 49

_A hankali ta jefa k'afafuwan ta a cikin gidan sannan ta soma tafiya cikin wasi-wasin da zuciyar ta ke mata mai hade da fargaba, sai Allah-Allah take kar Hajiya Kaka ta riske ta. tafiya take sut sut sut kamar wata babbar barauniya, tana ida k'arasowa a cikin gidan idanuwan ta suka fara yi mata tozali da Aunty Rukayya, yau dand'e kicihi ita ke sharar gida har wajen kofar Hajiya Saudat da kofar dakin Baba, yau aka sharo abin da bata tab'a yi ba, wanda hakan yasa dik wanda ya shigo a cikin gidan da mamaki yake fita, hatta ma wadanda ke gidan mamakin ta ya hana su b'arkata aikin komai

Ita kuma daman abin da take so kenan k'ari da k'arau ma ba komai yasa take yin dik wannan ba sai dan azabar da Fatima zata sha ta dad'a k'aruwa a wajen Hajiya Kaka, domin ranar yau haka take jinta kamar ranar Babbar sallah sabida tanada tabbacin yau Allah kadai ke iya amsar Fatima a hannun Hajiya Kaka

Tun yanda sukayi 4eyes da Fatima tayi saurin kauce fuskar ta daga kallonta dan kar ma takai ga b'ata mata lokaci wajen gudanar da shirinta na mugunta.
Fatima dama ta lura da hakan a fuskar Aunty Rukayya domin tun yanda suka yi ido hudu da ita, cikin mugun hali ta janye fuskar ta daganan sannan ta sake turmuk'e fuska sai kumburi take kamar ta fashe, ta san da walakin goro a miya.

Tafiya take amma gabanta nai mata ihu akan fargabar had'uwar ta da Hajiya Kaka, tana cikin yin tunane-tunanen yanda zata b'ullowa wannan mugun al amarin da take jin shi tamkar fitar rai a jikin ta, nan Ta tsinkanyo muryar HajiyaKaka tun daga cikin palour take cewa "Aje man abincina anan bak'ar munafuka, sannan wallahi dik kika kuskura kika gudu dik sanda na kamaki ba zan maki da kyau ba bak'ar shegiya 'yar malafar-uba mai fuskar Tunkiya mai k'afafuwan Jaki.!"

cikin wata mugunyar gidimewa. Fatima ta duk'a k'asa kamar farar kura ta ajiye kulolin a k'asa.
Aiko Hajiya Kaka kamar daman jiraye take Fatima ta duk'a k'asa, tayi wata irin hiranyowa sama daga cikin dakin aguje rik'e da Addah kamar wata 'yar ta'adda.

Ko da ta ida mik'ewa tsaye ta hango Hajiya Kaka na tunkaro wajen da take cikin wani mugun yanayi (na idan na kama ki kasheki zanyi na huta)
Aiko nan take k'afafuwan Fatima suka ce kazat-uba ai dole ne muje shan'iska, Innadillahi. wata irin arniyar walkad'owa ce da fatima tayi daga baya kamar jirgin yak'i, aguje ta fece daganan sai dai kuma wajen fita waje ne ke da matuk'ar wahala a gare ta ..domin Aunty Rukayya ce ta riska tsaye a bakin k'ofar fita waje tayi katutu dik tabi ta tattwale k'afafuwa kamar mai sabon kaciya, wai ita anan tarun hanya ce tayi a maimakon ta janyo kofar gidan ta kulle gabadai sai kuma Allah ya b'addar mata da dubarar yin hakan.

Sai da Fatima tayi kusan kawowa daf da Aunty Rukayya ta waiga ta bayanta ta hango Hajiya Kaka aguje iyakar gaskiyar ta kenan idan ta cin mata rafka mata wannan Addar zata yi, cikin hanzari ta maida duban ta ga Aunty Rukayya dake tsaye sai murmushin mugunta take binta da shi, aiko kamar tayar mota Fatima ta duk'e k'asa bata san lokacin da tabi ta OC'n Aunty Rukayya ba ta wazge.

WAHALA DA GATA season1Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon