*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*EPISODE>>>39
Kafin suyi wani yunk'urin aikata wani abu, tini su kaga wata hadaddiyar mota ta parker dai dai da wajen da suke, daga bi sani kuma suka jiyo sautin fitowar wata zazzak'ar muryar daga cikin wannan motar, tanai masu magana cikin wani tattausar lafazi kamar haka
"JI MANA 'YAN MATA RUND'UMAMMIN GANDAYE! KUZO MANA NA RAGE MAKU HANYA YAFI WANNAN YAWON DA KUKE TA FAMAR YI HAR KUN FARA GAJIYA, KUNGA KUMA BUGU DA K'ARI MA MOTA TA AKWAI AC A CIKIN TA SANNAN KUMA GA K'AMSHIM WANI HAD'AD'D'EN TURARE DA NA FESA A CIKIN MOTAR DIK KUMA DOMIN KU, KUZO MANA NA RAGE MAKU HANYA KARKUJA MA KANKU WATA MUMMUNAR ASARA KUNNNJI.!"
Cikin wata kasalalliyar murya ya katse zancene daganan domin ya san wannan sarewar muryar tashi ta ishe shi makamin saurin sa ce zuciyar bil'adam har da ma wasu sassa na jikin su da yake fatan samu.Su Hajiya Ammie kam tuni wannan muryar tayi bala'in tasiri da kwarjini a cikin zukatan su.
Har dai sun so su tsaya domin rage masu hanyar kamar yanda su kaji ya fada sabida har acikin zunzurutum mazurarin kogon zuciyar su su kaji shigar wannan hadaddiyar muryar ta shi da su kaji fitowarta kwatsan da k'ok'arin taimaka masu, nan da nan hankalin su yad'an kwanta domin har aran su su kaji sun gamsu da shi sabida har wata zuciya ta fara basu kwarin gwiwa wajen biyar shi wata kila ma ya kai su har inda zasu tafi...saidai kuma lokaci guda suka juya baya ko kallon motar ba su sake yi ba suka ci gaba da tafiyar su cikin salama.Gogan tin yanda yaga sun saita hanyar su ta ci gaba da tafiyar su alamu suka nuna mashi basu yarda ba ne, nan ya ji shi wani iri, sabida ganin suna son yi mashi buk'ulu ne akan Naman su k'iri-k'iri gashi yana kallo, har da hadiye yawun k'arfin hali, domin tun lokacin da yaji alamun shigowar bil'adam a cikin wannan duniyar tasu ta aljanai, tuni ya tanade dik wasu kaya da zai iya buk'
ata wajen harkar soye-soyen Naman jikin su,
Sabida yaji a jikin shi cewa wannan babbar harka ce ke ta famar tun karo shi a yau dinnan bama sai gobe ba, shi ya sa dik wani kwakkwaran shirin da ya kamata ace ya aiwatar kafin zuwan su yariga da ya gama, zuwan sune kadai yake jiran gani don ya san wannan abin shi yafi komai sauk'i a wajen shi, shi ta sa yayi gaggawar shirya ma kanshi wata gagarumar liyafa a gidan shi ta cin Naman su AmmieNan da nan ya gyara saitin hanyar shi, yabi bayan su, yana mai cika masu kunnuwa da shegen hon din motar shi sai bala'in k'ara kamar ya fasa masu kunnuwa, su Ammie kan tuni abin ya yi matuk'ar kai su mak'ura amma haka suka daure suka ci gaba da tafiyar su, sabida karar wannan hon din ya yi bala'in damuwar su hanik'an domin har sun fara jin kunnayen su nason kasa dauka.
nan da nan Balkisu taci maganin tauri ta cije ta matse ta tsaya cak babu ko alamar jin tsoro a tattare da ita domin dik a tunanin ta mutum ne shi ma kamar ita shi ya sa bata wani damu ba tunda dama wannan abin ba sababben abu bane a wajen ta ba, shi ma kuma a daidai wannan lokacin ne ya tsayar da motar shi waje guda a cikin ruwan sanyi kuma ya dakatar da dannan wannan Miskilin hon da yake ta famar samun su da shidik dan sabida k'eta da kuma huce takaici,
Tsayawar da yaga tayi shine yak'ara tabbatar mashi da cewa lallai tariga ta gama zumduma a cikin tarkonsa, Nan da nan yaji wani irin hadadden farin ciki ya lullube shi, yana mai k'ara jinjinawa kan shi, domin Har ya dan fara canza kala ta cikon wankan yadan fara shamk'amshi, wai shi ala dole Ya kasance me wani hadadden Gaye mai saurin sace zuciyar 'yam mata tsaf su dawo gare shi shi kuma daman kayan soye-soyen su suna kusa dan sabida guje ma yawan jinkiri, domin a halin yanzu har wani k'arin matsayi tare da karama abin teste harda su Yaji da kayan kamshi ya tanadar ma kanshi, sannan kuma ya yi alwashin yau kwattaho yattaru ba wanda zai iya hana shi ai watar da abin da ya yi niyyar aikatawa a gare su dan shi ba tab'a ido biyu da babbar harka irin wannan ba kuma yana ji yana gani da ran shi da lafiyar shi ya yi gangancin barinta har ta kaiga sub'ce ma shi ba.....
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
![](https://img.wattpad.com/cover/227203736-288-k316986.jpg)