002

338 31 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             _{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
            *«•••••••»*

*➡️002*

 

Aunty Rukayya na bud'e k'ofa, da k'arfi aka ingizo k'ofar sai da ta tashi fad'uwa k'asa cikin zafin nama ta daidaita tsayuwarta Sannan ta samu damar maida dubanta ga  masu shigowar cikin d'akin, wani d'an siririn tsaki ne wanda bata san lokacin fitowarsa ba tajaaa kafin ta kaiga kulle kofar.
              Cike da mugun jin haushin wad'anda suka shigo cikin dakin ta koma wani bangare na daban ta tsaya tare da yin k'icin-k'icin da fuska kamar wadda akayi ma albishirin mutuwa.

             Hajiya Saudatu da  Alhaji Kabiru,  su na  shiga cikin dakin suka nufi wajen da Hajiya Kaka  take, da hanzari Hajiya Saudatu ta samu nasarar dank'e hannunta wanda ke rik'e da bulalar.
            Cikin wani mugun huci kamar Maciji Hajiya Kaka ke magana tana cewa "Barni na gama cin ubanta tukunnan Rukayya yanda ko gobe ba zata yi sha'awar aikata ma wani makamancin haka ba Kyale ni dan Allah" tana magana tana shashshek'a kamar wadda ta d'auki buhun Hatsi.
           Cikin muryar fahimta taji an soma yi mata magana wanda hakan ya k'ara tunzurar da ita ta dalilin jin wannan k'ak'k'aurar muryar da take tamkar garwashin wuta a gare ta
              Daga nan kuma taji ta neme b'acin ranta ga Fatima kuma ta rasa gabad'ai ya tattara ya koma wajen Hajiya Saudat dan a halin yanzu ko ji take ko shak'e mata wuya zata iya yi har sai taga ta d'auke wuta tukunna sannan ta sarara.
           Hajiya Saudat ta ce "Haba Yaya! haba Yaya!!yanzu dan girman Allah ko wanne irin laifi ne Yarinyar nan ta maki ba zaki bari harda safe ki hukunta ta ba amma yanzu Fisabilillah kamar ba a cikin dare ba  kina ganin wann.........."

             Cike da wata bak'ar masifa ta dakatar da ita ta hanyar d'aga mata tafin hannunta guda tare da gwabce gudan daga rik'on da ta mata ta ce "Ke dan Allah ja can bak'ar matsiyaciya tantiriyar 'yar-iska, ke har kin san wani abu wai shi Dare, kin wani yi ma mutane zabun yak'an kamar zaki dake su wai ke nan mai wa'azi ko? Ai wannan wlhy iskanci ne da samun waje da har zaki shigo ma mutane cikin d'aki kai tsaye babu ko neman izini to dan kina wa?" ta karkare maganar ne tare da Jan wani dogon tsaki sannan ta  k'ara da ce mata "Mahaukacciya kawai mai zuciyar dabbobi..!"
           Sosai wad'annan mugayen kalaman suka b'ata ran Hajiya Saudat, har zata bud'e bakinta ita ma da k'ok'arin maida mata martani Alhaji Kabiru ya dakatar da ita ta hanyar yi mata nuni da ta saka mata ido kawai domin shima ya san halin Hajiya Kaka sarai kamar yunwar cikinsa idan har ta tashi b'arje masifarta ko waye kai ba zata ji kunyar raga maka ba, cikin tausasa murya ya shiga tambayar abin da ke faruwa, sai da tad'an ja tsawon lokaci kamar ba zata yi magana ba wajen ya yi tsit kamar babu kowa a wajen sai shashshek'ar kukan Fatima dake tashi kad'an kad'an kamar kukan tsuntsaye, sai can kamar abin dole ta soma mashi bayanin k'arya da gaskiya kamar yanda Aunty Rukayya ta gaya mata tare da sakaya ita ma ta ta k'aryar a ciki dan k'arama abin Citta. Ita dai Fatima duk'e kawai take tana sauraren Shata Hajiya Kaka babu halin yin magana balle ta samu damar fad'in gaskiyar  dan ko da ta fad'a Hajiya Kaka zata iya dafa Alkur'ani ta k'arya ta tare da bugun gabar ita tafi k'arfin ta mata k'arya sabida  indai wajen k'arya ne da kwarewa wajen iya bala'i da masifa da munafurci to zan iya ce maku Hajiya Kaka ko bata zo sahun gaba ba zata zo mabiyiya sannan ta k'ara da cewa "Ni kuma na rantse da Allah ko mutuwa zata yi sai ta wanke shi tsaf sannan zata kwanta, Fak'at.!
          Alhaji Kabiru sosai ya gamsu da dik maganganun Hajiya Kaka babu alamun k'amshin gaskiya a cikin su domin yasan Fatima ko kad'an ba zata iya aikata d'ai daga cikin abin da ta zayyano mashi ba sai dai  hakan yad'an cije ya dubi wajen da Fatima take ya ce mata "Kinga amshi ga Fitila kije ki  wanke zanen tunda har ta rantse ba zaki kwanta ba har sai kin wanke zanen." 
            Fatima "To Baba" kawai ta iya cewa da shi domin ta galabaitu hanik'an a hannun Hajiya Kaka.
              Ta tashi tsaye da hanzari tare da d'ingirisa dan k'afarta ta d'an samu matsala kad'an ta sanadiyyar mummunan takin da Aunty Rukayya ta mata, ta amshi fitilar a hannun shi cikin girmamawa da darajawa sannan ta fita waje wajen gabatar da aikin.
             Cike da wani zuzurutun tausayi suke binta da kallo har ta fice daga nan, haka su ma su Aunty Hajiya Kaka idanuwan su nakan Hajiya Saudat wanda akan bak'in ciki  ji take kamar ta hira sama ta far mata har sai ta huci takaicin da take ji a gare ta tukunna, kai tsaye suka ji Hajiya Kaka ta sako masu  magana da cewa "To tunda an gama ganin k'om sai a tafi a barmu mu sarara ko.!"
       Ba tare da Baba ya ce da ita ko k'ala ba ya juya ya bar wajen da hanzari sabida gudun kar zuciyar shi ta kai inda bayason ta isa, kasan cewar Hajiya Saudat na bayan shi kuma tana d'an nesa da shi kafin ta ida walkad'awa ita ma ta rufa mashi baya tuni ta tsinkanyo Aunty Rukayya na fad'in "Hajiya dubi munafukar matar nan yana fa fita kinga zata rufa ma shi baya kamar wata dak'ik'iya!"
                  Wata irin zazzafar tsayuwa ce tayi daga wajen da take ba tare da ta juyo ta bayanta ba dan sosai wannan maganar da ta doke dodon kunnenta ta yi bala'in bak'anta mata rai ganin ko a haife ta haife ta amma take gaya mata irin wannan banzan kalamin, a fusace ta juyo ta kalle Aunty Rukayya da ita sam bata yi tunanin ta ji ta ba..........!
*Follow me on wattpad and vote— Smart_Feenert*
*Be smart*
*Pls shere*

WAHALA DA GATA season1Onde histórias criam vida. Descubra agora