042

111 8 0
                                    

♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

EPISODE 42


Tun lokacin da suka fito daga gidan su Alhaji Kabiru, tun a bakin hanya ya samu damar raba tafiyar su shida iyalan shi,
domin nuna masu ya yi zai tafi Shago ne ya dubo abin da ke wakana acan sabida yad'an kwana biyu bai lek'a ba, kasancewar yana da yaran da ke kula mai da sana'ar shi.
Ba abin da ya iya fitowa a cikin bakin su sai kalmar "Allah ya kai lafiya.!"
ya ce " Ameen " har ya saita hanyar shi wajen tafiyar yaji dai daga cikin yaran shi Umar ya ce "Abba zan bika" ya ce "a'a Umar kayi zamanka mana, kabi Iyayanku ku koma gida yanzu zandawo!"

da yake yaron ba mai bidar diddigi ba ne, ya ce "To Abba a dawo lafiya !"
sanna suka wuce gabadayan su.
shi kuma a sannan ya maida gurin wajen zama a gareshi domin bai daga daganan ba har saida ya daina ganin ko k'urar su ta tafiyar,
Sai da ya furzar da wani irin zazzafan iska a cikin bakin sa na munsfurci sannan ya ce "Alhmdu lillah"
agurguje ya bar wajen cikin gaggawa ya nufi hanyar da zata sadashi da babban Titi.
Sauri sauri gudu-gudu yake tafiya domin samun abin hawa cikin gaggawa .. domin ya samu ya isa da wuri wajen kai rahoton gulma, ko tafiyar minti biyar baiyi ba ya samu wani Machine ya haye direct sai hanyar Asibitin su Alhaji Kabiru aka nufa da shi.
dik da wani irin mahaukacin gudun da mai Machine d'in yake amma haka ya dinga takuramai akan yak'ara gudun sosai ko da zai k'ifta girar shi kawai ya ganshi a cikin asibitin tsunbulbul, haka ko akayi,
Domin yanda mai machine din ya cika babbar riga da iska yaja giyar Machine d'ik ya taka Totur dinnan dakarfin Allah ya dinga zund'ar gudu kamar zai hira sama...dik inda suka bi suka wuce sai an dinga b'ub'b'ur ma masu Ashar, akan irin wannan mahaukaci gudun da suke yi kamar su tashi sama.

......

B'angaren su Fatima kuwa, Binta ce diyar Alhaji Mu'azu Fatima tad'an girmeta kadan da shekasa guda
Tazo ta samu Fatima har gida ta ce mata wata k'awarsu ce ba lafiya Idan za taje sai suje su dubata tare, bata aminta ba sai da taje ta gayawa Hajiya Kaka ta amince tare da gargad'in cewa karta sake ta bari ta nemeta ta amsa da "To Hajiya" sannan suka wuce.
Akan hanyar su ce ta tafiya ce suka hadu da wani mata shi ya yi parking din motar shi ta wajen su suna tafiya, sannan ya fito waje yana tambayar su gidan wani bawan Allah, sai akayi sa'a kuma da Binta ta san wajen ta tsaya tana mashi misali
Fatima ta koma wani gefe na daban ta tsaya tana jiran ta, a lokacin da Binta ke mashi masalin ne sai ga giftowar su Sa'idu Munafuki ta wajen su sun wuce ba tare da kowa ya lura da wani a cikin su ba in banda shi Munafukin da tin lokacin da ya tsinkanyo su yake ta famar rabe-raben idanuwa kamar Bakuru.

......

Aunty Rukayya ce ta fito daga cikin bedroom anan palour'n ta tarar da Hajiya Kaka zaune ta hakimce a saman doguwar kujera ta zaman mutum ukku kamar wata Tihwa tana debe ma faratan ta datti, cikin wani salon munafurci ta zo ta zauna saman d'aya da ke saiti da ta Hajiya Kaka ta ce "Yauwa Hajiya, d'azu kamar muryar Binta diyar Alhaji Mu'azu ce naji a cikin d'akinnan.?

Cikin yatsine fuska kamar kashin Kaji Hajiya Kaka ta ce "Eh ita ce! har ita waccen Shanshani Uwar yawo ta bita sunyi gaba wajen yawon su na Iskanci na biyar mazan banza da suka saba!."

Aunty Rukayya ta d'an sake wani murmushin munafurci domin taji antab'o mata inda yake yi mata kaikayi, kan tak'ara cewa wani abu, taji Hajiya Kaka ta katseta da cewa wai kingin abincinnan na sahur ansamu wanda za'a bawa shi kuwa? dan karya lalace tunda yau kin san mun tashi da Azumin watan Ramadana babban wata mai Alfarma.!"
Cikin wani mugun b'acin ran katse mata hanzari wajen yin gulma da Hajiya Kaka tayi ta ce "Tun d'azu da Fatima zata yi wanke-wanke naga ta tattara shi ta kai gidan su Ladidi.
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Where stories live. Discover now