*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*ᎬᏢᏆՏϴᎠᎬ>>>27
_Cikin rawan murya ta ce "Na'am hajiya magana kike yi ne?"
domin tabbatar da abin da kunnuwan ta suka jiyo mata dan ta san da sun amshe jakar a hannun ta to dik wani abin da ke cikin ta in dai sabo ne ta haramta da shi."Iyyeee, to kinji wani sabon salon iskanci kuma yanzu da tazo dashi ko Rukayya?, har da su kara tambaya taji dand'e raini ko?,"
Da karfi ta sake ce wa "To billahillazi dik kika bari na mike tsaye na cin maki a dakin nan wlhy ko na lahira sai yafi ki jin dad'i bak'ar makira mai bakin Jab'a._Cikin wani raki'in tsoro ta dinga takowa a hankali tana tafowa cikin wasi-wasi har tayi kusan kawowa wajen su ,nan da nan taji gaban ta ya dinga duka uku-uku
Tun kan ta ida kaiwa wajen da suke Aunty Rukayya ta yi zubun ta fizge jakar a hannun Fatima sai da hadadden belt din jakar ya fazge, sannan ta saka hannunta dand'e k'eta ta fazge zip din jakar sannan ta zubar da kayan gabaki daya ta watse su a saman carpet.Sai dai abin da suka gani yayi matuk'ar basu tsoro, domin dik abin da suka gani ba wanda suka santa da shi a ciki dik sababbin kaya ne kuma manyan masu bala'in tsada kamar ba'a san ciwon kud'i ba, irin su atamfinne leshi matiriyal shaddodi dogayen rigunoni qananan kaya ...kama daga riga da sket har ma da riga da wando doguwar riga kusan kala goma sha biyar,, nan take Aunty Rukayya ta sake kallon jakar da kyau domin tun dazu bata halkanta da yanda take ba sai dai da mamakinta wata hadaddiyar Jaka ce kalar black and pitch color's ce wadda gabadayan ta duwatsu ne a gewaye da ita kamar dogaran Sarkin Makkah.
_Nan take wani hamshakin bak'in ciki ya bayyana a fuskokin su karara kamar su saka ma kayan gabaki daya fetur su kone su akan haushi.
Nan take Hajiya Kaka ta ce "To kuma ke K'aramar shegiya debabbiyar albarka dik ina kayan da kika tafi da su ne?."
murya na rawa ta ce "Gabadaya anyi sadaka da su domin dik sun yayyage"."Iyyeeee lallai wannan mahaifiyar taki ta cika Babbar tantiriyar Munafuka, Yau ke Rukayya ki ji man wannan bak'in iskanci, To Allah ya isar man wlhy na barku ga Rabbul-samawati dan shi kadai zai iya fidda man hakki na dake kan ku babbak'un munafukai in k'asa da wuta, wato kenan munafurci na ne aka zauna yi ba dare ba rana ko? ana ta zagina, toh wallahi ban yafe ba ko A. aka ambata a cikin sunana wallahi har abada bazan taba yafewa ba Allah Ya isa a gareku sheguna babbak'un azzalummai.
Ita dai Fatima ba abin da take yi illa kuka,
Bata ankara ba taji Hajiya na fadin "wallahi ko wadannan tufafin sun haramta da ke dan wallahi har aba indai wadannan tufafin ne ba zaki taba saka su a jikinki ba munafuka, dan Allah Rukayya kwashe man tifafin gabadai ki ajiyewa Nusaiba su duka, wallahi kuma kinji narantse.""Hmm Hajiya ai kedai ki barsu kawai, a dai b'oye su a karkashin gado har lokacin da suka lalace sannan azuba a shara dan kin san Babban Munafukinnan Mahaifin su, ya ce bai yarda ya sake ganinta da tufafi ko waddanne iri ne ba indai bashi ya d'unka su ba da kan shi ba, Idan ko har ya samu labarin ta saka ko a b'oye ne, shi kuma daga wannan ranar ya rantse da Allah ba zaya sake kawo su gidannan ba."
"kuma fa kina da gaskiyar ki, ai kamata ya yi kice man Hamana dan nafi gane shi da wannan sunan, d'an shegiya.!"
Ta k'ark'are maganar ne tare da maida duban ta ga kayan Fatima ta ce "Iyyeeee hmm wai iskanci, dan Allah duba man wad'annan babbak'un wulakantattu wad'anda su kayo gadon son abin duniya har da wai wata atamfa mai suna english, wato ni na saka ke ma ki saka ko? To wallahi wad'annan kayan har abada ba zaki taba saka su ba in dai ina da rai da laafiya a cikin duniyar nan bakar makira, wai ba zaki tashi ba ne ki b'aceman da gani ba sai na kai ga sassab'a maki halittar jiki shegiya komud'ad'd'iyar banza."Aiko cikin wani matsanancin kuka Fatima tamik'e tsaye a guje ta nufi hanyar fita waje, sai jin tayi ta kaure wani kakkarfan abu abakin kofar ta ta fita waje, ba tare da ta ma tsaya duba ko menene a wajen ba ta tashi wazgewa aguji domin taji bala'in tsoron faruwar abin, amma da mamakin ta Sai jin tayi andanke hannun ta takin-takin ta kasa ko dagawa daga wajen da take, cike da firgici ta juyo fuskarta domin ganin ko wanene dan tana da tabbacin yanzu ta ta ta kare sai dai wata amma ba ita ba.
*****
_Ta Bangaren Sa'idu-munafuki kuwa tun karfe 6:30pm aka samu ya farfad'o, aiko cikin gaggawa likitoci suka k'ara yowa kan shi .,suka sake yin dik wani gwaje-gwajen da ya kamata tare da rubuta mai magungunan da zaya iya amfani da su, ba tare da bata lokaci ba sai ga wata Nurse ta shigo da ledar magungunan kasancewar akwai permacy a cikin asibitin, babu wani bata lokaci aka rubuta mai sallama domin jikin nashi kam dik ya wartsake, sannan Uncle Aminu da Uncle Mu'azzam tare da Uncle Musaddiq suka dawo da shi gida, dan a wannan lokacin su kad'ai ne ke asibitin tare da shi sai sauran ma'aikata, domin su ma su Alhaji Kabiru tun lokacin da su kaga anyi nasarar shawo kan matsalar su Uncle Uzaifa suka wuce da su gida.
•••••
Su na shigowa kwanar su Sa'idu-munafuki tun daga cikin mota diyan shi suka fara hango shi, shi da su Uncle Musaddiq zaune a bayan motar, kasan cewar farin glass ne tass a motar, sannan kuma Uncle Musaddiq ya dan kunna fitilar motar yana bincikar sauran maganin da ya fad'i k'asa daga cikin ledar.
_Aikuwa nan da nan diyan nashi suka dauki ihun mur'na kamar k'ananan Yara suka nufi cikin gidan sunai ma iyayen su albishir da dawowar Mahaifin su gida lafiya, nan fa mur'na da farin ciki yab'arke a tsakanin matan shi har dasu kukan farin ciki,.... sallamar da suka ji ce ta dawo da hankalin su a cikin duniyar da suka shiga ta kukan farin ciki, cikin bala'in kewar shi nad'an wani lokaci tare da farin cikin ganin shi gaba dayan su suka ruftuma su kaje wajen shi suka rugume shi kamar ya fad'i k'asa cikin wani mugun farin ciki marar misiltuwa.
_Su kam su Uncle's Aminu ko wannen su ya yi tsaye carko-carko yana kallon ikon Allah domin su ma abin ya yi matuk'ar sosa masu zuciya kamar su fashe da wani mahaukacin kuka da ke ta famar taso masu a cikin zuciya ga yanda su kaga matan shi da diyan shi suna murna hadi da kukan farin ciki na dawowar mijinsu cikin koshin lafiya, ma sha Allah.
Ba tare da wani bata lokaci ba suka ajiye kayakkin da suka zo mai da su har da magungunnan shi wanda dama sun gaya mai yanda zaya sha su tun a asibiti ...sannan suka nufi su ma hanyar da zata sada su ga gidan su.
Daga nan unguwa kowa yaji dawowar shi gida cikin koshin lafiya, ba wanda bai yi murna da farin cikin dawowar shi ba sai munafukai irin shi.
*****
_Abangaren su balkisu kuwa, kwance take tana cikin jin dad'i take kwasar baccin ta a saman wani hadadden gadon tare da fitar da wani zazzafan minshari kamar kwad'o..........
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share
![](https://img.wattpad.com/cover/227203736-288-k316986.jpg)