016

149 12 1
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

➡️016

Matan Sa'idu munafuki ne su biyu Asma'u da Sumayya sannan matar Alhaji Muttak'a Huwaila, a daya bangaren kuma diyansu ne ke biye dasu a bayan su kamar Jela,
Asiya da Umar su ne d'iyan Asma'u, sannan Hajarue ita ce d'iyar Sumayya, sannan Humaira da Amiira da kuma Binta su ne d'iyan Huwaila matar muttak'a.

_Tun yanda su kaga su
Alhaji Kabiru ne a hanyar sun yi gaba da gaba da su, nan take cikin su ya fara mird'awa k'ulululu alamun ya burkuce kenan..😜
           cikin borin kunya murya na makarkata gaba dayan su suka shiga gaida su tare da yi  masu jajen abin da ya same Hajiya Kaka dik da dai su Alhaji Kabiru sun ka sa fahimtar inda jajen nasu ya dosa domin tsananin tashin hankalin da yake damun su ya ma fi karfin zukatan su domin ko kadan y fahimce abin da suke nufi ba akai.
       Nan dai suma suka amsa masu cikin tsananin tashin hankali sannan suka nufi cikin gidan, su kuma su  Sumayya suka nufi haryar fita daga gidan cikin mutuwar jiki suka dinga tafiya somai-somai kamar wad'anda kwayakwai suka fashe ma a jiki ba wadda ke ta ce ko uffan, koda suka kawo hanyar shiga gidajen su  su kayi sallama da junan su ko wacce ta shiga gidan ta cikin rashin kwarin jiki mai had'e da nadama abin da suka dinga fad'a.

Sai dai kuma abin da ba su sani ba shi ne, tsakanin Alhaji Kabiru da Alhaji Ibrahim ba wanda ya fahimta da abin da suke tattaunawa akai, dan burin su dik bai wuce su isa cikin gidan ba.

....

Suna isa daga ciki, suka nufato b'angaren   Hajiya Kaka domin sun tsinkayo yaron mutane gidan  a cikin palour'n ta  kamar wajen da ake cin wata babbar kasuwa.

Hajiya  Khadija ce matar Alhaji Ibrahim tare da diyar ta Aisha, sai matar Uncle Uzaifa, Zahra'u da diyanta guda biyu Sulaiman da Abdullahi sannan matar Uncle Almustapha, Asma'u Ita da diyanta Zainab da Maryam sannan Uncle Aminu da ke zaune a saman kujera rike da magani a hannun shi yana bata tasha amma tak'i amsa, sannan Aunty Rukayya dake kwance saman doguwar kujera riqe da danta khalifa sai Nusaiba da Marwan wad'anda basu dade da dawowa ba.

Hajiya  Kaka kam dik  takaici Ya riga da ya ishe ta akan ganin mai bi ma mak'iyiyarta wato Hajiya Khadija, dan yanda ta tsane Hajiya Saudatu haka ta tsane Hajiya Khadija hakan yasa ma Hajiya Khadija ta dauke k'afar ta a gidan ita da yaran ta sai dai Idan da lalura kad'ai zaka iya ganin su ko shi kuma ba zasu wani jima anan sosai ba zasu koma bangaren su, wanda hakan ya sa wannan abin ba k'aramin bakin ciki yake sakawa Hajiya Kaka ba musamman idan ta tsinkayo ta  a cikin dakin Hajiya Saudat Ita da yaran ta suna zantawa, kamar ta Zuba masu Man Fetur gabadai su k'one da wuta haka take ji.

_Sama da k'asa take ta harare-hararenta tana kallon kowa a wulak'ance  sai k'ara cika take tana batsewa sai suracin bala'in da ke fita a saman fuskarta na bak'in ciki da yake damun ta, sai dai  kuma  ba wanda ya kula da abin da ma  take yi balantana har ya iya damun su.

       Shi kam Uncle Mukhtar  mamaki kawai ya ke na  irin wannan halin nata dan yaga har yazu ta kasa gyarawa da kanta.
           Shi dai a ganin shi, mutane su baro k'ofar su suzo dubiyarka domin  tayaka bakin cikin abin da ya same ka  amma ka nuna halin ko in kula da su.

......

_Da  hanzari su Alhaji  Kabiru  suka ida shigowa daga ciki tare da tambayar abin da ke faruwa, kafin kowa ya ce da su wani abu tuni Hajiya kaka tayi kuzutt ta sharbe Amsar da cewa "meye ko in banda sharin waccen bak'ar makirar" tana mai nuna masu Aunty Zahra'u   da d'anyatsa. nan kowa ya shiga mamakin fitowar wannan maganar ta ta.

Su dai sun gani da idon su Mazuru ne silar wannan al'amarin kuma Aunty Zahra'u bata ma wajen a lokacin da abin ya faru shigowar su Hajiya Khadija shi ne shigowar ta ita ma sabida hayaniyar da tayi yawa, sannan koda ta shigo bayan ta gaida ta tare
da duba jikin ta had'i da yi mata fatan alkhairi sannan ta koma gefe ita kad'ai ta tsaya dan gudun wani sabon jidalin Hajiya kaka ashe ko anan ma bata tsira ba.
           Haka dai kowa ya shiga cikin zullumi tare da sak'e-sak'e a cikin ran shi. Daga nan ta k'ara cewa.,

"Na rantse da Allah tsakani na da waccen mugunyar (cewa da Aunty Zahra'u) Allah ya isar man wallahi ta cuce ni  har abada ba zan taba yafe maki  alhaki na ba, bak'ar munafuka kana ganin ta kamar ta kwarai amma zalincin da ke cikin wannan bak'ar zuciyar ta ta wallahi yafi k'arfin a kira shi da kafurci sai da abin da yafi hakan  kuma wallahi summa tallahi yau ba zata kwana a cikin gidannan ba na rantse da Allah sai tabar shi tunda ba gidan ubanta ba ne.!"

Cikin daga murya mai had'e da wata irin mahaukacciyar tsawa Alhaji Kabiru ya dakatar da ita da ta hanyar cewa " ya isa haka.!" da k'arfin Allah sai da Hantar Hajiya Kaka ta kad'a sannan dik wanda yake wajen bak'aramin firgitar da shi wannan tsawar tayi ba domin k'arfinta da k'ararta kamar wajen da transformer ta buga.
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere

WAHALA DA GATA season1Where stories live. Discover now