005

198 18 0
                                        

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             _{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

*➡️005*

ALHAJI SULAIMAN wanda shi ne mahaifin Alhaji Kabiru  shahartaccen dan kasuwa ne wanda ya yi suna sosai a zamanin sa yana da mata guda biyu, Maryama da Asiya

Maryama Ita ce mata ta farko da Alhaji Sulaiman ya tab'a aure shekarar su goma sha daya Allah bai basu haihuwa ba, dik dα rashin damuwar da basu yi ba na daga hankullansu wajen rege-rege wajen biyar malaman tsibbo ko kuma bokaye, sun dangana a gurin ubanagiji domin sun san komai muk'addari ne a wajen shi, tayu wannan Ita ce k'addarar da mahaliccin sammai da qasai ya yanke masu tun ran gini tun ran zane.

Suna cikin zaman su na Jin dad'i da walwala ba wani tsangwama balan tana wani mugun furuci daga wajen junan su.

Kwatsan sai ga  'yan uwan Alhaji Sulaiman sun saka su gaba akan suna buk'atar ganin jinin shi a kusa da su

Inda wata k'anwar mahaifiyar Alhaji Sulaiman Sa'adatu da ke mashi fada cikin zafafan kalamai, kamar haka "Ai kana da hurumin k'ara aure ba wai ka tsaya da macce shekara da shekaru ba ko b'atan wata balantana a samu damar yin b'ari, dan haka tin yanzu  idan har kana da wadda kake so to ka kawo ta wajen mu mugan ta domin mu yaba da hankalinta da kuma tarbiyarta idan kuma baka da ita Ni inada wadda zan hada ka da ita."

Ya ce mata "gaskiya shi bai shirya zama da mata biyu ba dan Allah Iyah  (kasan cewar haka yake kiranta da shi) ki daina wannan zance ni dai ina zaune da matata lafiya kuma ko kadan bamu tada hankalinmu akan wannan matsalar ba dan Allah abar wannan maganar Iyah."
Iyah ta ce  "eyyyyeeeeee  kai ana son a maka gata kuma kana son bijirewa to wallahi aure ko babu fashi kaji na gaya maka.!" ya ce "gaskiya shi bai da ra'ayin haka dan Allah tayi hakuri kawai."  Ai kuwa nan iyah ta fashe da kuka tace "Tunda  nake da kai ban tab'a fad'a ka fad'a ba sai yanzu da har kake musanyar yawu da ni Yau ni na shiga ukku, Na san  ko da ace mahaifiyarka ta na raye abin da zata yi maka kenan amma ni da baka dauke Ni uwa ba  da yake an riga da an shanye ka shi ne zaka tirje idanuwanka tsage'tsage kana gaya man irin wadannan kalaman to wallahi sai ka gane kuren ko gobe ko Ni ko Kai.!"

Washe gari da sassafe 'yan'wan Alhaji Sulaiman  suka yo tattaki har gidan shi gabad'ayan su domin Sa'adatu ta gaya masu komai abin da ya faru dan dama sun san da zancen.

Anan ne fa aka zauna akayi ta rikici wanda yake shi ne domin anyita ta k'are rayukka da dama sun bace har takai da su kayi wani furucin da Ya yi matuk'ar tsoratar da  ran Alhaji Sulaiman

Inda suka ce "Idan dai har bai canza k'udirin shi ba na rashin k'ara auren,  to daga Wannan   ranar  mai kamar ta Yau ya debe lissafin kan shi daga cikin jerin yan'uwansu ba su ba shi dan haka kowa Ya kama hanyar gaban shi kuma tsakanin su dashi sai dai kallo idan har anyi rashin sa'a hanya ta hada su da shi,

Nan take hankalin sa  ya kai mak'ura wajen tashi, shi ma kan shi bai so ya yi musu dasu ba har ta kai su ga yin hakan, shi abin da yake gani idan har ya yi wannan abin da suke buk'ata  kamar bai ma Maryama adalci ba da irin zaman da su kayi tare da shekarun da suka kwashe dik bai bijiro mata da wannan ba kuma sai yanzu,  sannan sun gina rayuwarsu cikin aminci da kautatawar rayuwa yana cikin yin wannan tunanin yaga sun mik'e  tsaye domin wucewa daga wajen shi tunda  sun gama maganar da ta kawo su

Aiko cikin hanzari Ya dakatar da su nan take bai tsaya wata-wata  ba Ya ce  masu ya amince da k'udurin su na auren, sai dai  shi a halin yanzu bai da wata maccen da yake nema amma tinda Iyah  ta Samar mai  a shirye yake da auren ta domin biyayya a gare su."

Sosai suka ji dad'in wadannan kalaman da suka fito a bakin shi, sai dai basu son nuna mashi suka ce yaje dai ya k'ara tunani dan basu son sutirsasa shi yin abin da bai yi niyya ba tinda har sun gama maganar su komai yanzu ya wuce atsakanin su yayi dik abin da ran shi ya ke so.

Cikin rawar murya ya ce masu "wallahi harga Allah na amince da hakan, Iyah wallahi da na rasa ku a rayuwa ta gwanda na rasa komai da na mallaka ahalin yanzu dan Allah kuyi man aikin gafara ku yafe man da abin da Ya faru  yanzu, Nasan  ban kyauta ba amma yanzu A shirye nake na dauki ko wanne irin hukunci ne da ya fito daga gareku."
Sosai suma abin Ya basu tausayi irin yanda yake magana suma sun san har abada ba zasu iya rabuwa dashi ba, amma sunyi mashi hakan ne don  ya canza k'udurin da ya dauka na tauye kan shi da ya yi.

Nan take suka zauna suka tsara yanda al'amarin zaya kasance da kuma diyar mak'otan su Sa'adatu wadda ta ce  ta nema mai Ita, sosai kowa ya yaba da hankalin wannan yarinyar da kuma tarbiyar da ta samu a gurin iyayenta  har sun suka tsaida ranakun daurin auren domin tun kafin Sa'adatu ta gaya mai ta riga ta sanar da iyayen yarinyar sai dai ta  basu sharad'i akan idan kuma har Allah yasa yana da wadda yake son sake Auren yanzu to dan Allah suyi hakuri a manta da  wannan zancen.

Bangaren Maryama sosai Ita ma tayi  farin cikin jin hakan  a yanda fuskarta ta nuna mai amma a cikin zuciyarta kamar ta fashe da wani azababen kukan da yake cinta  acikin zuciyarta akan bak'in cikin wannan
labarin  da ya zo mata da shi.
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Donde viven las historias. Descúbrelo ahora