009

185 18 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             _{Maimaici}_
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

*➡️009*

daf'da zata shiga cikin gidan Uncle Uzaifa ta  hango wata yarinya wadda shekarun ta ba zasu haura ma 16 ba, ta fito daga cikin gidan Uncle Almustapha rik'e da wani abu a hannunta Sai dai kuma bata gane ko menene ba sabida yarinyar ta saka abin a cikin Hijab d'inta ta lullube.
Wanda hakan ya sa Hajiya Kaka na ganin hakan ta  dinga tunanin ko Gumi ne (Shimkafa d'anya) aka saka ma wannan  yarinyar a cikin leda Mudu (kwano) biyu ta kai ma tsofaffi
        A fiki kuwa ta ce "kaiiii wallahi Kaji ne ma da Namomi a ciki, kuma na rantse da Allah bata isa ta fita da su a gidannan ba, Ko da ta duba inda yarinyar take tsaye dazu bata ganta anan ba,
Cikin sauri-sauri mai hade da  gudu-gudu take tafiya bata ji bata gani dand'e ta samu damar cinma  yarinyar ta anshe Kajin da take tunanin su ne daddank'e a cikin Hijabin yarinyar,  sai da wannan yarinyar ta yi kusan kai ga bakin get na fita daga cikin gidan sannan Hajiya ta samu damar hango ta tana k'ok'arin ficewa daga cikin gidan gabadai.
        Ai ko cikin mugum d'aga murya ta wangale baki  kamar wata mai k'ok'arin kiran Sallah  ta dinga kwalawa wannan yarinyar kira kamar Allah ya aiko ta "ke....ke...ke..ko bakya jina ne shegiya 'yar'iska bak'ar b'arauniya, to wallahi dik ki kayi kuskuren fita da Kajinnan a cikin gidannan wallahi ban yafe su ba dakariyar makwadaiciya kawai 'yar kwaraka sarkin rashin dangana.
                Cike da mugun b'acin rai da rashin mutumcin da ke tattare da wannan  yarinyar tayo ribas ta dawo baya tana tafiya tana dallawa Hajiya Kaka wani wawan kallo mai cike da rainin hankali, sai da ta'iso daf da ita sannan ta ce "Ina fatan dai lafiya Tsohuwa dan naga tun d'azu kike ta kwala man kiran kamar Wadda tayo satar Gold."  Sake da baki dalalala kamar wani abin arziki Hajiya Kaka ta ce " lalalaaaaa to wallahi sai kin san  Ni  Hajiya Laure kike gayawa bakaken maganganu." cikin wani  mugun bala'i Hajiya Kaka ta yi nasarar finciko wannan yarinyar da k'arfi sai da  abin da ke cikin hijab d'inta  ya fad'o k'asa qwaqwall, a maimakon Hajiya taga kaji da namomi sun fad'o k'asa suna yawo,  sai taga akasin hakan domin Arakke ce ta gani irin zangeniyar nan mai kauri ta fad'o k'asa tana mulmula.
        Daga nan ta shiga yin inda-inda tana cewa "Yau ni naga bak'ar b'arauniya Arakken ma  sai anyo satar ta sabida daman  gadon satar aka yo.?"  Cikin daga murya mai cike da mugun haushin abin da Hajiya Kaka tayi mata ta ce " ke dan Allah  ja can bak'ar masifaffiyar Tsohuwa mai k'idan-dangin hauka, 'yar-tasha kawai, wallahi kinci sa'a badan ana can ana jira na a gida ba da na rantse da Allah sai na dagargaje Tsohuwar banza anan wajen  wallahi ki godewa Allah sabida Ni yanzu ba na da lokacin da zan tsaya batawa a wajen ki da har zan tsaya sa in sa da ke domin ko a waje ba'a wannan sakarcin da Ni sai dai a bawa hamota iska amma mu zuba ni da ke wata rana zamu hade, mtsww mahaukacciya kawai, wlhy sai na gyara maki zama."
              Sai da ta gama balbalin bala'in ta Sannan ta duk'a k'asa ta dauki Raken ta sannan  ta fice daganan.

Ita ma Hajiya Kaka Tsaye kawai take  ta kasa cewa ko uffan tare da mamakin wannan tantiriyar yarinyar, dan tun da take ba'a tab'a yi mata irin wannan cinmutuncin haka ba,  murmushi gefen baki kawai tayi sannan ta ce " zaki san kinyi da ni sannan tad'an sake wani d'an guntun kwalci "qallllll" ta fice daganan taje ta dauki kulolin da  daman sai da ta ajiye su gefe a k'asa sabida tsabar son yin jidali, da karfin Allah ta dauke su sannan ta nufi bangaren Uncle Uzaifa da su.

Da hanzari ta fad'a a cikin gidan, a maimakon tayi  sallama sai ta dinga fadin "Ni za'a maida Sakarya makwadaiciya Mayya dan an raina ni kuma sannan dan tsabar rashin mutumci d'an nawa ya sayo abu ya kawo a cikin gida dan a dafa kowa ya ci sai ya koshi  amma  dan rashin mutumci Ni a rasa wanda za'a saka man sai kwaya d'aya sannan miya ko cokali biyu bata yi ba kuma dand'e baqin ciki har yanzu an kasa canza man kulolin abin ci inyi magana ace man mafadaciya wallahi dik mai zagi na  na bar shi ga rabbus'samawati wal'ardi,
Kazatttt-uba, yanzu  dand'e tsabar rashin imani Zahra'u da yake daman ke tun can azal baki da mutumcin  Ina maki magana amma har Ni zaki share wato kam ke ko a jikinki dan baki san muhimmanci na ba ko, to wallahi yau ko Ni ko ke a cikin gidannan ko waye ubanki Yau a cikin k'asar nan sai kin bar gidannan, Shegiya mai mugun ci kamar Gara, bak'ar makira hatsabibiya jahila marar imani marar kunya kuma marar tausayi."  cikin sauri Aunty Zahra'u ta k'araso wajen ta  cikin girmamawa ta ce. " hajiya inawuni?." A tsawace ta ce "Da ban wuni ba zaki ganni tantiriya bakar miskila,  tun dazu in shigo cikin gida inyi ta magana dand'e tsabar iskanci ba wanda Ya fito balantana ma asan abin da ke tafe dani."

"Dan  Allah Hajiya kiyi hakuri wallahi maganin ciyon kai  nasha d'azu shi yasa ban san lokacin da bacci ya dauke Ni ba kuma ga yarannan dik sun tafi makaranta ba wanda ke nan." 
      "Ohooo dama nas an ai haka zaki ce  hmmm shegiya Zahra'u.! wai ke wanne irin Hali ne naki da bansani ba ai wallahi sai dai inba wani labari, ana can dai daki ana abin da aka saba koda yaushe, wato an samu banza dai ko? ai na sani ba sai kin bani amsa ba dan nasan ana dai  can kuryar d'aki ana cika babban Tumbi wato an cika k'atuwar roba da abinci an shige d'aki ana ci dan kar wani ya shigo shi ma ya saka  albarkar shi, dan wallahi tallahi nasan wannan k'aton tumbin naki Ko kad'an ba zai dauke flat guda ba sai dai goma, shi ya sa  dan kar ma a tsaya wani bata lokaci da flat, ake cika k'atuwar roba ana shigewa cikin d'akin a kulle dan kar ayi bako shi ma ya zauna yaci da yake daman anyi gadon rowa da mak'o."
            Zahra'u ta ce wallahi Hajiya  ba haka ba ne wallahi bacci nake yi kaina ne  ke man  ciyo tun da  safe wallahi sai yanzu da nasha magani."

"Hmm to dama abincin ki ne na kawo maki sai a had'a a kaiwa k'armusasshin tsofaffi 'yan yunwa wad'anda ba su gadi Komai ba sai bakin talaucin tsiya....."
Follow me on wattpad and vote— Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere

WAHALA DA GATA season1Where stories live. Discover now