*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*➡️017
Cikin d'aga murya aka soma yi mata magana kamar haka,
"Ke wai yaushe zakiyi hankali ne? yaushe ne zaki gyara halayen ki? yaushe ne dik wannan mugun halin naki zaki daina shi? wallahi tun wuri gwanda ki canza rayuwa tun kafin lokaci ya k'ure maki, amma ace kullum kana cikin masifa da anyi ance ke ko gajiya bakya yi kullum ke ake ji kafin aji kowa! To wallahi........ Da hanzari Alhaji Ibrahim ya samu ya dakatar da shi ta hanyar cewa,
"Haba Alhaji dan Allah kayi hak'uri kasan harkokin matan wlhy addu'a ce kawai magani kowa hak'uri yake yi da su, muje part dinka a sasanta wannan al'amari dan Allah kaga yara dik suna kallon abin da ke faruwa ai ba za'a biye masu ba dik abin da su kayi haquri ake yi da su hankalin mu da nasu ba d'ai ba dan Allah muje."_ Hajiya Kaka da ta gama muzanta a wajen kamar ta bud'e k'asa ta shige akan kunya sannan dik wanda ta kalla sai taga idanuwan sa na gare ta daga manyan har bisa ga yaran Wanda hakan ba k'aramin tsarguwa tayi ba tare da jin kan ta ya yi gudan k'ato a wajen,
Haka dai ta matse ta ce "Assalamu Alaikum ya ku munafukai ai sai a kama jiki kowa ya koma inda ya fito tunda anji abin da ake son ji daman."
ba wanda ya motsa a wajen dan kowanne abin da yake tunani daban a cikin zuciyar shiDa taga alamun ko a hakan ma ba wanda ya kula ta sai taji ta k'ara tserguwa, nan take ta shiga tunanin neman mafita wanda hakan ya sa zuciyar ta ta fara raya mata cewa, K'ila abin da su kaga Alhaji ya yi mata ne a gaban su ne yasa yanzu har sun fara samun damar raina ta, ta ce to amma bari nasan maganin su.
Kai tsaye cikin d'aga murya ta ce "Wai da babbar kazat-uba ko anfi k'arfin abar mini dakina ne tunda bada shi kuka taho ba?."
Cikin mugun firgici hankalin kowa ya dawo kan shi sannan suka dinga bin layi-layi suna fita daga cikin dakin one by one kowacce ta nemi hanyar tafiya gidan ta._Ita kuma fatima dama a shirye take Uncle Mukhtar kawai take jira,
Nan take shi ma ya d'auki makullin motar shi ya ce ta tashi su tafi, aiko cikin tsananin farin ciki ta mik'e tsaye ta dauke jakar ta ta tufafi tabi bayan shi ta ce masu ta tafi sai dai ba wanda yayi mata ko kallon rahma a cikin su in banda tsarin da suka raka ta da shi marwan kadai Ya ce Allah ya kiyaye hanya Fatima ko shi ko sai da Nusaiba tadan shureshi a k'afa sannan taja tsaki.A B'angaren su Baba kuwa Alhaji Ibrahim bayan ya zaunar da shi waje guda sannan ya shiga kwantar mashi da hankali da maganganu masu shiga rai sannan shi ma ya tashi ya yi tafiyar shi na shi b'angaren amma shi ma tunanin wannan halin na Hajiya Kaka yana bala'in daure mashi kai sosai bisaga inda aka fito dori, kwanciyar hankai ba irin wadda basa yi amma tin lokacin da ta ji Alhaji Kabiru zai k'ara aure tun daga wannan lokacin ba su sake zama cikin kwanciyar hankali ba.... haka dai yake tafiya tare da tunanin wannan sauyin na Hajiya Kaka har ya ida isa a kofar gidan shi ya shige abin sa amma zuciyar shi a dagule
_Sai da Uncle Mukhtar ya fara wucewa da ita supermarket Ya yi mata siyayya sannan ya wuce da ita gida.
Suna kowowa a bakin get yafito waje, kasancewar gidan ba maigadi a ciki amma gidan da kagan shi sai kasan bak'aramin mutum ya gina shi ba, kama daga bakin get harzuwa cikin harabar gidan fulawowine masu bala'in kyau da kuma daukar ido_Yana fitowa ya fara bud'e get kafin ya ce me?, Fatima tuni har ta fito daga cikin motar ta wazge a guje tayi cikin gidan su tana maijin dadi da tsantsar farin cikin ganin ta a cikin gidan su wanda take jin shi tamkar aljannar duniya a gareta
Uncle Mukhtar da yariga ya yi mutuwar tsaye yanda yaga ko ida bude get baiyi ba Fatima ta kutsa a ciki da guda ta wuce tana mai kyakkewa d'auke da wani tsantsar farin ciki kamar wadda ta fito daga cikin kurkuku, wanda hakan ba k'aramin farin ciki ya saka shi ba domin yana bala'in son ganin farin cikin ta domin irin wahala da wuyar da take sha a gurin su Hajiya Kaka ba k'aramin tausayin ta yake yi ba._Koda ta isa a cikin gida direct palour mummy ta nufa, tana shiga ciki ta cinma su Zinatu da Suhaila, tana sallama kamar daga sama su kayi kuzut suka mik'e tsaye cikin tsantsar farin ciki suka wazgo aguje suka rungume juna su nata ihun murna wanda hakan ya jawo hankalin mummy dake dakin daddy cikin hanzari tayo b'angaren ta domin ganin abin da ke faruwa
_Uncle Mukhtar na shigowa da motar shi ya nufi parkin space ya yi percking sannan ya kulle get din, direct ya nufe b'angaren Daddy dan dama kafin Ya iso sai da ya kira shi ya ji ko yana gidan yau yace mashi eh ya taso tun dazu daga wajen aiki.
Mummy na shigawo cikin dakin ta tsinkayo Fatima acan tare da su Zinatu, aiko bata san lokacin da wani daddadan farin ciki ya lullube ta ba, sai dai kuma ta wani bangaren tayi bala'in tausaya ma halin da taga Fatima a ciki dik ta rame ga tambuna a saman fuskarta kamar na gezozi ga kuma raunin da taji a k'afar ta dik ya lalata mata k'afa a wajen gefen farcen ta babba, bata san lokacin da wasu zazzafan hawaye suka zubo mata ba a saman kuncen ta, cikin hanzari ta goge su dan kar yaran su lura da hakan,
_Abin dai sai hamdala domin su sun riga da sun yi nisa a cikin murna da farin cikin ganin junan su basu ma san da zuwan mummy a wajen ba..........
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere
ESTÁS LEYENDO
WAHALA DA GATA season1
FantasíaSeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...