*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE**_Start on 28/5/2020_*
*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_**_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ 18
Fuskarta d'auke da annuri ta ida k'arasawa wajen da su ke, Fatima na ganin ta tayi wajen ta cikin farin ciki tare da durk'usawa har k'asa ta gaida ta cikin tsantsar farin ciki ta ce "mummy anwuni lafiya" cikin sakin fuska ta amsa mata da "lafiya k'alau 'Yar Mama ((kasancewar ta 'yar fari yasa take kiran ta da haka )) sannan ta kara da cewa "yaushe aka zo ne" ta ce "yanzunnan Uncle Mukhtar ya kawo ni yana ma bakin get."
_Mummy ta ce "Allah sarki meyasa bai wuce ciki ba?."
ta ce "yana bude get ne zaiyi parking"
Mummy ta ce "ok baban ku na ciki, kije ki gaida shi.!"
nan fa taji cikin ta ya fara mird'awa domin kamar yanda take jin tsoron Hajiya Kaka haka shi ma take jin tsoron sa.Mummy sosai ta lura da hakan amma sai ta fauze domin ita ma ba yanda ta iya ne, sannan ta ce "lafiya naga dik yanayin ki ya canza ko bakya jin dadin jikinki ne?."
ta ce "A'a Mummy wlhy lafiya k'alau!"
ta ce "To ba damuwa amma maza ki je ki gaida shi yana dakin shi."_Cikin mutuwar jiki ta tashi ta dinga tafiya guda-guda kamar wadda bata da lakka, Mummy ta lura da hakan kuma ta san abin da yasa, haka dai ta share da zancen tare da maida duban ta gasu Suhaila, da su tun lokacin da Fatima ta tashi suka ci gaba da kallon film d'in da suke yi, kai tsaye ta ce ma su "wai kunyi sallar la'asar kuwa.?"
gabadayan su suka amsa da "Eh mummy munyi tun dazu da kika tayar da mu muka bi jam'i!"
tace "ok"Fatima tun kafin ta kai ga shiga cikin dakin Daddy taji gaban ta na duka ukku-ukku daganan ta dinga kalima tare da ambaton sunayen Allah, sai gata a bakin kofar shiga, daganan ta shiga fargabar shiga cikin dakin domin wani irin mugun duka da take jin gabanta na yi kamar ya tsage nan take ta dinga fadin *ᎪᏞᏞᎪᎻᏌᎷᎷᎪ ᏆNNᎪ NᎪJ'ᎪᏞᏌKᎪ FᏆ'NᏌᎻᏌᎡᏆᎻᏆᎷ ᏔᎪ NᎪ'ᏌᏃᏌ ᏴᏆKᎪ ᎷᏆN ᏚᎻᏌᎡᏌᎡᏆᎻᏆᎷ* tare da yin bisimillah sannan ta fada a cikin dakin da sallama
nan ta hango shi shi da Uncle Mukhtar zaune a cikin babban palour dake cikin dakin suna fira abin su gwanin ban sha'awa ba su ma san da zuwanta ba sai da takara karasawa a kusa da su sanna ta sake yi masu sallama tare da rusunawa har k'asa ta gaida su kanta a noce a k'asa, amma a maimakon jin amsar Daddy ciki ciki kamar yanda ya Saba wanda idan ma baka halkanta da kyau ba ba za ma kasan ya bud'e bakin ya yi maganar ba amma sai taga ciki sakin fuska ya amsa mata da lafiya kalau Fatima, anzo lafiya ta ce "lafiya lau Dady ya muka same ku?." Ya ce " lafiya kalau!" ciki-ciki tace "Alhamdu lillahi!" cikin rawar jiki da makarkata ta mike tsaye ta fice daga dakin cikin sauri kamar wadda ake kora,
Uncle Mukhtar da imani yariga da ya cika mashi zuciya har bai san lokacin da wani guntun murmushi ya kubce domin tunda yake da shi bai taba ganin Daddy yakalle
ta ko da fuskar rahma ba balantana harya iya Amsa gaisuwar ta kamar haka,
su dik tunanin su tsana ce da rashin so ke kawo hakan shi ya sa bai damu da ita ba, hmm basu san dik cikin diyan shi yafi ji da ita ba, wadda yake ji tankar tsokar jikin shi dik abin da su Hajiya Kaka ke yi mata basu san ko kad'an baya Jin dadins hi ba, kawai dai bai iya nunawa ne.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season1
FantasySeason 1. "Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan uba...