037

114 11 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

EPISODE>>>37_*

"Hunhunhunhunnnn"

dariyar cikin mak'oshi kenan Ita ce abin da ya fara fitowa daga cikin bakin Boka Mintsinkyu kafin ya ce da su wani abu.

_Ba tare da b'ata lokaci ba ya ce masu "SHARADI NA FARKO shine zan baku bak'in Zakara wanda ya kasance wajibi ne a gareku da kuje ku binne shi a cikin mak'abartar FANTIMAU Sannan zaku hadu da abubuwa kala kala akan hanyar ku ta tafiya mak'abartar, kar ku kuskura kuji tsoron komai dake cikin jejin domin Idan kuka nuna harkar jin tsoro a nan to dik abin da ya faru da ku kuka janyowa kan ku.!"

_Nan take gaban su ya dinga duka uku-uku sai famar hadiyan yawu suke ga wani gumin da keta famar gangaro masu a fuska tare da saka hannayen su biyu suna sharb'ewa akan wani dan'ballajja'un tsoron da yake tsotstsokalo su, gashi kuma babu Alama ko ''yar kadan da zata iya nuna masu cewa akwai alamar sassauci a tattare da wannan bak'ar tatsatstsiyar fuskar Boka Mintsinkyu. domin sun halkanta da ko kadan babu alamun Imani atattare da shi.

_Kafin su kaiga furta wata kalmar tuni Ammie ta tsinci wani gawurtaccen kuma hamshak'in Bak'in Zakara zaune daram a saman hannayen ta, Innadillah, wata irin kururuwace tayi mai cike da ban firgici tsagwaron sa, haka Ita ma Balkisu ba'abar ta a baya ba wajen bada tata gudamuwa ta nuna alamun tsoro da firgici a tattare da fuskar ta.

Cikin mugun k'arfin hali Ammie ta cira hannayenta sama kamar wadda zata kida kalangu ta yarfar da shi daga saman hannayen ta sai dai amaimakon taga ya fad'i k'asa amma sai jin sa tayi tsaye tsangalgal a saman Kwanyar kanta, bata ankara ba taJi ya watsa mata wata Irin arniyar dariya mai cike da ban al'ajabi sannan ya ce, "Aiko kinyi a banza wallahi.!"
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang