032

117 8 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
             [Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
         *_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

EPISODE>>>32

_Wata irin bak'ar dariya ce da su kaji anabyi mai kama da kukan Rago wanda hakan ne Ya yi sanadiyar falkawar su da hanzari cikin mugun firgici.

Su duba nan su duba can domin k'ara tantancen gurin da suka tsintsi kan su cikin firgici dan basu tab'a ganin irin wannan wajen da suka tsintse kansu ba ko a cikin Mafalki.
Wanda Hakan ya yi sanadiyar mummunan tashi da hankalin su ya yi gashi har yanzu basu iya cewa ko uffan, Sai dai su gani kuma su ji amma ba zasu iya tsinanawa kansu da komai ba.
Wata k'atuwar murya ce su kaji daga sama tanai masu magana a cikin muryar ban tsoro kamar haka

"Kunce zaku biya Ko? ."
lokaci guda kuma su kaji an sake b'arkewa da wata irin kafurtacciyar dariya mai kama da ta aljannu. Sannan daga bisani kuma suka ji so 20second ba ayi ba an tsayar da dariyar gabadai.

Rabe-raben ido, shi kad'ai ne aikin su, sai dai hakan baitsinane su da komai ba illah duhun da ke cikin wajen.
Ba su ankara ba sai ganin su kayi wani Abu mai kamar hayaki yana saukowa daga sama yana dawowa k'asa

Cikin gaggawa su kayi hanzarin daga kawunan su sama domin ganin inda wannan abin ke tasowa
Sai dai kuma sun k'ara jama kan su masifa ne wadda har sai da suka sake goge idanuwan su da kyau domin tabbatar da abin da suka gani ba gizo ba ne, domin wani ruftunemen maciji ne irin gawurtaccennan mai siffar jikin kada amma fuskarshi ta banbanta da ta sauran macizan, domin fuskarshi sak tayi kama da fuskar Boka Mintsinkyu.
Wata gid'imammiyar dariya ce da su kaji wadda ta k'ara saka su kokwanton a inda dariyar take fitowa, domin irin dariyarnance tacan cikin Mak'ogoro.....HUNHUNHUNNNN!!!!!!! Mai cike da mugunta,
Nan take cikin wata barkatacciyar murya
mai kama da ta mutum biyu su kaji ya kira wani Mutum Mai suna TSINYU.

_Wannan sunan ne da ya yi nasarar shiga cikin dodon kunnen Ammie wanda ba k'aramin tsoratar da'ita yayi ba domin wannan sunan ko a cikin Mafalki taji shi zata iya yin kuzut ta sharb'e zancen da sunan tasan mai shi, tana cikin yin wannan banzan tunanin ne kamar wadda aka ce ma ta tayar da kanta sama ta tsinkanyo wani Mutum rik'e da wata k'azamar kwarya a hannayen shi Mai bala'in shegen warin ruwan rub'ab'b'en k'urji kuma da dikkan alamu sun nuna cewa wajen su ne yake tunkarowa da ita
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

WAHALA DA GATA season1Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz