019

136 12 0
                                    

*♥️♦️WAHALA DA GATA♥️♦️*
[Maimaici]
*NOVEL SERIES, SEASON ONE*

*_Start on 28/5/2020_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ✔️*
*_{BE SMART}_*

*_[EMAIL. www.smartfeenert@yahoo.com]_*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*—•«•»•«»•-•«»•«•»•—*

ᎬᏢᏆᏚᎾᎠᎬ 19

Cikin mugun firgici Nusaiba ta falka, sabida shurin da Hajiya Kaka tayi mata  har sai da ya yi sanadiyyar barin ta a shimfidarta ta fad'a wani gefe tare da sakin wata razananniyar k'ara wadda sai da tayi sanadiyyar falkawar Aunty Rukayya daga daddad'an  baccin da take

Cike da wata mugunyar gidemewa Aunty Rukayya tayi gefen da Nusaiba take domin ganin  abin da ke faruwa tare da tambayar ta  "lafiya" cikin wani matsanancin kuka Nusaiba ke gaya ma Aunty Rukayya abin da Hajiya Kaka tayi mata, nan da nan ran Aunty Rukayya ya yi matuk'ar baci ta ce "Haba Hajiya! yanzu ita da ke bacci bata ma san a inda kanta yake ba amma kiyi mata irin wannan danyen hukunci ai ya kamata dik abin da tayi ki bari tukunna har lokacin da ta farka sannan dik abin da zakiyi ma ta sai kiyi ko!  wannan zwaluncin da me Ya yi kama.!

    Hajiya Kaka da haushi dik Ya riga da ya gama turmuke ta domin wadannan maganganun na Aunty Rukayya ba k'aramin bala'in suke soso mata ba.

Ta ce "Lallai Rukayya wuyan ki ya yi kauri, yanzu ni kike gayawa dik wadannan maganganun akan 'yarki dan baki da Imani............ "Assalamu'alaikum!"
         Sallamar da ta jiyo ne a bakin kofa  ya katse mata hanzari wajen ci gaba da yin fad'an, kai tsaye ta ce, "Lafiya" 
      Yaron ya ce "Wani ne ke neman Al-Amin abakin garka..." Mtswww iskancin banza to bashinan halan bakasan dakinsu ba ne dan'iskan banza?.
       yaron dai bai k'ara cewa da ita  ko uffan ba ya wuce abin shi.

_Nan take kuma dubanta ya dawo kan Aunty Rukayya cikin lalama take yi mata magana kamar ta kwarai, ta ce Rukayya "Yaushe kika canza Rayuwar ki haka?  ba haka nasan ki ba, har kifiifita diyar ki, diyar ma ta fari akan mahaifiyar ki kuma a gaba gare ta kike gayaman wadannan maganganun haka hmm!, aini wlhy a tunani na ko gilmata nayi a k'asa na yanke ba zaki taba bude bakinki ba kice man dan me nayi amma sai gashi har da tukwicin bak'ak'en maganganu nake samu a wajen ki kuma dik akan ta, Amma Albasa ba tayi halin ruwa ba dan wallahi ni sanda Allah yayi Ni ban tab'a nunin  iyaye na da ko dan'yatsa ba amma ke gashi har da azzaluma kika kirani dashi akan 'yarki, hmmm duniya kenan duniya mai halin dan mangwaro.

_Jikin Rukayya ya yi bala'in mutuwa matuk'a wanda har bata san lokacin da ta ce "Kiyi hakuri Hajiya,  insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba."
     Hajiya Kaka ta ce "Hmm ba komai Allah dai Ya saukaka!"
        Aunty Rukayya ta ce "Ameen" sannan tace ma su Nusaiba suje su kurkure bakin su suzo ga shinkafar jiyanan suci suk'arya da ita kafin ak'are abincin rana, suka amsa da toh gabad'ayansu suka fice daga dakin,
        Sannan Aunty Rukayya ta bud'e baki ta ce ma "Wai yanzu Hajiya dik wa zaiyi wadannan ayukkan da Fatima tazo tabari ko 'yar aiki za'a dauko ne kafin  ta dawo.!"
         Hajiya Kaka ta d'an sake wani d'anguntun murmushi kafin ta bata amsa da cewa "Waye kuwa zai yi in banda ke! Kuma kinga kin samu k'arin mataimaka tunda ga d'iyan ki nan ku dinga yi tare kafin ta dawo daga gida.

  Cikin mugun firgici Aunty Rukayya ta ce "Ni shin"
         Cikin d'aure fuska Hajiya ta ce  "Eh ke mana ko ba zaki iya ba ne?."
     Ai kuwa nan Aunty Rukayya ta mike tsaye ta ce "Tabd'i! wallahi kuwa ashe akwai gumu dan tun farko da nasan wannan shawarar kika yanke wallahi da ba a bar Fatima ta tafi ba dan Wallahi ni ba abin da zan yi a cikin wannan aikin, da me zanji ne? Rainon d'ana koda yin aikin da yafi k'arfi na wanda ko kayi ba za'a ce maka an gode ba.

         Hajiya kaka ta ce " iyyeee lallai Rukayya,
         cikin bak'in bala'i ta ce ke har kin isa in ce abu ki ce a'a to wallahi tin wuri ki nema ma kanki mafita domin aiki kan babu fashi wallahi sai kinyi."
     Aunty Rukayya ta ce " wallahi ba wanda ya isa ya saka ni yin abin da banyi niya ba." Ta k'arkare maganar ne tare da d'age dankwalin ta a saman goshin ta ta maida shi ture kaga tsiya.

Hajiya Kaka ta ce "Babbar kazat-uba yanzu Rukayya ni kike yi wa hakan."
        Kai tsaye ta ce "Rasss wallahi kuwa, akan me kuwa ko wanne gayyar na ayya idan ya kwaso tarkacen shi na tsiya  sai ya jibge shi a kaina to wallahi bazan iya ba na gaji da wannan  danyen wulak'anci da ake muna man."
       Hajiya kaka kamar ta fashe da wani fitinannen kuka akan bak'in ciki amma sai ta dake shi a cikin zuciyar ta sannan ta ce  "Lallai kuwa Rukayya wuyan ki ya isa yanka, to wlhy ko aiki babu fashi."
          Aunty Rukayya ta ce "wallahi ba wanda ya isa ni kuma."
         Hajiya Kaka ta ce "lalalaaa wallahi ina ganin kin manta da ko wacece Hajiya Laure  amma bara yanzu na tuna maki.

Nan da nan Hajiya Kaka ta d'ebe d'ankwalin ta ta sha d'amara, Aunty Rukayya na ganin hakan tayi hanzarin shigewa cikin k'uryar daki ta kulle kanta da sakata dan ta san halin Hajiya kaka kamar yunwar cikin ta saraii zata iya dukan ta,
          Nan Hajiya Kaka ta ce "Ashe wallahi k'aryar k'idandangin iskanci kike yi ai da kin tsaya tunda kin ce ke tantiriyar  'yar'iska ce, da kin tsaya kinga k'aryar iskanci da kinga abin da zai faru dake wallahi.

Kai tsaye Aunty Rukayya ta ce "wallahi ba abin da zai faru da ni sai alkhairi." Tayi maganar ne tare da tunanin ta tsira ne sabida ta kulle d'akin
          Nan fa  Hajiya Kaka ta fad'i Aunty Rukayya  ta fad'i  dik abin da ta ce sai ta maida mata da goman shi  nan take Hajiya kaka tayi wani irin kukan kura  ta hira sama kamar wata tsuntsuwa ta dauke ganbun d'akin da k'arfin Allah sai da ya bud'e gabadai,
            nan fa suka shiga fafatawa ita da gudan jinin ta Aunty Rukayy.

Alhaji Kabiru da su Hajiya Saudat dik suna jin abin da ke faruwa amma ba wanda ya shiga dakin domin kashe wutar, kowa ya saka masu ido domin suyi abin da suka ga dama ita da diyar ta wadda akan ta tana iya b'atawa da kowa wanda har Hajiya Saudat ta fito ita da yaran ta zasu je wajen ziyara gidan su iya da su Uncle Musaddiq
           Har a wannan Lokacin su Oga Hajiya Fafatawa ne suke, shi ma Alhaji Kabiru ya fito ya tafi masallaci domin ya huta da jin wannan hayaniyar ta su shi ma Marwan  binshi ya yi suka tafi tare  ita Kuma Nusaiba da bata da wajen zuwa ta zauna waje tana sauraren ikon Allah.
         Fafatawar ba ta wasa ba ce tsakanin ta da  'yar ta  ta a cikin dakin, wanda Idan Hajiya Kaka taje wajen dukan Aunty Rukayya sai ta kauce ta buge gina Ko kuma gado Ko kuma wani abu wanda ke cikin dakin,
          Daganan Hajiya Kaka tayi tintub'e  da wata kwalba wadda dama an ajeye ta ne sabida kunna maganin sauro, Hajiya  Kaka ta fad'i tuwww a k'asa reram  kamar wani k'atoton  dutsi.

Ai kuwa daganan Aunty Rukayya ta samu damar yin tsalle sama ta k'etare Hajiya Kaka ta fice a guje daga cikin  dakin, Nusaiba na ganin haka ita ma tabi bayanta aguje suka wazge tare da barin cikin gidan gabadai,
   Hajiya bata ma tsaya bin ta jikin taba, cikin hanzari da zafin nama tamik'e tsaye da niyar bin bayan Aunty Rukayya ai kuwa nan kaji abinnan gufffff da k'arfin Allah ta kaura k'atoton goshin ta a saman bangon dakin, ba tare da b'ata lokaci ba wani wargajejin Lolo ya bayyana k'arara a saman k'aton Goshin ta, daga nan sai ga fitowar jini a sama  malalala yana fita waje.
      Sai dai a maimakon ko yanzu ta bawa kanta hutu amma inaaa abin ya cutura hanik'an  domin ita ko a jikin ta, agurguje ta sake saita hanyar ta ta fita waje cikin matsanancin gudu kamar Taya ta fito daga cikin dakin a guje tana kawowa daf da fita waje su kayi kicib'us kamar suyi kaura ita da matar..........
Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shere

WAHALA DA GATA season1Where stories live. Discover now