Chapter 50

87 11 3
                                        


Yan biki sun hallara kowa yazo yan California na zuwa sukace babu yadda za’ayi ayi bikin the famous Abdulrahim amma ace ba zasuyi ball ba dan haka dole Bello ya shigar da ball cikin events din bikin shi zasu farayi ranar laraba tsakanin abokansa na NFL da abokansa na gida, kowa idan aka gaya masa sai yayi dariya saboda kowa ya riga yasan wadanda zasuci ta yayama ordinary yan ball na bayan layi zasuyi da yan ball na duniya NFL gaba daya? Amma dai kodan ayi dariya ma dole suyi wannan hadin dan kowa yasan za’a bawa abokan gida kashine ba wani abuba, a ranar kuma su Dr Abdullahi suka sauka a Nigeria shi da matarsa safiya da kuma Zainab sai yaransu guda uku ‘yar jaririyar da take goyo mai sunan Khadija, ai kuwa Khadija tayi murna sosai dama tunda akayi haihuwar take ta kulafucin zuwa ta gano yarinyar Abdulrahman ya hanata saboda jikinta ta kuma yi murna sosai saboda zuwan Zainab at least ta samu kawar da zasuyi hidimar tare.

Ranar laraba karfe 4:30pm aka saka wasan kuma a katin gayyatar ma an sanar da kowa babu African time wasane da turawa, a cikin wani babban stadium aka yi wasan abokan gida sun saka green da white jc irin na yan wasan Nigeria su kuma yan NFL sun saka red and white jc Abdulrahim na cikin yan gida, an kawata wajen sosai ga wajen zaman yan kallo nan ga wajen zaman amare nan su biyu kowa da kujerarta ga kuma ma’aikata nan suna ta yawo suna rabon dan abin tabawa da lemuka kamar dai a turai, Aisha ta shigo ta tawagarta ita da kawayenta da kuma yan uwanta wadanda suma suke son zuwa kallo dan kowa aka gaya masa wai da turawa za’ayi match din sai kaji yace shima zashi nan fa kallo ya koma kansu yan matan nata ba dai kyauba ga kuma indiyawa suma daga danginta na can duk uncle Ahmad ya kwasosu, Aisha tayi kwalliya iya kwalliya itama nata kayan nata doguwar rigace ta saka Mai Dan banzan kyau Sea green anyi mata kwalliya da white stones kamar dai jc din da angonta zai saka sai walwali takeyi, yan uwanta suka nufi mazauninsu itama da kawayenta aka gabatar musu da nasu wajen zaman sai kuma ga Amira nan ita ma da nata kawayen Khadijace a gaba ita da Zainab dan tunda aka fara shirin bikin ma suka tattara suka koma gidan dady cikin kawayen Amira, itama dai Amiran irin shigar jikin Aisha ce a jikinta sai dai tata green din tayi army maimakon sea da Aisha ta saka, Amma da yake shades din duk masu duhune sai sukayi kamar iri daya, itama tayi kyau sosai kamar ka dauketa ka fita da gudu.

Bayan kowa ya gama zama Abdulraman ya shigo wajen shima yaci kwalliya sai dai yana shigowa friends dinsu na gida sukazo suka jashi sukace wallahi sai yayi ball din shima, nan fa akayi ta dariya yana cewa bazaiyiba su kuma sukace sai yayi wasu ma cikinsu sukaje suka zagaye Amira sukace bazai gantaba sai yaje ya sako jc ya kuma yadda zaiyi ball, a dole Abdulrahman ya sake shiga suka fito tare shi da Abdulrahim.

Idan ka gansu banda gashin dake kan Abdulrahim sai kuma dan banbanci na building din jikinsu zakayi tsammanin mutum dayane, kullum suna kara girma kamarsu na kuma fitowa kyansu na kuma fitowa koda yake jin dadin da suke sake shigane kullum rayuwa na kuma budawa kullum idan suka duba sai suga tafi jiya kyau wannan dalilin yasa babu abinda zasucewa ubangijin talikai sai godiya domin babu abinda bai basuba rayuwarsu miracle ce babu wanda zaiyi tsammanin wadannan almajiran da suke yawo babu takalmi a bakin danja suna bara zasu zama haka.
Suna fitowa wani cikin yan NFL james ya fito da wasu customized bandana guda biyu daga cikin kayansa green ce dafarin rubutu a jiki daya an rubuta shahim daya ameeman yaje ya mikawa Ameera daya ya mikawa Aisha daya yace kowanne ango yazo amaryarsa ta daura masa kamar alamaceta neman sa’a ko Karin kwarin gwuiwa daga amaren, anan ma anci dariya kowa yazo ya tsugunna su kuma su Amira suka daura musu bandana din a goshi sannan sukayi cikin filin da gudu.

Gaba Daya Abdulrahman wani iri yakeji tunda ba sabawa yayiba kwata kwata baima san inda ya kamata ya tsayaba shidai ya shiga fili, ga kayan jikinsa shi bai Saba saka dangalallun kaya irin haka a cikin mutaneba, 4:40pm dai dai aka fara wasan ai kuwa kamar yadda akayi zato hakance ta faru tun a 20mins din farko yan NFL sukaci 10 yan gida nada kan jaki, yan kallo dariya kawai sukeyi su Amira kuwa kamar cikinsu zaiyi ciwo Abdulrahman sau biyu yana faduwa shi kadai ba wanda ya tabashi saboda tsabar rashin sabo.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Mga kuwentong kahuhumalingan mo. Tumuklas ngayon