Chapter 48

67 10 4
                                        

Satinsu Bello biyu a dubai sun gama siyan komai hatta da akwatunan da za'a saka kayan sun siya sun aikosu ta ruwa, wata rana kafin su kammala siyayyar Bello da hajiya na zaune suna kallo Khadija kuma tana balcony suna waya da Abdulrahman hajiya ta kalli Bello tana murmushi tace "nikam Abdulmalik ma koma gida kuwa?" ya juyo da hankalinsa kanta yace "me yasa hajiya? Akwai wani abu da ba'a siya bane?" tace "aa na fara tunanin na koma shagunan duk da mukaje na sake siyo komai daidai dan kar na koma gida a sake sakani dawowa" Bello ya dan yamutsa fuska yace "banajin zaki dawo tunda su biyune amaren kuma komai biyu muka siya" hajiya tace "ai alama na gani cewar amaren zasu zama uku Amira Aisha da Khadija" ya tsaya kawai yana kallonta can yace "Khadija kuma? Wacce khadijan?" hajiya tace "karka rainamin hankali an gaya maka bansan abinda kukeyibane? Kai da wannan khadijan nake fada" sai kuma yayi saurin dauke kai yana dariya yana susar keya yace "kai hajiya ba haka bane fa" tace "to menene? Kanaso ka gayamin ba soyayya kukeba?" ya kalli kofar balcony din har yanzu waya take tana dariya yace "ni dai nake abuna amma ita bata tayani ni nake kidana nake kuma rawata" hajiya ta dan shafa gashin kansa tace "karka damu Abdulmalik dama ai babu abu mai kyau da yake zuwa da sauki zaka sameta kawai tana dan jan ajintane amma itama tana sonka Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi" Bello yayi ajiyar zuciya ya maida kansa kan tv din tare da cewa "ameen ya Allah".

Kamar yadda kamfanin da su abdulrahman suka bawa aikin gininsu sukayi musu alkawari wata guda cif suka gama aikin a lokacin biki saura sati hudu a satinne kuma su Bello suka dawo dan haka sai suka sake bawa wani kamfanin shi kuma kwangilar furnishing gidan gaba daya part din mazan da kuma dakunan Khadija a kowanne part (dan gidan kowa da part dinta) cikin sati guda aka kammala komai sai part din amaren su kawai aka bari ba'asa komaiba.

Ana sauran sati uku a fara biki su Abdulrahim sukaje gidan dady da yamma a ka'ida Abdulrahman zance yazo Khadija kuma akwai shirin da sukeyi da Amira abinda tazo zasuyi magana kenan su Bello kuwa yan rakiyane, a harabar gidan suka tarar da dady yana zaune kan carpet da dan tintin yana karatun jarida suna zuwa gaba daya suka zube a gabansa suka gaisheshi, dady ya tashi zaune sosai yana amsa musu cikin fara'a ya fara tsokanar Khadija "tame gari har ina cewa zamu hade bikinku gaba daya ku ukun kuma sai naji shiru?" ta saka fuskarta cikin cinyoyinta tana dariya duk suma suka saka mata dariya Abdulrahim yace "ayya dady ai wannan tame garin bata da me garin tukunna" Bello ya tsikara masa cinke a kafa da sauri ya matsa gefe yana dariya.

Ana cikin haka sai ga Amira ta fito da dogon hijabinta har kasa fuskarta kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa baki kirin, gaba daya suka tsura mata ido kowa gabansa sai faduwa yakeyi saboda yanayin fuskartata ta nuna ba lafiyaba, tana zuwa babu wanda ta kula ta samu waje ta zauna daidai jikin dady ta dora kanta akan kafadarsa murya a dashe kamar wadda taci kuka tace "dady?" ya dan kalleta da kulawa yace "naam princess me ya sameki?" ta danja hanci sannan tace "dady na fasa auren na fasa auren yaya Abdulrahman" babu wanda bai tsorata da abinda Amira tace ba da sauri ba tare da Abdulrahman ya kula da dady dake wajenba ya matso kusa da ita yana kokarin dago fuskarta yace "what? No Amira me kike cewa? Na nayi miki? Kina cikin hayyacinki kuwa?" amma sai taki dago kai ta kalleshi sai wani irin kuka data saka, a hankali dady ya saka hannu ya rungumota jikinsa sannan ya dagawa Abdulrahman hannu alamar yayi shiru ya kalli Amira yace "princess menene ya faru me yasa kikace kin fasa aurensa bayan gashi biki ya kusa?" ta kifa kanta a kafadar dady kuka kawai takeyi kamar ranta zai fita ta kasa cewa komai hankalin kowa a wajen a tashe yake Khadija ma sai kuka takeyi, mikewa kawai dady yayi da ita a jikinsa sannan ya kalli Abdulrahman wanda fuskarsa ta koma kamar wanda zai dora hannu aka ya zunduma ihu kallon fuskarsa kadai ya isa ya saka mai raguwar zuciya kuka yace "karka damu Abdulrahman koma menene yake faruwa zan bincika kuje gida ku cigaba da shirinku" Abdulrahman ya kuma kyabe fuska yace "amma dady..." dady ya daga masa hannu yace "nace kuje zan nemeku" bai jira komaiba yaja Amiran cikin gida ya barsu a wajen.

Daki dady yakai Amira ya kwantar da ita a kan gado shi kuma ya zauna a bakin gadon yana dan dukan bayanta a hanakali har ta daina kukan ta koma ajiyar zuciya daga nan kuma sai bacci duk da magriba ta gabato amma kawai sai yayi mata addu'a ya juya ya fita, dakin momy ya shiga itama tana kwance kan gado dan tunda aka fara maganar aurennan ta koma ko zaman falo bata fiyayiba idan kaje dakinma bata wata magana har dady na tunanin ita kanta da a yanzu za'a aunata ba za'a rasa ciwon zuciya ko hawan jini tare da itama saboda tsabar saka kai a wahala da tayi, ya tsaya a kanta ta dago kai ta kalleshi sai kuma ta yunkura ta mike zaune ya kare mata kallo fuskarnan kamar mutuwa yace "me kika gayawa Amira? Me kikayi mata?" momy ta kalleshi da mamakin karya a fuskarta amma da yake ya santa tamkar tafin hannunsa yana kallonta yasan expression din na karyane tace "ban gane me nayi mataba me tace nayi mata? Ni babu abinda nayi mata dan yanzu kasa ta riga ta gama rainani gaba daya" dady ya fahimci so take ta canja zancen dan haka ya doka mata tsawa har sai da ta firgita yace "kinga alamar wasa a idona? Zaki gayamin abinda kikayi mata ko kuwa? an gayamiki bansan abinda nakebane da Amira zatazo a wannan lokacin tace ta fasa auren Abdulrahman kuma nayi tsammanin yin kantane? Wallahi ko ki gayamin abinda kikayi mata ko kuma yanzunnan ranki zaiyi mummunan bacin da baki taba tsammaniba" momy ta kalleshi da tsoro karara a fuskarta dan bata taba ganinsa irin hakaba sai kuma ta fara tunanin abinda ya faru awa kusan biyu da suka wuce.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Stories to obsess over. Discover now