Chapter 47

50 10 1
                                        

Shirye shirye sun kankama sosai ta kowanne fanni, ginin su abdulrahman ya kankama duk ukun akeyi duk da cewa Bello ba yanzu zaiyi aurenba ko budurwa ma bashi da ita amma dai yace wallahi ba zasu taho su barshi acan gidanba shi kadai shima gudowa zaiyi, gidan su Aisha ma shiri sukeyi sosai dan antynta dake maiduguri ma kanwar cp tazo ta tafi da ita shima uncle Ahmad uncle dinta dake india har yazo gaba daya shi da iyalinsa yayi aure tuntuni da matarsa da yaransu biyu Fatima da Irfan.
Gidan dadyne kawai babu abinda akeyi dan da anty zulai ma tazo take cewa "yaya dama cewa nayi kaga bikinnan ba wani da yawa aka sakashiba ya kamata ace mun fara komai da wuri kar lokaci ya kure mana me da me kake ganin zamu fara yanzu" dady yace "zulaiha ai kune mata ku kukasan me ya kamata ayi sai dai kuyi magana da Mariya ko kuma su safiya (kannen momy) zaki tuntuba?" anty zulai ta kalli momy dake ta danna waya kamar ba da ita ake maganaba tace "anty Mariya bakice komaiba ko kun fara wasu shirye shiryene" momy bata dago kanta daga kan wayartaba tace "babu shirye shiryen da muka fara kuma ba zamu faraba dan babu wani aure da za'ayi tsakanin Amira da wannan almajirin" dady ya tsaya kawai yana kallonta can yace "Mariya menene matsalarkine da Abdulrahman? Me ya tabayi miki wanda yasa kika tsaneshi haka?" ta ajiye wayar ta gyara zamanta tana kallon dady sosai tace "ta yaya kake tsammanin zan dauki 'yata kwaya daya da Allah ya bani na bawa almajiri? Kuma almajirin ma nawa na gidana dana bashi sadakar abinci da gwanjon 'yayana?" dady yace "sai kuma ya zama menene aibun hakan? Dan yana almajiri har yanzu almajirinne? Dan kin bashi kwance har yanzu kwancen kike bashi? Dan yayi miki aikatau har yanzu aikatau din yake miki? Mariya ki dawo hayyacinki dama rannan Amiran ta gayamin wai tace miki ba zata iya rayuwa bashiba kikace wai Allah ya jikanta ai ba ita kadai kika haifaba ko? Saboda rashin hankali? Ku mata wani lokacin idan kukaki gaskiya sai tunaninku ya koma kamar na yara wallahi" anty zulai tace "to banda abinki anty Mariya da kike cewa kin bashi kwancen kayan yaranki kema dai kinsan yanzu sai dai ya bawa yaran naki kwance kuma what matters is abinda yake yanzu ko abinda zai iya zama nan gaba ba abinda ada ya taba zamaba beside almajirancin ai ba haramun bane" momy ta daga wa anty zulai hannu tace "kinga zulai karki nemi ki rainawa kanki hankali bana son gulma da kinibibi ke idan 'yar kice zaki bashine? Ko kuwa dan ke baki haifi 'ya macen kinsan wahalartaba?" anty zulai tace "Amira 'yatace ko da banyi nakudartaba, sannan kema ba rawa kikayi Allah ya baki macenba ni kuma ba laifi nayi daya bani maza zallaba kuma wallahi da ace ina da macen kuma yazo yace yanaso babu abinda zai hanani na bashi as long as halinsa da asalinsa masu kyaune" dady ya daga musu hannu yace "kunga dan Allah banason rashin hankali mekenan? Amira dai yarinyatace kuma na bayar da ita banajin kuma kin isa kisani na maida musu kudinsu indai har ba wani genuine dalili kika kawo a kan yaron wanda addini ya yadda dashiba" momy tace "amma rannan fa haka suka hada kai suka yiwa Usman duka nan yayi ta jinya dana gaya maka ma ko shiga bakayi ka dubashiba yan dabane ko wannan ma bai isa dalilin da za'a hanashi 'yaba?" dady yace "ban yadda sun hadu sun dakeshiba koda ma sun dakeshin tabbas wani abu yayi musu mai girma tunda lokacin da suna yara duk abinda yayi musu ai basu taba dukan nasaba lokacin ma da basu da hankali kenan basu da aikinyi balle yanzu" momy ta kuta sai kuma ta mike tsaye tace "shikenan sai ka aurar da yarinyar na gani ba da izininaba idan kuma zakasa ta bijireminne to sai mu gani" ta sunkuci wayarta tayi daki a fusace, anty zulai ta kada kai to "to haka anty Mariyan ta koma?" dady yayi ajiyar zuciya yana kwanciya sosai jikin kujerar da yake zaune sannan yace "wallahi akan yaronnanne duk ta koma haka kuma duk laifin Usmanne shi yake zugata da su safiya ma sun zugata amma tunda yaron yayi kudi sai kuma suka koma bayansa amma na rasa shi Usman menene matsalarsa ita kuma akwai biyewa yara"

A ranar da Bello da ya dawo daga delta suka takurawa Abdulrahman sai da suka maida Khadija gida shi dama so yayi sai ya sakeyi mata echocardiogram ya tabbatar ta samu lafiya kafin ya sallameta shi kuma akwai interval din da ake dauka tsakani kafin a sake wani amma yanzu dole ya maidata gida.

Tana komawa gida kuma Bello yaje ya marairaicewa hajiyarsa akan ta lallaba su Abdulrahman din su bari ta tafi da Khadija Dubai a cewarsa idan aka fita da ita kasar waje ta dan huta zatafi warwarewa akan a gida da zasu barta ita kadai ko 'yar uwa mace ma babu, nan da nan kuwa hajiya ta karbi shawarar tasa dama kullum tana sha'awar idan taga uwa ta tasa yarta a gaba sun tafi kasashen duniya shopping sai taji inama itama tana da ita da sunje gashi dama tun dawowar Bellon basu taba fita wata kasa tareba sai dai babura kawai.
Ba karamar drama kuwa akashaba kafin suka yadda da tafiyar tata Abdulrahman fadi yake "ni hajiya bawai banason taje bane kinga bata da lafiya cikin jirgin nake tsoro tunda bata taba hawaba zata iya tsorata idan zai tashi hakan kuma zai iya janyo mata relapse" Bello yace "karka damu Abdul tare zamuje bazan bari ta tsorataba" duk suka tsaya suna kallonsa har hajiyan dan dai ita basuyi dashi zai bisuba amma sai ta basar batace komaiba, Abdulrahim ya kalleshi yace "ha! Speaking of jin tsoro ka manta yadda kayi ranar da ka fara hawa jirgi? Hajiya kingansunan wannan ya rikeni ta nan wannan ya kankameni tanan kamar zasu yagani wai duk tsoro sukeji as if an gaya musu mutuwa ake in an shiga jirgin" Bello ya harareshi yace "karka rainawa kanka hankali yaushe naji tsoro?" Abdulrahim yace "kaidai ne kake neman ka rainawa kanka hankali" hajiya tana dariya tace "ohh Allah zasu fara ku dai kamar masu ganin hanjin juna indai kuka zauna sai kunyi fada" Abdulrahim yace "wallahi hajiya Abdulmalik dinne dan rainin wayo baya bani girma kwata kwata" Bello ya harareshi yace "kaifa bakasan asalin date of birth dinkaba maybe ma na girmeka" Abdulrahim ya bude baki zaiyi magana Abdulrahman yace "dan Allah ya isheku mu koma maganar gaskiya maganar tafiya da Khadija ko aa" a karshe dai suka yadda za'a tafi da ita wanda dama tunda aka sallameta daga asibiti ta dawo nan gidan prof saboda can din ba kowa bai kamata su barta a gida ita kadaiba.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Historias para obsesionarse. Descúbrelo ahora