Har dady yakai bakin kofa momy tace "dady" muryarta na rawa alamar kukan da takeyi, bai kulataba yayi waje ita kuma ta mike da sauri ta biyo bayansa tana cigaba dayi masa magana, suna fitowa ya juyo a fusace batayi auneba sai ji tayi ya dauketa da kyakykyawan mari wanda sai dataga wucewar wuta a idonta ta kuma zube a wajen, dady ya nunata da yatsa. Yace "mariya me nace miki? Me nace miki akan yarinyarnan?" da gudu Abubakar yazo ya riketa tace "wallahi Allah dady zuwa nayi na gaya mata na yadda na tarar da ita a haka wallahi na yadda a aura matashi" cikin fushi dady yace "na gaya miki ina bukatar yaddarki? Bana bukatar yaddarki idan kinso ki mutu amma insha Allahu sai na aurawa Amira Abdulrahman ko kinaso ko kinaki kuma daga yau tabar gabanki dauketa zanyi gaba daya sai kin sake ganinta sannan zaki nemi kashemin ita, tunda ke bakya sonta mu muna sonta kuma da kike maganar sun daki danki ke kin binciki dalilin da yasa suka dakeshin? To kanwarsu yace yanaso duk da sunsan ba sonsu yakeba suka yadda shine ya zagesu a gabanta ta tare musu ya daketa, ko aurenta yakeyi kuwa ya saka hannu ya daketa wallahi ko ni ubansa sai na kashe auren bayan ya kwana a hannun yan sanda mutuniyar banza kawai gani kikayi ana lallabaki shiyasa" Umar ya rike hannun dady yana cewa "dady please ya isa haka dan Allah ku daina" dady ya juyo ya kalli umar yace "Umar ai an daina ba za'a kumaba ba sai tana gidan sannan za'a kumaba? Idan tabar gidan ai banma gantaba balle nayi mata magana" umar ya kara kankame hannun dady su Abdulrahim ma duk suka taso suna bashi hakuri ana haka Usman ya shigo sai kuma ya tsaya yayi dim yana kallonsu momy na kasa tana kuka su kuma duk sunyi wani carko carko, da hanzari ya karaso wajen momy yana cewa "subhanallahi momy lafiya menene ya faru?" ya daga kai yana kallon abubakar yace "yaya menene yake faruwane?" Abubakar ya dafe koshinsa saboda wani irin sarawa da yake masa yace "Amirace" Usman ya kalli kofar dakin Amira ya kuma kallon Abubakar yace "tayi me?" Abubakar yace "ta sami attack ne" Usman ya kuma kallon kofar dakin Amiran sannan yayi wata yar dariya yace "wallahi karya take pretending ne" ai kuwa kamar ya ballo dam din daya cika yake shirin ballewa da kansa, anger din da ba'a bari dady yayi releasing akan momyba ya juye masa dan rufeshi kawai yayi da duka kamar wanda Allah ya hallicceshi purposely dan ya dakeshi.
Gaba daya gidan suka fara kokarin rike dady yayinda Abdulrahim ya janye Usman daya tsugunnun da dady bai barshi ya mikeba momy kuwa ko motsi batayiba sai kara sautin kukanta da tayi, dady yace "kai wanne irin tantirine Usman? Kaine silar komai amma ba zamaka ji tausayin yar uwarkaba ta kusa mutuwa sannan kace wai pretending take? Wato bata dameka bama ko tayi rai ko ta mutu ko?" dady na cikin wannan fadan Aliyu ma ya shigo da earpiece dinsa a kunne dan baisan abinda ke faruwaba sai daya shigo yaga mutane a tsaye carko carko da sauri ya zare earpiece din yana binsu da kallo, ga masu kuka nan nayi (momy da Khadija) ga kuma masu tashin hankali rubutuce a fuska tamkar zai fara diga kasa dan yawa, jiki a sanyaye ya karaso dakin koma menene yasan ba abin arziki bane yake faruwa ya kalli umar da yafi kusa dashi kamar me rada yace "what's going on?" fuskar umar kamar zaiyi kuka yace "Amira ce..." ai Aliyu baiji karshen zancenba ya fara kiran "innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbiyallahu wa ni'imal wakil" kawai sai yayi dakin Amiran da gudu shima umar ya bishi sai a ciki ya samu ya kamoshi suka fito har ya fara hawaye kira yake "yaya Umar me ya sameta ba abinda ya sameta ko tana raye ko? Innalillahi" dady ya dan dauke kansa yace "hmm" sannan ya kalli Usman da shima ya fara hawaye yace "kagani ko? Kaga yaran arziki masu son juna ko? Baima tsaya an gama gaya masa abinda ya sametaba amma hankalinsa ya tashi babban tashin hankalinsa ace wani mummunan abu ya sameta amma kai da yake shedanne a kanka abinda ka farayi shine dariya ka kumace wai pretense ne, wallahi banda kai a gida aka haifeka na rantse da Allah da cewa zanyi kai ba dana bane musanye akayimin dan gaba daya komai naka ya fita daban ka fita daban da yan uwanka banda kamanni, ba abinda zance maka sai dai Allah ya shiryeka ya nuna maka hanyar daidai" yana rufe bakinsa ya juya ya fice daga gidan, su Abubakar dai babu mai bakin magana sai zagaye momy da suka sakeyi harshi Usman din shi kuwa Abdulrahman juyawa shima yayi ya fita harabar gidan sai kuma ga su Bello sun biyo bayansa duk suka samu waje kan baranda suka zauna kowa yaza uban tagumi.
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
