Page 1

1.2K 35 4
                                    

MATAR AMEER...(2021)

By Princess Amrah
NWA

Page 01

Kanta ta hada da guiwa, in banda kuka babu abin da take yi. Cike da jin haushi matar da ke gefenta ta dafa kafadarta, duk da takaicin da ke lullube da zuciyarta hakan bai hana ta tausasa kalaminta ba ta ce,
"Ki yi hakuri ki daina kukan nan Ameerah. Ke ba 'yar karamar yarinya ba balle in rarrashe ki, sannan kin tasa ni a gaba tun bakwai na safe kike ruzgar kuka kin ki yin shiru. Wai ya kike so in yi da ke ne? Ya kike so in yi da raina? Ko so kike ni ma in yi kukan duka sai mu taru mu zama daya? Kin ga idan Babanku ya dawo shi kenan shi ma sai ya jone mu yi tare. Idan su Saddam ma suka dawo duka sai mu ci gaba da yi tare har Sumayya."

Cikin kukan da Ameerah ke yi ta dago ta saki dariya. "Lallai ma Ammi." Kawai ta fada tana kara hada kanta da guiwa tana neman ci gaba da wani kukan.

"Bari ki ga in tashi na gane zana kike so ba wani abu ba. Kukan naki ma na iya-shege ne." Mami ta fada tana yunkurin mikewa.

Mikewar ita ma ta yi Ameerah tana dira kafafuwanta a kasa.
"Wai don Allah Ammi idan ban yi kuka ba me zan yi? Kin gani fa duka-duka kwana biyar kenan da dawowar Yah Ameer amma babu ko kunya sai ga shi da sassafe ya zo min sallama wai zai tafi Kebbi Ammi sau biyu fa kawai muka hadu da shi sai na ukun yau da ya zo yi min sallama..."

Guntun tsaki Ammi ta yi, ta mike hade da fadin "Ai shi ya sa na ce duka kike so. In banda samun wuri, daga abun kirki ma ya zo miki sallamar? Idan wani ne ai sai dai kawai ya kira ki a waya ya ce miki ya tafi. Amma kika ci sa'a duk sammakon da ya yi hakan bai hana shi zuwa ya ga fuskarki ba."

Ajiyar zuciya Ameerah ta sauke, gaskiya ne abin da Ammi ta fada mata, domin kuwa tafiyar kanta ta zame masa dole ne kamar yanda ya fada mata. Sai dai ita ya za ta yi? Baki daya kewar Ameer take yi, tun suna da kananan shekaru karatu ya raba su, sai yanzu da ya kammala ya dawo ne kuma sai ya ce zai tafi Kebbi kuma wai har sati biyu zai yi? Ta share guntuwar kwallar da ta kara sauko mata hade da nufar upstairs.

Gyada kai kawai Ammi ta yi, ta shafi fuskarta da hannunta na dama sannan ta nufi kitchen a zuciyarta tana jinjina girma da karfin soyayyar da take tsakanin wadannan masoyan guda biyu.

Wanka Ameerah ta yi bayan ta fito ta zira doguwar rigar material mara nauyi sannan ta feshe jikinta da turare. Wayarta ce ta ji tana ringing, special tone dinsa ne wanda hakan ya saka ta sakin sassanyan murmushi ta nufi daukar wayar. Can kuma ta tsino baki ta ce "Ba ma zan dauka ba yanzu sai ta tsinke ka sake kira." Ta murguda baki tana kokarin shafa kwalli.

Bayan wayar ta tsinke ya sake kiran ta, da gaggawa ta dauka don dama da kyar ta iya daurewa, ba ta iya jurar ganin kiran Ameer ba ta dauka ba sai da babban dalili.

Dauka ta yi ba tare da ta ce komai ba ta ji shi ya ce "Matar Ameer..." cikin wata irin murya mai cike da zallar soyayya.

Kiran ta da wannan sunan kadai ya mantar da ita fushin da take yi da shi. Ta saki murmushi tana fadin "Mijin Ameerah..." ta gatsine baki, "Bayan ma ka tafi ka bar ni, kana ji kana gani ina kuka a haka ka tafiyar ka, maimakon ka fasa tafiyar."

Dariya ta ba shi, sai dai bai isa ya dara ba, ba wuya za ta kara hasala in dai Ameerah ce.

"Yi hakuri masoyiya, kin san ba da son raina na tafi ba, don tafiyar ta zame min dole ne. Ki yi hakuri kin ji? Idan na dawo zan dauki kowanne irin hukunci naki amma ba zan iya jurar fushinki ba. Ki yi hakuri ki saki ranki ko zan samu yin abin da ya kawo ni cikin dadin zuciya."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now