Page 4

514 19 0
                                    

MATAR AMEER...(2021)

By Princess Amrah
NWA

Page 04

"Hello...I'm home."
Ameerah ta fada bayan ta shigo cikin parlor. Takalminta ta cire tana jin muryar Amminta na fadin,

"Ban san ko sai yaushe Ameerah za ki san kin girma ba. Kin shigo babu sallamah sai yaren nasara."

Dariya Ameerah ta yi tana tinkarar dakin Ammin ta inda ta jiyo muryarta.
"Hajia Doctor Ammin Ameerah..." ta fada kan jikinta tana dorawa da
"Ai ba zan taba girma ba in dai ina tare da Ammina."

Gyada kai kawai Ammin tata ta yi tana fadin "Ni dai sake ni. Kina ganin a gajiye nake ni ma ban jima da dawowa daga aiki ba."

Daga ta ta yi tana jiyo muryar Ameer da ke rafka sallama.

"Au, ashe mutumin naki ya dawo."

"Eh ya dawo Ammi. Bai ko ci abinci ba ya dangana da inda nake. Ya yi sa'a dama na gama."

"To ma shaa Allahu. Sai ki je ki zuba masa abincin ai ki kai masa garden. Ban kuma ce ki je ki hana shi ci ba."

Ameerah ta kwakkwabe baki tana dire-diren kafa,
"Ni na lura Ammi kamar kin fi son Yah Ameer a kaina."

Guntun tsaki Ammi ta yi,
"Ke ba ki san ma abun nan ba ya miki kyau ba. Ki bari autata ta yi amma ba ke ba gotai-gotai."

"Ba wata auta Ammina. Ai dai na tabbata ko a wurin aiki ko a family ba a kiran ki Maman Sumayya, sai dai a ce Maman Ameerah. Ko na yi karya?"
Ta karisa maganar da dariya sosai tana barin dakin.

Haka suke gidan nasu, tamkar kawayen juna tun daga mahaifinsu har zuwa kannen Ameerah. Dukkan wanda zai zo gidan sai ya tafi da shaawarsu, saboda yanda suka shaku da junansu, iyayen ke sakartar da kansu a cikin ya'yansu.

"Yah Ameer bari in kai maka abinci garden, ka ci kafin in gama in fito." Ta fada hade da nufar hanyar kitchen. Ammi ta san ko ta ce ta kai masa abincin a dining area ba zai iya ci da kyau ba.

Tana gama zuba masa abincin ta nufi garden da shi. Tsararren wuri ne inda aka zagaye shi da shuke-shuke, ga wasu irin furanni masu tsananin kamshi da kyau. Daga can gefe kuma kujerun shakatawa ne kowanne da teburi a tsakiyarshi. Sai wani irin kurtu mai dan fadi wanda ruwa ne a cikinsa yake ambaliya hade da furanni masu kyau. A takaice dai wuri ne da dukkan mai rai zai tsinci kansa a walwala idan ya zauna.

A tsakiyar teburin ta girka babban tray din da ke kunshe da hadaddun food warmers, sai plate da bowl, a gefe guda kuma jug ne wanda aka cika da chapman. Bayan ta ajje ta koma parlor ta sanar da shi sannan ta haye sama inda dakinsu yake ita da Sumayya. Kayan jikinta ta rage sannan ta daura towel ta shiga wanka.

Da ta fito cantu cream kawai ta shafa ta feshe jikinta da bode spray na burmi oud da ya kasance favorite turarensu ita da Ameer, kamshinsu iri daya ne kowa ma ya sani. Top gown ce ta saka sai ta dora boyfriend jacket a kai, ta yi tolling white veil sannan ta dauki wayarta ta fita.

Ta samu ya gama cin abincin yana latsar waya. Ba ta yi sallama ba sai tafi da ta yi da karfi wanda ya sanya shi zabura yana kallon ta.

"Ni kam ban san sau yaushe ne Yah Ameer zai zama jarumi ba." Ta fada tana zama kan kujerar da ke fuskantarshi.

"Sai ranar da Ameerah ta girma da tsokana." Ya ba ta amsa hade da gatsine bakinshi.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now