Page 30

231 15 3
                                    


Page 30

Suna zaune tare da Daddy kamar yanda suka saba duk dare, wayarshi ta yi ringing. Doctor Awwal Psychologist ya gani a rubuce, hakan ya sanya shi gaggauta dauka yana kara wayar a kunnenshi.

"Barka da dare Doctor."
Daddy ya fada cikin sakin fuska.

"Yawwa Alhaji, barkanmu. Ina wuni?"

"Lafiya lau. Ya iyali?"

"Alhamdulillah." Doctor Awwal ya fada, yana dorawa da
"Ya mai jiki?"

"Ya ji sauki sosai. Gaskiya ba laifi ana samun improvement. Sai dai ciwon yana yawan tasar masa yanzu. A rana sai ya buge shi sau uku, mun ma gaji da zuwa asibiti, allurar kawai ake zuwa a masa a gida."

"Subhanallahi! Shi ne kuma Improvement din Alhaji?"
Ya fada cikin mamaki.

Gajeren murmushi Daddy ya yi, ya ce
"Sosai Doctor. Mutumin da da ba ya fara'a, amma yanzu koyaushe fuskarsa cikin annuri take duk da ba wai dariya yake yi ba. Sannan ya saki jikinshi sosai da mu, idan yana da bukatar wani abu babu haufin komai yake danna bell. Sannan abu mafi jin dadin ma shi ne yanda ya fara gane magana sosai."

"Ah gaskiya an gode ma Allah. To amma kuma Alhaji yawan bugunsa da ciwon nan yake yi anya babu wani abu da yake faruwa?"

"Wani abu kamar me kenan Doctor?"

"Kamar yawan tunani. Matukar zai sanya ma ranshi sai ya tuna da wani abu na rayuwarshi to haka ciwon zai yawaita bugunshi. Ko kuma may be idan ya sha magani ba ya samun hutu, brain dinshi ba ta relaxing kamar yanda ake so."

Dan shiru Daddy ya yi, kafin ya ce
"Tun dai kwanaki ciwon ya zo masa da wani irin salo, yana ta kokarin magana amma ta k'i fitowa. To daga nan ne ciwon ya yawaita sosai."

"Tabbas bai rasa nasaba da yawaitar tashinshi. Yana da kyau in gan shi ido da ido. Gobe da safe kafin in wuce aiki zan biyo ta nan."

Murmushi Daddy ya yi,
"Kar mu shiga time dinka Doctor, ko su zo su same ka da shi goben?"

Murmushin shi ma Doctor Awwal ya yi,
"Kar ka damu Alhaji. Zan zo in shaa Allahu. Already ina da address dinku."

"To likita, godiya muke."

"Babu komai, yi wa kai ne."

Daga nan suka yanke wayoyin. Daddy ya yi wa Labiba bayanin yanda suka yi da Doctor Awwal din.

Washe gari da sassafe Doctor Awwal ya zo, ya kira Daddy ya ba shi izinin shigowa.

Labiba ta tarbe shi suka nufi dakin Ameer. Ya tashi daga bacci yana kallon ceiling. Jin sallamar su Labiba ya sanya shi kallon kofar yana sauke ajiyar zuciya.

Kan kujera Doctor Awwal ya zauna, sai ga Daddy ma ya shigo. Ya ba shi hannu suka gaisa cike da aminci.

"Mallam Muhammad ya jikin naka?"
Doctor Awwal ya fada yana kallon shi da sakin faffad'an murmushi.

Kai kawai Ameer ya d'aga masa.

"Alhamdulillah. Gaskiya na ga ci gaban da aka samu."
Ya fada yana sake examining dinsa.
"Kalle ni nan Muhammad."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now