Page 17

279 19 0
                                    

Page 17
***

Da murmushi take kallon shi, tana nema musu amincin Allah tare da karasowa cikin dakin.
"Yah Muhammad afwan yau na makara ko? Wallahi mun je airport ne tarbar Aunty Aysha yau suka dawo daga tafiya." Ta zauna tana sakin nishi.
"Ka ci abinci dai ko?" Ta bude kular abincin da Daddy ya ce a rinka kawo masa a restaurant kullum ya biya kudin sati guda.
"Yah Muhammad ba ka ci abinci ba. Doctor Awwal bai shigo ba ne?" Ta ja kujerarta zuwa kusa da shi. Cokalin ciki ta warware daga jikin tissue, ta kalle shi tana fadin
"Haa."
Ba musu ya bude bakin ta zuba masa abinci. Bayan ya cinye ta sake nuna masa da bakinta alamun 'haa' din ta zuba masa. A hankali take ba shi abincin har sai da ya ci daidai cikinshi, ta fahimci ya koshi sannan ta jawo tissue ta goge masa bakinsa. Robar ruwa ta bude ta zuba a cikin karamin kofi ta ba shi ya sha.

"Yawwa Yah Muhammad dina. Ka yi hamdala ko?" Ta sakar masa murmushi. Ko kallon ta bai yi ba sai dan runtse idonshi da ya yi.

"Kana jin bacci ne?" Ta mike ta fara kokarin kwantar masa da gadon.
"Ka yi baccinka sosai, bari in je wurin Doctor Awwal in ji yanda ake ciki batun zuwa psychiatry din. Gwara idan sun gama da kai ne mu san inda muka dosa."

Ta kama hanya ta fita. Da sallama ta shiga Office din nashi ya amsa, bayan ta gaishe shi ya ba ta izinin zama, ta zauna tana kallon shi ya rufe takardun da ke gabanshi.

"Kanwar patient kina lafiya?"

"Alhamdulillahi Doctor. Ya aiki?"

"Lafiya lau. Dazu na shiga ai na samu yana barci. Sai ban tashe shi ba kawai na taho. Na yi mamaki da ba ki zo ba har lokacin ai. Na ce ko wani uzurin ne ya tsayar da ke?"

Murmushi ta yi tana fadin
"Eh Doctor na je Airport ne."

"Okay. Gaskiya sai dai mu kara gode wa Allah, domin kuwa kullum kara samun improvement ake yi. Ya ji sauki sosai ciwukan  nashi ma na ga duk sun fara k'amewa. Dama kuma ciwo shi yake shiga baki daya, sauki sai a hankali."

Ta jinjina kai tana kallon shi.

"Mun yi magana da Doctor Lucas. Ya ce nan da 2 days ma za a sallame shi. Za a mayar da shi psychiatry, amma ba wai za a yi admitting dinsa ba ne ba, za dai a rinka kai shi ne duk bayan wadansu lokuta, kuma ana karbar masa magani. Mu kam mun gama da shi."

"Ok Doctor. Thank you so much."

"You're welcome my dear. Sai dai ni ba na nan za a yi discharging dinsa, because gobe zan yi tafiya may be sai after 2 weeks zan dawo. So I have to tell you do's and don'ts na yanda za ku kula da shi. Na so Alhaji yana nan don in jaddada a gabanshi, but fine, tunda na lura kina da hankali sosai da nutsuwa." Ya mayar da dukkan hankalinshi gare ta.

"Mai irin larurin nan ba ya son kad'aici ko kadan. Saboda kadaici ko ga mai lafiyar ma yana d'arsa abubuwa mabambanta, ka zauna ka yi ta sake-saken abubuwa, ka yi ta tufka da warwara, to balle kuma mai larurar kwakwalwa, ba wuya duk wani treatment zai rinka dagulewa yana komawa baya. So ku kula sosai kin ji? Sannan abu na biyu, a nisanci yanayin damuwa ko tashin hankali, kula ko bayyana damuwa k'arara na rikita masu irin wannan larurar, yana dagula lissafinsu, yana kuma kulle wasu abubuwa da ake kokarin ganin sun kwance. Sai abu na uku, ku rinka duba yanayinshi, masu dementia kan iya wayar gari ko kadan ba su son damuwa ko kusanci mai yawa, a duk sadda kuka gan shi a irin wannan yanayin, kar a yawaita shige masa, magana ma kar a yi mai tsayi sosai da shi, simple sentences wanda ba su wuce 5 zuwa 7 ba. Daga nan kuna iya barinshi da favorite dinsa, may be watching movies, football, or anything dai da kuka san yana so. Within some hours za ku gan shi ya dawo normal. Daga nan sai a ci gaba daga inda aka tsaya. Abu na hudu shi ne kar a rinka forcing dinsa a kan duk abin da ya nuna yana so zai yi, ko kuma abin da ya nuna ba ya so ba zai yi ba. Idan a hankali kun nuna masa kar ya yi still ya yi insisting, ku bar shi ya yi din, tilasta shi zai iya k'ara dagula masa kwakwalwa. Na biyar, hayaniya ko daga murya duk ba su dace ba a inda yake. Magana cikin aminci ita ce daidai da masu irin larurarshi.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now