Page 16

266 18 0
                                    

Page 16
***

Yau da wata irin kewar Ameer ta tashi. Sati guda kenan da bayyanar rashin Ameer din, sai dai ji take tamkar an shekara babu shi. Tunda take ba ta taba daukar ko kwana biyu ba su yi magana ko a chat ko a waya ba, duk runtsi za su nemi junansu, ko da rigima ce ta hada su atata awanni biyar, za ta neme shi ko kuma shi ya neme ta. Har akwai lokutan da karatu ya masa zafi sosai, amma duk da haka yakan ware lokutan da za su yi magana ko da kadan ce. Idan wani daga cikinsu ma na ciwo, sukan nemi junansu ko na kalilan din sakan ne su dai ji muryar juna.

Wannan dalilin ne ya sanya ta wahala sosai. A kullu yaumin jin rashin Ameer take a matsayin sabon abu gare ta. A rana tana neman lambar wayarshi sau ba adadi, haka kuma lambar da ta karba wurin Abban Ameer wadda aka masa text ranar da Ameer din zai dawo. Har MTN Office sun je an yi bincike a kan layin, sai dai babu wata tsayayyar magana a kai.

Wani irin kuka take yi, shi ba mai sauti sosai ba, sai dai hatta kumnuwanta suna amsa kuwwarshi. Kanta ta kife a saman pillow, tana wata irin shessheka, tana jin tamkar zuciyarta za ta bare ta fito.
'Sai yaushe ne zan samu sassauci? Sai yaushe ne zuciyata za ta aminta cewa Yah Ameer ya riga ya tafi inda ba a dawowa?' Ta tambayi kanta.

Ta kwashi kusan minti ashirin duke a wurin tana kuka, idanuwanta take ji suna mata tsattsaurar zinga, har tana ji tamkar za su zazzalo waje. A daddafe ta duke ta shiga bandaki. Ta wanke fuskarta sannan ta fito, don ba ta so Ammi ta gane halin da take ciki, ba ta son yanayin da take jefa iyayen nata a ciki.

Sumayya ce ta shigo da gudu dan dama sun yi hutun islamiyya. Ta fada kan jikin Ameerah,
"Aunty wai ki shirya inji Ammi za mu fita."

"Zuwa ina?" Ta fadi cikin pretending kar Sumayya ta gane kukan da ta yi. Sai dai ba ta sani ba, duk wanda zai kalle ta sai ya san fuskarta ba daidai take ba. Saboda yanda idanuwanta suka kad'a suka yi jajur. Sannan rumfar idon ma kanta a kumbure take.

"Ni dai ban sani ba haka kawai ta ce in fada miki. Allah ma Ya sa Pack za ta kai mu daga nan mu wuce Havilla ice cream."

Ameerah ta gyada kai tana murmushi sannan ta mike domin sauya kaya. Doguwar riga ce ta atampa, tana da manyan zane blue da red, hakan ya sanya ta zira dogon hijabi mai hannu light blue.

"Yanzu Aunty idan pack za mu je kuma sai ki saka wannan dogon hijabin? Ina ma laifin ki yafa gyale." Sumayya ta furta tana bin Ameerah ta kallo.

"Kya dai kai su in kaya ne. Ni dai ba zan sauya hijabin nan ba."

Tabe baki ta yi tana sauya kayan ita ma.
"To ya mutum zai yi? Tunda Yaya ta sanya dogon hijabi ai dole kanwa ma ta sanya dan kar 'yan sa ido su dame ta da surutu."

Ita dai kadai ke kidinta tana rawarta. Ta saka irin atampar jikin Ameerah amma ita red din hijabi ta sanya.

A tare suka sauka, Ammi har ta shirya su take jira.
"Yau ake bakwai din Ameer. Duk da sun ce ba taron addu'a za a yi ba amma dai na ga cancantar mu je din shi ya sa na ce ki shirya. Tun ranar uku ba mu sake komawa ba."

Kai kawai Ameerah ta daga tana jin wani abu ya mata babakere a tsakanin kirjinta. Ita kam ba ta san ranar da wannan abun zai fice mata ba, ba ta san ranar da kirjinta zai daina nauyi ba.
Bakinta ko abinci ta ci d'acinsa take ji saboda rashin appetite, sai dai kawai ta ci saboda maganin yunwa, da kuma tilascin da Ammi ke mata.

Cikin motar Ammin suka shiga, Ameerah a gaba sai Sumayya baya tana zuba surutu.
"Dan Allah Ammi zan roki wata alfarma ni kam."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now