Page 35

228 18 2
                                    


Page 35

It is with great pleasure that I am here to celebrate another year of my life. I am grateful for surviving all the challenges throughout the last 365 days and turning a year older.
Happy birthday to me🥳🎉🥰

***

Wani irin farin ciki ne mamaye da zukata da fuskokinsu. Ko ba ka san su ba idan ka yi musu kallo guda za ka san cewa lallai mutanen biyu suna cike da nishadi. Cike da annuri Daddy ya ce

"Na jima ina neman wannan hanyar, ina neman wannan damar, sai dai ina ta ganin hakan ba mai yiwuwa ba ne. Ashe kana taka ne Allah kuma Yana naShi. Na ji dadi sosai abokina."

Shi ma Khaleed Zannah din annuri bai kau daga saman fuskarshi ba ya ce
"Na yarda da kai abokina. Da gaske ban dauka yaran za su amince cikin sauki haka ba, na dauka za su k'i yarda shi ya sa ma ban gama daukar abun da muhimmanci ba. Ashe za su karbi zabin namu da hannu bibbiyu."

"Allah ne Ya dubi zumuncinmu tun na yarinta Ya ga cancantar bai kamata ya yanke daga kanmu ba, shi ne Ya saukaka mana lamarin."

"Haka ne Likita."
Khaleed Zannah ya furta yana murmushi.
"Yaushe za mu kawo kayan sa rana da sauran abubuwa?"

Daddy ya maka masa duka da karfi
"Babu wannan a tsakaninmu. Kar ka manta ni da kaina mai siyan kayan neman auren Junior in kai ne. Don haka, dukkan wani abun bukata ni zan saya, shi din ma saboda family and friends su shaidi sa ranar ne ba don wani abu ba. Zan sayi dukkan abin da ya dace zan kai musu."

"Kuma dai? Anya kuwa za a yi haka Likita?"

Gyada masa kai Daddy ya yi, kafin ya ce
"Kar in ji wani zance makamancin haka daga bakinka Khaleed Zannah. Duk mun wuce wannan zamanin. Yanzu kawai abin da nake so da kai shi ne ka turo Junior wurinta, saboda su fara shakuwa, na tabbatar da in dai sun so a cikin wata guda ma za su iya shakuwar, to balle kuma har wata biyu."

Kai ya jinjina Khaleed Zannah, yana fadin
"Tun jiya na fada masa ya yi kokari ya fara zuwa, na tabbata zai zo din."

"To alhamdulillahi. Allah Ya tabbatar mana da alkhairi Ya gwada mana lokacin lafiya. Allah kuma Ya daidai tsakaninsu."
Daddy ya furta yana mikewa.
"Ni bari in wuce abokina, daga nan ma asibiti zan nufa akwai meeting da za mu yi karfe sha biyu."

"To amin ya Rabbi. Allah Ya taimaka."

Daga haka Daddy ya fice, cike da farin ciki yake driving yana ayyana yanda bikin 'yar lele da dan lelensa zai kasance.

Da yamma bayan la'asar Ameerah ta shigo gida. Sai da ta fara wucewa ta dakin Ammi ta gaishe ta sannan ta nufi kitchen don wata irin yunwa ce ta dawo da ita. Jollof din macaroni mai kifi ce aka yi, ta zuba daidai cikinta sannan ta debo kunun aya a glass cup ta dawo parlor bisa carpet ta hau ci.
Bayan ta gama ta dauki jaka da wayarta ta haura sama. Wanka ta yi, ta saka rigar material mara nauyi, sannan ta feshe jikinta da turaren burmi oud. Hula ta saka kalar rigar sannan ta dauki wayarta ta sauka parlor, a daidai sannan Daddy ya shigo Sumayya biye da shi ya dauko ta daga makaranta.

Murmushi Ameerah ta saki tana yi musu sannu da zuwa, ta karbi lemu da ruwan faro da ke hannun Daddy da alama a wurin meeting ne aka ba shi su, ta kai fridge.

"Sumy Gayu 'yan makaranta."
Ta fadi da murmushi a fuskarta.

Sumayya da ke hawan bene ta juyo ita ma da murmushin a fuskarta ta ce
"Aunty sarkin tsokana."
Tana tsananin jin dadin yanda Ameerar ta saki jikinta yanzu.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now