Page 51

214 11 0
                                    


Page 51

Tare suka shiga kitchen su duka suka hau aikin girki. Farar shinkafa da miyar kaza suka yi, sai hadadden tofu salad, sai kuma kunun aya wanda ya ji kwakwa da dabino.

Ameer ta fara zuba mawa ta kai masa har daki saboda ya bar musu falon ne don sauran su saki jikinsu sosai.

"Yau shi kenan kin ga 'yan uwanki kin guje ni ko Matar Amir?"
Ya fada yana kama hannunta.

"Am so sorry darling, ka ga bai kamata su zo ba kuma in tare wurinka in bar su."

Ya dan tabe baki yana sakin hannun nata bayan ya jawo ta ya manna da jikinshi.
"Na ji, na kuma yarda. Amma dai ai kya dan rinka zuwa duba ni a kai a kai ko?"

"Yi hakuri to ka yafe min."
Ta fadi tana kiciniyar kwace jikinta.

Ya jawo fuskarta daf da tashi har hancinshi yana gugar nata ya ce
"Na yi. Ya aikin? Ya gajiya?"

"Alhamdulillah."
Ta ba shi amsa a hankali.

Bakinshi ya hada da nata, sun kai minti biyu a haka kafin ya bar ta ta tafi.
Ko da ta je parlor har sun zubo abincin a tray ita suke jira.

"Am sorry for keeping you waiting."
Ta fada tana zama kusa da Labiba.

"Babu komai fa. Ni sai da na ce ai dama tare kika zuba muku ku ci a can kawai."
Labiba ta fada cikin sigar tsokana.

"Kar mu fara 'yar haka da ke."

"Allah kuwa ai gaskiya ce. Mun zo mun hana ki zama tare da mijinki."

"Labiba zan miki fashin goshi idan ba ki bar ni da zancen nan ba."

Dariya suka dauka su duka sannan suka fara cin abincin.

Suna gamawa ana kiran la'asar. Sumayya ta hau shiri saboda Marwan ya kira ta ya ce yana kusa da gidan ya shiga masallaci da ya yi sallah zai karaso su tafi.

Bayan Sumayya ta tafi ba da jimawa ba Saddam ya zo. Sai da ya ci abinci ya taba barkwancin nashi da ya saba sannan ya ce da su Labiba su tashi ya mayar da su gida.

Daki Ameerah ta shiga, cikin wata babbar leda ta hada ma su Labiba tarkacen kayan shafa da na gashi masu yawa, tana fitowa ta mika ma Khadija da fadin
"Ga shi nan ku uku har da Fauzah."

Godiya suka yi sosai sannan ta raka su har compound din gidan, ta gaishe da maigadi da ke zaune yana cin abinci ya amsa mata da sakewar fuska sannan ta juya ta shiga gida.

Sai da suka sake yin wanka domin shirin zuwa wurin Daddyn Labiba kamar yanda suka masa alkawari. Bakar abaya Ameerah ta saka sannan ta yana bak'in kallabinta, ba ta yi makeup ba sai magic lip gloss da ta shafa ya zama light pink a bakinta. Shi kuma Ameer black Shirt mai tambarin Channel daga tsakiya ya sanya da blue din 3 quarter, tare suka fito ta rufe kofa sannan ta hau tura shi har zuwa bakin mota. Duk da yake Ameer gurgu ne zaune a cikin wheelchair amma babu wanda zai gan su su biyun nan bai yi sha'awarsu ba. Sun wani irin yin matching da juna, maigadi ma tun daga nesa yake bin su da kallo yana jinjina ma kokarin Ameerah, saboda a wannan zamanin ba kowacce cikakkiyar yarinya ce za ta yarda sa auren gurgun da kodayaushe yana zaune cikin keken guragu ba, sai dai irin wanda ke ma junansu soyayya ta tsakani da Allah wadda babu algus a cikinta, kamar dai yanda Ameerar take son Ameer.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now