Page 22

225 17 0
                                    


Page 22
***

Yana zaune kan sofa din dakinshi ya ji wayarshi na ringing, da ya duba ya ga bakuwar number ce ya latsa yana saka ta a hands free don dama dabi'arshi ce hakan.
Zazzakar muryarta ce ta daki dodon kunnuwanshi.
"Barka da dare Haidar." Ta fada a takaice.

"Yawwa barka. Who are you please?" Ya tambaye ta don shi kam bai gane muryar ba.

"Yeah na san ba za ka gane ba. Sunana Bahijja..."

Tun ba ta kai karshe ba ya ce
"An fada miki ina da wacce nake so?"

Shiru ta yi tana jin wani irin kishi na ratsa ta. Da kyar ta iya budar bakinta ta ce
"An fada min. And I agree ka aure ta, in ya so bayan lokaci kadan sai a yi zancen namu auren, kafin nan na gama graduation preparations dina."

Mamaki ne ya kama shi, ta yanda duk kudi da matsayin mahaifinta amma ta lik'e masa, har ta yarda za ta aure shi bayan ya auri Ameerah.

"I really love you Haidar. Tunda nake a rayuwata ban taba jin son wani d'a namiji ba sai kai. You're the first and last person in shaa Allahu da zan so a rayuwata. I hope za ka so ni, ko da rabin son da nake maka ne."

Shiru ya yi yana matukar al'ajabinta. Wace irin soyayya ce take masa haka?

"Don Allah don't disappoint me Haidar. Ni mutum ce da idan ina son abu nake kaunarshi da dukkan zuciyata. Mahaifina ya dauki kaunar duk duniya ya dora a kaina. Ya yi mamaki lokacin da na tinkare shi da zancen na samu wanda nake so, saboda yanda yake matukar son ganin ya aurar da ni inda zan ji dadi. Tun kafin a yi nisa idan har ka san ba ka jin soyayyata ka fada min gaskiya, in shaa Allahu zan kwakkwafi zuciyata though it's not easy amma zan roki Allah ya sassauta min, Allah ba Ya kallafa wa bawa abinda ba zai iya dauka ba."

Idan har ya ce yana son Bahijja ya yi karya, sai dai kalamanta ba kadan suka ratsa shi ba, sai ya tsinci kanshi da tausayinta, kawai ji ya yi yana son fada mata gaskiya ta je ta nemi wanda zai so ta tsakaninshi da Allah don shi kam ba ya jin sonta. Sai kuma kalaman iyayenshi suka fado masa a rai.
Yanzu idan bai amince ya auri Bahijja ba hakan na nufin asirinshi da na iyayenshi zai tonu? Duk fantamawar nan da yake cikin kudi dole ya daina? Ya gyada kanshi yana tunanin mafita. Ji ya yi ta ce

"Kar ka damu kanka, kar kuma ka takura wa kanka. If you don't love me just feel free and let me know."

Licking lips dinshi ya yi kafin a hankali ya ce
"I do..." ya dan dakata daga nan, yana jin tsananin tausayinta.

"You do what?" Ta tambaye shi cikin matsuwa da jin amsarshi.

"I love you too."
Ya ba ta amsa ba wai don ya kai har cikin zuciyarshi ba.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana sakin hamdala a bayyane.
"Alhamdulillah, na gode wa Azza wa Jalla, now, when are you coming to our house?"

"Whenever you have time."
Ya ba ta amsa a hankali.
"I need to discuss something with you, amma na fi so sai ga ni ga ki."

"Zan ji dadi idan a yanzu ma ka ce min za ka zo."
Ta fada cikin farin ciki.

"Now it's already late. Gobe zan zo around 11am."

"Allah Shi kai mu."
Ta ba shi amsa a hankali.

"Good night."
Ya fada hade da tsinke wayar.
Guntun tsaki ya saki yana jin wani irin takaici mamaye da shi. Allah ma Ya sani ba wai don farin cikin iyayenshi kadai ya yi ba, domin nashi farin cikin ne. Bai san yanda rayuwarshi za ta kasance idan ya rasa wani abu na jin dadi ba. Bai taba sanin babu ba, akwai kawai ya sani. Dalilin da ya sanya shi karbar soyayyar Bahijja kenan.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now