Page 41

233 15 0
                                    


Page 41

A haka ta yi wunin ranar cike da kulawar Amminta, duk bayan minti kadan za ta shigo ta duba ta, sannan ta tambaye ta ko tana da wata matsala. A wannan zamanin dole uwa cire kunya da karar dan fari za ta yi ta kula da 'yarta, saboda mutane ba kowa ba ne yake da karar duba maka naka, idan kuwa ka rasa shi to kai ne ka yi rashi. Hakan ne ya sa Ammi ma ta cire duk wannan karar da take ta Ameerah, dama Haneefa, Saleema da Fareeda ne kadai masu kokarin yi mata karar, to kuma duk ba su riga da sun iso ba, sai dai 'yan uwa da dangi, kowa kuwa harkar gabansa yake, wasu ma kila sun manta da Ameerar a cikin daki, don haka idan har ita ba ta kula da ita ba babu ma wanda zai tuna mata da ita balle har a bukaci jin matsalarta.

(Haka rayuwar nan ta yanzu take, kowa nashi ya sani. Idan har kara da kawaici ka tsaya yi to tabbas za ka ga kara, saboda mutanen yanzu ba kowa ya san wannan ba. Sai dai a inda ka san ana yi maka karar, to sai ka yi. Matsalar da ake fuskanta kenan a rayuwar nan tamu, a da, 'yan uwa suna daukar yaran 'yan uwansu a matsayin nasu, haka dangi ma. Amma a yanzu kowa tasa ta fisshe shi, don haka yi kokari ka ja naka a jikinka, ba a wannan zamanin ba ne ake cewa ka so naka duniya ta ki shi ba ko kuma ka ki naka duniya ta so shi. An dade da wuce wannan zamanin, zamanin da makwafci ma zai dauki danka a matsayin nashi. A yanzu wasu ma burinsu su ga kana janye naka daga jikinka sai su samu damar taya ka. Allah Ya sa mu dace amin.)

Da la'asar aka fara shirin tafiya wurin bud'ar kai. Mommy Haneefa ce ta shigo dakin Ameerah ta ce mata ta shirya tare za a je wurin budar kan 'yar uwarta da ita. Ta ji dadi sosai, ko ba komai za ta rage kewa. Ta kira Bahijja ta fada mata su hadu can gidan amaryar ko kuma ta zo nan gidansu yanzu su tafi tare.

Wanka ta sake yi, ta sanya atamfa super light brown, sannan ta ciro wata lapaya mai kama da Indian sari, kalarta bak'a ce da duwatsu golden brown. Bayan ta daura kallabin atamfar ta nada lapayar. Har ta dauko turare za ta fesa sai kuma ta tuna da hukuncinta a yanzu, ta mayar ta ajiye tana jin hawaye na neman fito mata. Bak'ar kulacca wadda ta saya a wurin ZeeVash (masu son saye ga lambarta nan 09131111029 Abuja take amma tana turawa kowanne gari. Kulacca ce mai kyau mai kamshi ga zama jiki, sannan tana gyara fata ta rinka shining da taushi. Akwai armpit powder ma, wacce idan aka shafa ta babu zufa babu wari, kowanne irin zafi ake yi kuwa.)

Kulaccar ita ta zame mata maimakon turare, saboda kamshinta very soft ne ba ya tashi sai wanda ya shiga jikinka ne zai iya jiyo shi.

Tana gamawa Bahijja ta zo. Tare suka sauka, har an fara kwasar mutane zuwa gidan iyayen mijin Sumayya da ke Makarfi road inda a can ne za a yi budar kan.

A motar Bahijja suka tafi, ita ce zaune a gaba sai yaran Bahijjar a baya suna wasa.

Ko da suka isa duk mutane sun hallara, babban filin gidan cike yake da mutane an jera kujeru, sannan daga can gefe kuma an zagaye wani wuri da ado da kujera ta zaman mutum biyu wato ango da amarya.
Ba a jima ba amaryar ta fito, sai ga angon ma. Iyayen ango suka sayi fuskar amarya a kan naira dubu dari, sannan ango ma ya saya a kan dubu hamsin. Daga nan kuma aka ci gaba da kidi ana zuba ma amarya kudi, inda dangin ango da dangin amarya kowa ya nuna tashi bajintar.

Daidai maghrib aka tashi taron, inda ango da kanshi ya ce zai mayar da amaryarshi bayan isha, su Ameerah kuma gidan amaryar suka koma saboda su gyaggyara mata shi.

Ba ma wani gyara mai yawa ba ne, wanke toilet da turaren wuta ne kawai, sauran ayyukan duk sai da kawayenta suka yi kafin su tafi wurin budar kan.

Sai da su Sumayya suka iso sannan Ameerah suka tafi su ma, Sumayya sai kuka take yi su Ameerah na mata dariya wai kukan shagwaba ne.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now