Page 25

210 13 0
                                    


Page 25

Da hanzari Ammi ta fito daga motar, kafin ta iso har mutane sun zagaye yaron, wurinshi ta je tana kuka tana ambatar sunan Allah.
"Ya Rabbi ka saukaka min, Allah ka kawo min d'auki." Ta fada cikin kuka.

Daukarshi ta yi ta saka a cikin mota tare da wasu matasa guda biyu, saboda yaron almajiri ne, babu ma wanda ya san makarantarsu. Tana kuka ta tada motar, tana yi tana waigen baya inda yaron yake kwance, first U-turn dinta ta sha ta koma asibitinsu. Suna zuwa aka karbe shi emergency, saboda an san ta an san mijinta ya sa ba a tsaya neman 'yan sanda ba kawai aka hau kanshi.

Jin ta shiru har kusan awa daya ba ta iso ba ya sa Saddam ya sake kiran ta.
Cikin kuka ya ce
"Ammi dukkanku shiru, babu ke da Daddy..."

Cikin hanzari ta tarbe shi da
"Na samu karamin accident ne Saddam. But Alhamdulillahi ba da jimawa ba zan iso in shaa Allahu."
Ta fada tana kokarin saisaita nutsuwarta, ba ta so ta fada musu gaskiya dan kar hankalinsu ya kara tashi.
"Har yanzun nan sai da na sake kiran Likita amma bai dauka ba. Ina addu'a Allah dai Ya sa lafiya yake. Bai taba yin irin haka ba."

"To amin Ammi. Ni ma ina tasake kiran shi shiru."
Ya fada yana share hawaye.

"To ya jikin Ameerar?"
Ta tambaya tana fatan ya ce mata ta ji sauki sai ji ta yi ya ce

"Har yanzu dai suna kanta Ammi. Babu wani gamsasshen bayani."

Ta sauke ajiyar zuciya tana fadin
"Ba a kai ta ICU din ba?"

"Eh."
Ya fadi a hankali.

"Alhamdulillah! In shaa Allahu sauki na nan zuwa gare ta. Ku ci gaba da addua. Ina Sumayya?"

"Ga ta nan tana ta kuka Ammi."

"Ba ta wayar." Ta ba shi umurni.

Mika ma Sumayya wayar ta yi, cikin kuka ta ce
"Ammi har yanzu Aunty ba ta tashi ba."
Ta kara barkewa da wani kukan.

"Kina ji na Sumayya? Za ta tashi in shaa Allahu. Ki daina kuka kar ke ma wani ciwon ya same ki. Ku yi mata addua Allah Yana tare da mu."

Kai kawai Sumayya ta daga tana mika wa Saddam wayar.

"Ina Musaddiq?"
Ammi ta tambaya.

"Ga shi." Ya fada yana mika masa wayar.
Shi ne kadai mai dan guntun karfin hali a cikinsu. Ko dama can duk ya fi su hakuri, ga shi da shiru-shiru da zurfin ciki.

"Ku ci gaba da addua Musaddiq. Na samu karamin accident ne har motata ta samu matsala na wuce a gyara, so zan iya taking time kafin in iso. Ku yi duk abin da ya dace. Daddy kuma wayarshi ba a dauka. Amma ina tunanin wani babban uzuri ne ya jawo haka."

"Okay Ammi. Allah Ya kara tsarewa."
Abin da Musaddiq ya fada kenan cikin sanyin murya.

"Ameen yarona. Ku kula da kanku. Zan kira Mommy yanzu in fada mata, sai ta zo ta zauna tare da ku kafin in iso."

Daga haka ta yanke wayar ta latsa kiran Mommy sai dai har ta tsinke ba a dauka ba. Ta kira Mami ringing daya ta dauka da sallama a bakinta.

Cikin yanayin muryar da Ammi ta amsa sallamar kadai ya tabbatar wa Mami da cewa ba lafiya ba.

"Mami ina wuni?"
Ta samu ga gaishe ta a hankali.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now