Page 19

268 16 0
                                    


Page 19

Yau kam tare suka daura aniyar tafiya asibiti  da Maryam. Tun da wuri suka gama shiri, Daddy ma suka tarar ya gama su kadai yake jira.
"Yau har da Hajia Mero?" Ya fada cikin tsokana yana kallon Maryam.

"Wayyo Allah Daddy wannan sunan fa ba na son shi. Kamar wata tsohuwa."

"Dama ai tsohuwar ce. Sunan Kakata ne Hajia Lami."

Dariya sosai Labiba ke yi, kafin ta ce
"Shi kenan ni kam na samu suna."

Cikin nishadi suka shiga motar, Labiba a gidan gaba sai Maryam baya suna ci gaba da hira cike da nishadi.

***
A observation room suka samu Ameer ya dan jingina jikin bango sai kalle-kalle yake yi.

"Muhammad d'ana, ya karfin jikin naka?"
As usual dai, kallon shi kawai ya yi, sai dai kallon da yake wa Daddy da Labiba a yanzu ya sha bamban da irin wanda yake musu a baya. Kallo ne yake musu irin wanda ke tabbatar da ya fara sanin su. Duk da babu fara'a a fuskarshi, sai dai annuri ne mamaye da ita. Sosai ya fara sakin jikinshi da su.

"Yah Muhammad wannan irin kallo haka?" Labiba ta fada tana masa murmushi.
Ta karaso kusa da shi a hankali ta ce
"Ko ina maka kama da budurwarka ne?" Yanda har Daddy da Maryam ba za su iya jin me ta fada ba.

Ameer ya janye dubanshi daga gare ta yana sake kallon Daddy.

Maryam ce ta ciro breakfast din da suka zo da shi daga cikin basket.
"Ki zo ki zuba masa Labiba, ba zai rasa jin yunwa ba." Ta fada tana kallon Labibar.

Babu musu ta dauko kofi ta zuba masa ruwan zafin, ta zuba madara da ovaltine sannan ta jujjuya masa. Ta jawo kujera ta zauna a kusa da shi, a hankali take ba shi tea din har sai da ya shanye duka. Sannan ta zubo soyayyen dankali da kwai ta mika masa.
"Yah Muhammad ko za ka gwada fara ci mu gani? Doctor ya ce a rinka yi ana koya maka ta haka ne za ka fara ganewa."

Bai gane abin da take fada ba, sai dai ganin yanda ta mika masa plate din ya sanya shi karba yana duban ta.

"Ka ci Yah Muhammad, kamar yanda nake ba ka din nan."

Still dai bai gane ba. Hakan ya sanya ta karba ta dibi kadan ta kai a bakinta. Sannan ta masa murmushi tana masa nuni da shi din ma haka zai yi.

Tana sake mika masa kuwa ya yi yanda ta yi din, sai dai bai kara kaiwa a baki ba ya mika mata. Ta karba ta kara ci, ta ba shi shi ma ya kara ci. Da haka suka rinka yi har ya fahimta. Daddy da ke zaune sai murmushi yake musu, yana jinjina wa fasahar da Labibarshi ke gare ta.

Suna cikin haka likita ya shigo. Bayan sun gaisa da Daddy ya shaida masa cewa an gama observing dinsa, don haka suna iya tafiya da shi gida yanzu, tunda dama ba kwantar da shi za a yi ba, 24 hours ne ake da bukatan sake bincikarshi.

Godiya Daddy ya masa sosai, likitan ya ce ya bi shi Office dinshi su yi magana.

Likitan ne a gaba Daddy biye da shi. Bayan sun zauna suka sake gaisawa cikin mutunci.
"Patient din nan bai da matsalar tab'in kwakwalwa ko kadan. Kamar dai yanda bayanai suka gabata a wurin likitoci toh wannan din su ne damuwar shi. Akwai magungunan da zai rinka sha kullum safe da dare, brain dinsa tana da bukatan relaxing kanta, so a duk sadda ya sha su, ku bar shi shi kadai, so samu ma ya yi barci ya farka sannan ya ci gaba da zama a cikin mutane. Idan ana tafiya a sannu ciwon nashi za ku ga yana yin sauki, yana rage bugunshi, to daga nan za a rage masa karfin magungunan, wanda yake shan guda biyu zai dawo guda daya, mai guda daya kuma zai koma rabi, daga haka ma har a zo lokacin da zai daina shan su baki daya. Fatanmu dai shi ne a dage, idan ya tsallake ko da rana daya ne bai sha maganin nan ba za a iya samun matsala, don haka idan ma alerm za ku yi setting fine, safe da dare, kuma yana shan su ya kwanta tun kafin su sake shi ko ya kwanta barcin ma ya k'i zuwa."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now