Page 42

271 15 0
                                    


Page 42

Mamaki ma hana ta magana ya yi, sai bin shi da idanuwa kawai da take yi. Sai yanzu take daukar maganganun Ammi, take watsa su a cikin kwakwalwarta, take yi musu fahimta ta tsanaki.
Da gaske ne duk abin da Ammin ta fada, da gaske lamarin Ubangiji sai Shi. Allah mai tausayi da jink'an bayinSa.

"Wannan mamakin da yake yawo a saman fuskarki ya kamata ki janye shi MATAR AMEER. Domin kuwa lamarin Allah Ya fi gaban haka."
Ya fada yana kallon ta.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana jin zuciyarta na wani irin girma, soyayyar Ameer wadda ba ta taba zaton ta kai adadin haka ba tana yawatawa a cikin zuciyar tata.

"Ina ka shiga duk tsayin lokacin nan? A wacce duniyar kake Yah Ameer?"

"Ni dai don Allah a canja min suna haka nan. Tun muna yara a Yah Ameer nake, yanzu matsayin ya canzu, na koma Officially MIJIN AMEERAH."
Ya karasa zancen da kanne mata ido daya.

"Ka ba ni amsa ni dai. Me ya sa kake zaune a kan wheelchair?"

Ya daga kafada a hankali ya ce
"Kin ga yanda rayuwa ta yi da ni ko? Rabo na da tafiya shekara bakwai da rabi kenan Ameerah, sai dai a cikin keken nan. Baki daya rayuwata a nan na yi ta tsayin lokacin nan da ba na tare da ke."

Wani irin kuka ta sake fashewa da shi, tausayinshi na ratsa zuciyarta.

"Kina kuka mijinki ya zama musaki ko?"
Ya jefa mata tambayar cikin murmushi.

Gyada kanta ta yi, tana fadin
"A duk yanda ka zo ina maraba da kai Yah Ameer, ko da a cikin halin hauka kake ba zan taba gudunka ba, ba zan kyamaci yanayinka ba. Ganin ka kadai ya sanyaya zuciyata, duk da cewa zuciyata ta jima tana ba ni tabbacin kana raye, za ka kuma dawo duk daren dadewa."

"Na sani...na san ba za ki taba guduna ba Ameerah, na san cewa nak'asata ba za ta shafi soyayyarmu ba."

Sai a yanzu ta samu nasarar sakar masa murmushi, ga hawaye kuma ga farin ciki, ta yi kneel down hade da manne jikinsu wuri guda, fuskarta a saman kirjinshi, suna jin bugun zukatan junansu.

***
FLASH BACK
***

Daddy yana zaune sai kawai ga kira ya shigo masa da wata lambar Nigeria, dama kuma tsumayen kiran Doctor Ashraf yake yi saboda har da lambarsa ya tura masa ta Mail ya kuma ce ya neme shi in dai sakon nan ya riske shi.

Da sallama a bakinshi ya dauki kiran, sai kuwa ga muryar Doctor Ashraf din ya amsa sallama. Farin ciki fal a fuska da zuciyar Daddy ya ce

"My Doctor sai kawai ka bace min b'at ko?"

"Barka da dare Yallabai. Wallahi kaddarori suka yi ta fada min. It's a long story dai."
Doctor Ashraf ya fadi cikin murnar samun Daddy da ya yi.

"Ba ni labari my Doctor, all this while me ya faru da kai? Ina wancan layin naka ya shiga? Na wahala wurin neman ka har na gaji. Kai kuma ya gagara ka sake nema na ko?"

"Yallabai accident na samu wata rana a hanyata ta zuwa Kaduna daga Birnin Kebbi. Na fi shekara guda ina jinya har sai da aka cire rai da samun sauki na, sai kuma daga baya Allah Ya kawo saukin, a lokacin kuma na so yin welcome back na layina amma aka ce an riga an yi blocking layin saboda na jima rabo na da shi. Da na sayi wani kuma ka san IPhone yanda take, ban yi back up na komai daga ICloud ba, babu a email, so komai na yi losing dinsa, komai ya dawo min sabo. Tunda na samu sauki kuma sai kawai aka samo min transfer na dawo gida na ci gaba da aiki. Duk da haka kana raina Yallabai, na bi duk hanyar da ya kamata in same ka amma ban samu ba, shi ya sa ka ji ni shiru tsawon lokaci."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now