Page 68

235 12 0
                                    


Page 68

"Dear reader,

Ban san ga waye sakonnan zai fara isa ba, ban san wanda zai fara karanta shi ba. Sai dai ko ma waye, zan so ya isar da shi ga iyaye da 'yan uwana. Sunana Ameer Nuraddeen, zan yi tafiyar da ba lallai in dawo gare ku ba. Ban san me yake damu na ba, ban san ta yanda za ku fahimci wannan zantukan nawa ba. Sai dai abin da nake so ku gane shi ne bawa ba ya taba tsallake wa kaddararsa. Na san za ku ce me ya sa na yarda da tafiyar bayan kuma hankalina bai kwanta da ita ba? Babu yanda na iya ne. Mr Patric ya bukaci mu yi tafiyar bude ido ni da shi daga nan zai ba ni shawarwarin yanda zan zauna lafiya a AHC tare da samun kyakkyawan rabo. Ina ji a jikina wani abu zai iya samu na wanda takamaimai ba zan ce ga shi ba. Ban sani ba ko hatsarin mota ne ko kuma za mu hadu da 'yan ta'adda. Ko ma dai mene ne za mu yi tafiyar a yau jumu'a. Ina fatan kada wannan zargin nawa ya tabbata. Ina fatan dawowa gare ku cikin koshin lafiya da aminci.

Ameer."

Tuni Ameer da ke sauraron rubutun da ya tabbatar da shi ya yi shi da kanshi wadansu abubuwa suka hau yi masa yawo. Ya kalli fuskar Mr Patric da ya kwabe ta zufa na tsattsafo masa, sannan ya juya ya kalli Gambo da abokan aikinsa, sai kawai ya hau tuna yanda komai ya kasance, munanan kalaman da Mr Patric ya rinka yi masa a kan mahaifinsa suka hau dawo masa. Yana tuna yanda Gambo da yaranshi suke dukanshi da iya karfinsu har zuwa lokacin da ya kasa ko da daga hannunshi ne.
Bai san sadda ruwan hawaye ya hau wanke masa fuska ba. Wata irin tsanar Patric din tana ratsa shi.

Mikewa ya yi da hanzari yana fitowa tsakiyar fili. Hannunshi ya daga hade da fadin
"Ina da magana ya mai shari'a."
Duka idanuwa suka dawo kanshi.

Alkali ya ce
"Muna sauraron ka."

"Na tuna komai ya mai shari'a, wannan wasikar ta sanya ni tuna duk abubuwan da suka wakana..."

Daga nan ya hau labarta musu kaf abubuwan da suka faru tun daga tsarin tafiyar har zuwa sauke Mallam Musa da suka yi shi ya karbi driving, da shigar su daji wurin su Gambo, ya fadi duk maganganun da suka yi tsakaninshi da Patric, da kuma dukan da suka yi masa.

Alkali ya dubi su Gambo da fuskokinsu ke jina-jina ya ce
"Kotu za ta so jin gamsasshen bayani daga gare ku. Shin akwai karya ko karin wani abu daga bakin Ibrahim da Ameer?"

Shashi daya daga cikin yaran Gambo ya ce
"Babu kari a ciki ya mai shari'a sai ma ragi da aka samu. Mu ne nan yaran Mr Patric, yana saka mu aikata kisan kai a duk lokacin da ya ga dama, mun kashe mutane sun fi karfin dari. Abin da mutane ba su gane ba shi ne kwata-kwata Mr Patric ba mutumin kirki ba ne ba kamar yanda yake nunar musu. Daukakar da ya samu kuwa yana kashe duk wanda ya ga suna neman kamo matsayinsa a kamfanin ya kuma batar da duk wani record nasu."

Gambo ya karbe da fadin
"Mr Patric mugun mutumi ne. Duk tsayin shekaru goma sha biyu muna yi masa aiki amma bai taba tunanin cewa wani daga cikinmu ya yi aure ba. Rayuwarmu ta kare a cikin daji kudin ma da yake ba mu ba wani samun morarsu muke yi da kyau ba. Shi kuwa yana can cikin familynshi hankalinshi kwance cikin AC. Idan ma har kotu ba ta yanke masa hukunci daidai da mummunan halinsa ba to da wannan hannuwan nawa zan kashe shi. Ban taba yin tirrr da halin da ya jefa mu ba sai kwanaki uku da suka wuce da aka kama mu. Na fahimci cewa su masu kudin nan kansu kadai suka sani, suna mayar da mu 'yan iskan gari yayin da suke gefe da yaransu suna ba su rayuwa mai kyau. Tir da halinka Patric."

Ya karasa maganar yana dafe kanshi da hannuwanshi guda biyu yana jin wasu irin hawaye masu gumi suna sauko masa.

(Wannan shi ne babban kuskuren da ya'yan talakawa suke yi musamman karnukan siyasa. Za su dage hauka su zama 'yan ta'addan karfi da yaji saboda Oganninsu, su kuwa Ogannin nasu ma ba lallai idan a k'asar yaransu suke ba. Allah Ya sa mu dace amin.)

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now