Page 20

376 16 0
                                    


Page 20

*Alal hakika ke ta daban ce ko a cikin duniyata. Ba zan ce kin fi kowa gare ni ba, ba zan ce kin zarce kowa ba a duniyar rubutuna. Sai dai kina da wata irin daraja wacce ban san yanda zan fasalta ta ba, ban san ma ta inda zan fara ba. Zarah BB, ke din ba k'awa ba ce kadai gare ni, 'yar uwa kike, 'yar uwa mai tarin daraja. Darajarki mai girma ce a cikin duniyata! Wannan shafin naki ne, na sadaukar da shi gare ki.*

***
Cikin rarrashi mahaifiyarshi ke ba shi hakuri, sai dai fa tamkar ba da shi take ba. Ta haggu maganar tata take shiga suruf ta fice ta dama.
"Ka yi hakuri Haidar, na san ba lallai ba ne ka fahimci manufarmu ta son yin auren nan, sai dai ina so ka sani, ni da mahaifinka ba za mu taba cutar da kai ba, ba za mu hada ka da abinda muka san zai zama matsala a rayuwarka ba. Muna da babban dalilinmu na aikata haka."

"Look! Ummi..."

Ido ta zaro tana bin shi da kallon mamaki. D'an da ta haifa da cikinta ne yake mata wannan tsawar haka.

"Kar ku yi forcing dina ga auren wacce ba na so."

"We are not trying to force you Haidar. Kawai abin da nake so ka fahimta shi ne ba za mu aikata dukkan abin da muka san zai iya zama matsala ba ni da mahaifinka. Ka yi hakuri ka rungumi auren Bahijja, in ya so idan muka samu abin da muke nema sai ka auri duk wacce kake so..."

"Ummi." Ya kira sunanta yana sake bin ta da kallo.
"I will not marry anyone  idan ba Ameerah ba. Though she doesn't love me but she must marry me."

"It's not a problem Haidar. I promise you that she must marry you whether she loves you or not. Ni dai burina shi ne ka auri Bahijja a yanzu. Yarinyan ba ta da wata matsala am very sure that you will love her ba dole sai yanzu ba. She is pretty much, very classy girl. 'Yar gayu da ita ga fara'a."

Bai janye idonshi ba daga gare ta, ya ce
"Wai wane irin dalili ne ya sa kuke so na aure ta Ummi? Na tabbata ba za ku kafe a kan dole sai na auri yarinyar da ko ganin ta ban taba yi ba ba tare da wani dalili mai karfi ba. Na san ki, na san Dad, duk abin da kuka san za ku k'aru shi kuke aikatawa."

Murmushi Ummin ta sakar masa,
"Kuma ka san da wannan shi ne kake neman yi mana buk'ulu? Bari in karasa warware maka, ta yiwu za ka fahimci manufarmu da kyau idan ka ji komai."

Kallon ta yake yi ba tare da ya ce komai ba, ba ta jira mai zai ce din ba ta ci gaba da cewa,

"Alhaji Farouk Danfaranshi shi ne mahaifin Bahijja. Ita kadai ce diyarshi duk duniya, ita din ma da kyar da jib'in goshi ya same ta. Sai da ya shafe fiye da shekaru ashirin da aure kafin daga baya ya auri wata 'yar Maiduguri ita ta haifa masa ita. Ba sai na tsaya dogon zance ba, kawai ka yi imagining yanda mutum zai tsinci kansa a lokacin da ya yi shekara ashirin bai samu haihuwa ba sai kuma ya zo ya samu. Ya sadaukar da duk wani lokacinshi gare ta. Ya ba ta gata fiye da tunaninka. Babu k'asar da ba ya kai Bahijja tun tana jinjirarta har zuwa zancen nan da nake maka." Ta dan yi shiru daga nan, tana dorawa da
"Bahijja ta gan ka ta ce tana son ka Haidar. Da ajinta, da kyau da gayun nata duk ta b'arar, ta zo har gidan nan ta nunar da kai take son aure."

Cikin mamaki ya ce
"Amma Ummi ya aka yi ta san ni har ta san gidanmu?"

"Kun hadu ne a Dalema Supermarket kamar yanda ta fada min. Shi ne ta saka one of her security ya bi bayanka har ya gano nan gidan. Da ta zo mai gadi ne ya sanar min isowarta, ta hanyar lambobin motar da take ciki da kuma na biye da ita ya sanya muka gane diyar waye. In a respect manner muka gaisa, sannan take fada min kudurinta game da kai. Ni mamaki ma abun ya ba ni, saboda 'ya'yan gwamnoni da sarakuna ne kadai suka cancanci su aure ta don su ne daidai da ita."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now