Page 67

190 9 0
                                    


Page 67

Alkali Kamaluddini ya kalli Ameerah ya ce
"Kotu na sauraron hujjarki ta gaba. Sannan su Mallam Surajo za su iya komawa su zauna idan da yiwuwar sake ganawa da su za a bukace su."

Bayan sun koma sun zauna Ameerah ta ce
"Ya mai girma mai shari'a, zan so kotu ta bada dama domin a haska majigi, saboda hujjar tawa ta gaba ta kallo ce."

Alkali ya dubi cikin ma'aikatan da ke jere gabanshi ya ba su izinin su hada majigin. Kafin su gama hadawa Ameerah ta ce
"Har ila yau dai ina ba kotun nan mai adalci hakuri a kan mayar da mu baya da nake yi, kasantuwar waccan shari'ar komai ya zo mana a jagule ne ya sanya yanzu komai yake komawa baya saboda warware kawuna daga duhu."

Alkali Kamaluddini ya jinjina kai alamun gamsuwa sannan ya dora da
"Kotu na maraba da duk wata hujja taki in dai gamsasshiya ce. Sannan lauyoyi masu kare wanda ake kara ku ma kuna da damar yin suka ga hujjar da ba ta yi muku ba."

A daidai lokacin aka gama hada majigin. Ameerah ta mika wayarta suka jona da ita, sannan da kanta ta gano videonsu da Kabiru inda ya dage yana ta warware musu duk yanda lamurran suka faru.

Idanuwan mutane na kan majigin har zuwa lokacin da ya kai aya. Mamaki karara a fuskokin mutane, John da Moses sai keta zufa suke. Sun sa an kama musu Kabiru an tafi da shi an boye ashe a banza aikin gama ya riga ya gama. A wannan gabar sosai suka fara karaya. Sai dai da yake dukkansu tsofaffin barristers ne sai ba su nuna yanda za a iya gane cewa they are discouraged ba.

Bayan an gama kallo duka Ameerah ta zare wayarta sannan ta bada izinin a kashe majigin. Ta juya ga alkali ta ce
"Ya mai girma mai shari'a, ina fatan da wannan hujjar kotu za ta kara gasgata zancen Kamal Karofi da kuma iyayen Ibrahim Surajo, sannan ina fatan kotu za ta yi watsi da hujjar da lauyoyin da ke kare wanda ake kara suka kawo dangane da cewa karatun Ibrahim da Kamal na bogi ne shi ya sa aka kore su daga aiki. Wannan zai kara tabbatar wa kotu da cewa dalilin da ya sanya aka kore wadannan bayin Allah daga aiki a AHC shi ne don kar su tona wa Mr Patric asiri saboda an san su kadai ne suke da alaka da Ameer sosai a duk kamfanin. Na gode ya mai shari'a."

Ta koma ta zauna tana sakin murmushi. Hada ido suka yi da Ameer shi ma ya sakar mata murmushin hade da kara mata kwarin guiwa.

Alkali ya kalli su John ya ce
"Barrister John ko kuna da wani bayani dangane da abin da aka haska yanzu a majigi?"

Moses ya mike hade da fitowa fili ya ce
"Eh ina da shi ya kai shari'a."

"Kotu ta ba ka dama."
Alkalin ya fada idanuwanshi kyam a kansa.

"Ya mai girma mai shari'a, a cikin mutane uku da muka gabatar mutum daya ne kacal aka samu ya yi wadannan zantukan. Sannan idan da gaske ne yana ina yanzu? Ina so kotu mai adalci da ta yi duba ta tsanaki, domin kuwa a kan kudi Kabiru zai iya yin komai..."

Ameerah ta mike hade da daga hannunta tana son yin magana amma alkali ya dakatar da ita,
"Ki bari har ya gama fadin abin da zai fada sannan."

Komawa ta yi ta zauna ba don ta ji dadi ba saboda amsar da take son ba shi ba ta son ta kufce mata a daidai wannan gabar.

Ya ci gaba da cewa
"Tunda har ba duk shaidunmu ne suka fadi haka ba bai kamata wannan kotun mai adalci ta yi la'akari da zancen Kabiru kadai ba. Na gode ya mai shari'a."

Ya koma ya zauna.
"Barrister Ameerah za ki iya yin magana."
Alkalin ya fada yana kallon ta. Ta taka a hankali ta fito sannan ta ce

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now