Page 43

217 15 0
                                    


Page 43

Cikin azama Labiba ta yi kanshi, a tsorace take saboda bai taba yin irin haka ba, tunda ciwonsa yake tashi bai taba sumewa ba, sai dai kakkafewar nan yana convulsion kamar yanda ya saba. Ga shi ita kuma ba ta da ilmin wannan fannin.

Allurarshi ta dauko ta tsiyaya a sirinji, sai dai ta tsaya ta kasa yi masa ita saboda babu amfanin yin, ana yin ta ne saboda ya samu barci ko da zai tashi babu ciwon, to a yanzu kuma ba ma a farke yake ba ya suma.

Ta latsa kiran Daddy har ta tsinke bai dauka ba, dama kuma ya fada mata zai yi meeting da wasu da zai yi ma contract.
Ta kira Doctor Awwal bayan ya dauka ta shaida masa abin da ya faru.

"Wannan kuma wani ciwo ne na daban Labiba, ba fannina ba ne. Ki kira Doctor Lucas ko kuma ki kai shi asibiti wurinshi."

"Okay Doctor."
Ta fada cikin wata irin murya.

Kiran Doctor Lucas ta latsa, bayan ya dauka ta zayyane masa abin da ya faru. Cewa ya yi ta gaggauta kawo shi asibiti, sannan a karshe ya kwantar mata da hankali cewa ta yiwu wani karin ci gaban ne aka samu.

Leo ta kira ya zo da hanzari, rabon da ciwon Ameer ya tashi a kai shi asibiti an jima, duk sadda zai tashi Labiba ce take kula da shi, amma ga shi yau abun ya fi karfinta.

Sungumar Ameer ya yi yana gaba Labiba na biye da shi, ta dauko makullin mota da purse dinta sannan ta bude masa motar ya kwantar da Ameer.
A rikice take tukin motar tana yi tana waigen Ameer da har yanzu ko motsi ba ya yi. Cikin minti talatin suka isa asibitin saboda gudun da take tsugagawa.

Da sauri ta kira ma'aikatan suka dora shi kan gado, kai tsaye Office din Doctor Lucas ta nufa suna mara mata baya.

A kan gadon duba marassa lafiya suka kwantar da shi, Doctor Lucas ya sauke madaidaicin labulen yanda babu wanda zai iya ganin shi. Cikin kwarewa ya hau duba Ameer din, bayan minti kadan ya fito ya samu Labiba ta kasa tsaye ta kasa zaune sai zufa take yi duk da sanyin da ke fita daga AC din dakin.

Rubutu ya yi a wata 'yar takarda ya mika mata ya ce ta je ta sayo wata allura da sauri. Bayan ta karba ta nufi pharmacy ta sayo allurar hade da sirinji. Da gaggawa ta koma office din ta ba shi.

Wurin Ameer ya koma ya yi masa allurar, a take ya sauke wani irin nannauyan ajiyar zuciya ya dan bude idonshi sannan ya sake rufewa.
Shi ma Doctor Lucas din ajiyar zuciyar ya sauke sannan ya fito da annuri a fuskarshi ya zauna kan kujerarshi.

"Da alama akwai nasara."
Ya fada cikin harshen turanci yana kallon Labiba da duk ta rikice tashin hankali ya bayyana k'arara a fuskarta.

"Am sure zai tashi da tuna wadansu abubuwan na daga rayuwarshi. Kwakwalwarshi ta dan hargitsa ne sanadiyyar wasu abubuwa da ya tuna, hargitsewar nan da ya yi shi ya sanya hankalinshi ya tashi har ya suma. A irin wannan matsalar tashi dama dole sai hakan ta kasance in dai zai dawo da memory dinsa. To sai ki gode ma Allah don da alama kaso mai tsoka na rayuwarshi ta baya zai dawo masa."

Hamdala hade da ruwan hawaye ta sauke a lokaci guda, tana kara godiya ga Allah da Ya nuna mata wannan ranar.

Awa biyar ya yi yana barcin ya farfado. Da kanshi ya tashi kishingide yana dudduba ceiling yana tunanin a inda yake. Jin motsinshi ya sanya Doctor Lucas ya zo wurinshi, da annuri ya ba shi hannu suka gaisa sannan ya fita waje ya kira Labiba da ke tare da Leo a reception. Labiba na ganin shi ta yi saurin mikewa ta nufi inda yake.
A tare suka shiga office din tare da nufar kan gadon da Ameer yake.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now