Page 69

224 8 0
                                    


Page 69

Tun daga nan SS suka hau bincike ba tare da ko 'yan sanda sun sani ba. Kuma duk abin nan da suke yi tare suke yin sa da Daddy. Da yamma likis suka samu nasarar shiga cikin dajin hanyar zuru wanda ta nan ne Daddy ya tsinci Ameer. Rarrabuwa suka yi saboda dazuzzukan wurin suna da girma sosai.

Sun sha wahala sosai don har sai da dare ya yi suna shirin tafiya wasu daga cikin ma'aikatan suka kira Ogan cewa ga su nan sun samu nasarar cafke duka 'yan ta'addar har ma da Ibrahim da ke kwance yana bacci.
Ba karamin jin dadin wannan nasarar da suka yi ba Alhaji Sardauna ya yi.

A wani irin kebantaccen wuri ne aka kai su, inda suka kara tabbatar wa SS din da halayen Mr Patric. Shi ne aka umurci Gambo da kar ya kuskura ko da wasa ya nuna wa Mr Patric din komai, wayarshi na hannun daya daga cikin masu tsaron shi, duk sadda ya kira zai ba shi su yi magana kamar yanda suka saba.

A bangaren Barrister Jani kuwa a ACH ya fara nashi binciken, inda tun daga kan kananan ma'aikata har zuwa manya ya hau binciken yanayin mu'amalar Patric din da mutane sai dai amsa daya ake ba shi cewa mutumin kirki ne mai fara'a. Ya binciki asalin wanda yake kan kujerar GM nan aka shaida masa wani Matawalle ne dan nan cikin Birnin Kebbi. Bai wani sha wahalar neman iyalin Matawalle ba suka shaida masa ai kashe shi aka yi da guba a cikin shayi, kuma sun tabbatar da cewa daga kamfanin da yake aiki ne. Ya yi bincike tsaf a kan duk wasu masu matsayi da suke barin aiki a kamfanin wasu kuma suke rasa rayukansu cewa sun dauko samun wani babban matsayi ne.

Hakan ya kara tabbatar masa da cewa kisan gilla Mr Patric yake aikatawa duk don kar ma wani ya taddo shi matsayi.

Barrister Jani ya samu Daddy da zancen shi ne ya ba shi labarin halin da ake ciki, ya kuma ba shi tabbacin komai ya zo karshe.
Ibrahim kuwa sun sha kuka shi da Sufyan sadda suka hadu. Sun so a tsaftace shi sai dai Barrister Jani ya ce zai fi kyautuwa a daure ya ci gaba da zama a haka har zuwa ranar zaman kotu, zuwan shi a haka shi zai kara inganta musu hujjar tasu.

Daddyn Labiba ya kira Ameerah ya shaida mata halin da ake ciki. Ta ji dadi sosai ta kuma kara jinjina wa mutunci irin na wannan bawan Allah. A karshe ya ce mata ta yi shiru da zancen har sai an shiga kotu yanda kowa abun zai zo masa baghtatan. Ta yi na'am da shawarar tashi daga nan ta masa sallama hade da yanke kiran.

Wannan kenan.
Back to our story.

Wani irin lunch ne aka shirya mai cike da kayan more rayuwa. Su Ameer, Sufyan, Kamal, da kuma Ibrahim tare suka zuba hadaddiyar fried rice din da ke lullube da pepper chicken da salad. Suna ci suna nishadi ana tada labaran baya.

Bayan sun gama duka Daddyn Labiba ya yi gyaran murya, hakan ya sa duk suka saurara suna mayar da hankulansu gare shi.

"Ina mai kara godiya ga Allah madaukakin Sarki da faruwar wannan al'amari. Sannan ina mika sakon jaje tare da ban hakuri gare mu baki daya, domin kuwa duk abubuwan nan da suka faru kamfanina ne silarsu. Na ji dadi kwarai da Allah Ya bayyana min gaskiya, Ya bayyana wa duniya baki daya cewa mutumin da muke wa kallon na kirki ba fa na kirkin ba ne kasurgumin dan ta'adda ne. A yanzu da gaskiya ta yi halinta, ba tare da neman shawarar kowa ba na yanke hukunci, wanda nake fatan dukkanmu nan za mu karbe shi da hannu bibbiyu. Muhammad Ameer..."
Ya juya ya kalli Ameer da shi din ma shi yake kallo. Ya ci gaba da cewa
"Na yanke shawarar kai ne za ka zama sabon General Manager na AMAL HOUSING COMPANY. Ma'ana ga baki daya kamfanin zai koma a karkashin kulawa da ikonka."
Dukkansu kallon Daddy suke yi, Ameer ya kasa rufe bakinshi saboda tsananin nauyin da yake ji na hukuncin Daddy. A zahirin gaskiya wannan matsayin ya yi masa girma, ba ya ji da shi ya dace. Shi baki daya ma tsoron aiki a kamfanin yake yi. Bai gama tunanin da yake yi ba ya ji Daddy ya ci gaba da cewa
"Kamal, Sufyan, da kuma Ibrahim, dukkanku za ku koma aikinku tare da matsayi mai girma. Kodayake ni ba zan yanke wannan hukuncin ba, abokinku da ya kasance shugaba a kamfanin shi zai zabi matsayin da ya dace da ku ya ba ku."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now