Page 52

239 12 0
                                    

Page 52

Wani irin mamaki ne ya kama Ameerah, domin ita dai har ga Allah ba ta ga alamun wadannan kyawawan halayen da Daddy ya lissafa tattare da Mr. Patric ba. Sam-sam bai da zubin mutanen kwarai.

"Da gaske yana da mutunci, saboda ba zan manta ba kafin duk wani abu ya faru da ni sosai ya kyautata min. Har ma ya ce zan raka shi shakatawa daga nan zai ba ni kyawawan shawarwari wadanda za su sanya ni jin dadin zama a AHC."

"Kun je?"
Ameerah ta gaggauta jefa masa tambaya.

"Ban sani ba Meerah. Ban sake sanin komai ba, ba zan iya ce miki ga wani abu ba baya ga cewa za mu yi tafiya."

"Shi kenan. Mu dai dage da addu'a in shaa Allahu nasara tana tare da mu."

Cikin annuri Daddy ya ce
"Da izinin Ubangiji kuwa."

Ameer ya kalli Ameerah ya ce
"Kamar maghrib ce ake kira. Mu tafi gida ko?"

Ta jinjina masa kai. Sallama suka yi da Daddy, ya ce zai koma ciki ya yi alwalla sannan ya fito ya je masallaci.

Tura Ameer take yi za su nufi inda motarsu take a parking space keken ya kufce mata ya tafi babu burki tare da nufar wani matashi da ke sanye da mataccen jeans da farar rigar da ta koma light brown saboda datti.

Cikin azama Ameer ya take burkin keken ya samu ya daidaita shi.
Gabanta ne ya yi mummunan faduwa, ita ba ta ma san yanda aka yi ta zurfafa a tunani ba har keken ya kwace mata.

Hakuri suka hau ba matashin da ke rike da dogon brush na shara dayan hannunshi kuma bokitin mopping.

Yana dago kanshi ya kalle ta sai da gabanta ya fadi. Tunanin a inda ta san shi ta hau yi sai dai ta rasa. Hakan ya sanya ta gaggawar janye idonta daga gare shi tana istighfaari.

Shi kuwa bai daina kallon nata ba sai ma kara kusantowa da ya yi inda take.

Ganin kallon-kallon da suke aika ma junansu ya sanya Ameer daure fuska yana fadin
"Mu je mana."

Kafin ta daidaita hannunta bisa kenan matashin da idanuwanshi suka cika da kwalla ya ce

"Ameerah!"

Kallon mamaki take masa, kafin ta ji ya ci gaba da fadin

"Na san ba ki gane ni ba. Sunana Haidar Makarfi."

Ido ta fiddo waje tana sake bin shi da kallo. Da yatsa take nuna shi, da kyar ta iya fadin
"Haidar? Kai ne...kai ne ka koma haka?"

Kwallar da ke makale a cikin idonshi ce ta sauko. Ameer dai ya yi facing front dinshi sai tafarfasa zuciyarshi ke yi.

"Ni ne, ni ne da kaina Ameerah. Kin ga yanda rayuwa ta yi da ni ko? Kin ga na zama ma'aikacin hotel."
Ya saki guntun murmushin da iyakacinshi bisa lebo.
"Duk da juyewar da duniya ta yi da ni har yanzu ina son ki Ameerah."

A fusace Ameer ya sa duka hannuwanshi yana janye na Ameerah da ke kan handle na wheelchair dinshi. Cikin bacin rai ya murza da kanshi ya ci gaba da tukawa kamar yanda ya saba da kanshi.

Idonta cike da hawaye ta kalli Haidar sannan ta bi Ameer da kallo.
Kafin ta ce komai Haidar ya ce

"Ki je ki rarrashi mijinki na san abin da yake ji. Ki fada masa cewa a da can da nake da matsayi ma ba ki so ni ba balle yanzu da na zama kaskantaccen mutum mai shara da goge-goge a hotel. Ki ba shi hakuri, babu abin da za ki yi da mutum kamar ni Ameerah. Na so ki, kuma har yanzu soyayyarki na nan a cikin zuciyata. Ina miki fatan alkhairi."
Daga haka ya bar wurin yana share kwallarsa.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now