Page 58

202 10 0
                                    


Page 58

Mr Patric ya tattauna sosai shi da Barrister John, suna cikin magana ma Barrister Moses ya zo don ya kira Mr Patric din ya fada ma sa ya gama abin da yake yi ga shi nan zuwa. Tare ya ci gaba da ba su labarin duk abin da ya faru, babu ko A da ya rage a ciki saboda sun nunar masa da cewa duk abin da ya lullube bai bude musu ba zai iya jawo matsala a zaman kotu. Gwara su san komai don su san ta hanyar magance shi.

Tabbatar masa suka yi cewa komai zai tafi yanda suke so. Sannan su duka biyun za su zama masu kare shi. Babu wani karamin alhaki da zai iya kada su a wannan karamin case din wanda babu wata budaddiyar hanya da Mr Patric ya bari wacce za a iya gane shi.

Million goma ya ba su sannan ya ba su tabbacin idan har suka yi nasara a case din zai ba su wata million gomar. Wannan lamari ya yi musu dadi kwarai da gaske. Don haka suka yi alwashin tsayawa a bisa kafafuwansu da kyau wurin ganin sun yi aikin da ya dace.

***
Saddam na zaune a Office dinsu ya latsa kiran Gimbiya Amrah. Cike da farin ciki ta dauka, ya gaishe ta cikin girmamawa sannan ya tambayi mai martaba.

"Yana lafiya Muhammad. Ya tafi Saudia amma muna sa ran dawowar shi sati mai zuwa."

"Allah Ya dawo da shi lafiya."
Saddam ya fada yana son dorawa da zancen aurenshi sai dai nauyi yake ji.

"Ya wurin su Maman ta su Musaddiq? An kwana biyu ba mu gaisa ba ko a waya. Zan yi kokari idan mai martaba ya zo mu zo muku har gida, tunda an yi biki ba a gayyace mu ba sai daga baya muke jin labari."

Ya yi murmushi sannan a hankali ya ce
"Dama na kira ne in fada muku..."
Sai kuma ya yi shiru wata irin kunya yake jin tana lullube shi. Bai dauka cewa duk confidence dinshi zai iya neman shi ya rasa ba.

"Go on my Muhammad. Lafiya dai ko?"

"Uhm lafiya kalau."

"To fada min ka ji? Ko mun yi daughter in-law ne?"
Ta tambaye shi tana murmushi.

"Eh shi ne dalilin kiran. Ku ne iyayena ku ya kamata na fara fada wa. Saboda ko na fada ma Daddyna cewa zai yi shi babu ruwanshi, mai martaba ne mai neman auren."

Hamdala ta saki tare da fadin
"Na ji dadi yarona ya girma."

Ya saki murmushi yana sake jin nauyinta.

"Yar wane gari ce?"
Ta jefa masa tambaya.

"Yan asalin jihar Kebbi ne amma ba a kasar nan suke zaune ba. Su ne wanda Yaya Ameer wanda ya auri Aunty Ameerah ya yi rayuwa a gidansu. Sadda suka dawo da shi gida ne muka fara gaisawa da ita. Sunanta Labiba."

Da annuri Gimbiya Amrah ta ce
"Wow! Gaskiya na ji dadi sosai. Idan har gidan su yarinyar sun shirya yi mata aure mu ma a shirye muke da mu aurar da yaronmu tunda yana aikinsa. Don haka a yau din nan zan sanar da mai martaba a waya. In ya so sai in kira ka daga baya, idan ta kama sai ka turo lambar wayar mahaifinta, su fara yin maganar a waya kafin a san ranar ganawarsu."

Wani irin farin ciki ne ya lullube shi. Bai san sadda ya furta
"Thank you so much." Ba.

"Ba na hana ka wannan godiyar ba Muhammad?"

"A yi hakuri ba zan sake ba."

"Good boy. Allah Ya yi maka albarka."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now