Page 66

198 9 0
                                    


Page 66

Ana gobe za a shiga kotu Ameerah na tare da Ameer a dakinta da dare ta ce
"Ka san me cheri? Kawai jikina ba ya ba ni Kabiru zai je kotu. Zai yi kokari ya tsira da dubu dari biyar dinsa ne."

"Kike gani? Amma fa har shagon da yake kwana muka same shi. Ya kuma san mun san wurin."

Dariya Ameerah ta yi ta ce
"Ba ka san halin mutane ba. Wannan yana da zubin 'yan duniya sosai. Ni dai kawai a gani na ba zai je ba."

"To ai ko bai zo ba da sauki tunda muna da recording."
Ya fadi yana murmushi.

"Ku recording kuke da shi to ni video gare ni."

Cike da mamaki Ameer ya kwalalo ido yana kallon ta. Ta ce
"Duk zaman nan da muka yi Ammi na daga dakin Daddy ta saita ta window tana daukar komai. Sai dai ba sosai voice din ya fito ba."

"Alhamdulillahi kai amma dai na ji dadi. Me ya sa ba ki fada min da wuri ba ai da mun samu masu editing su jona voice dinmu da na video din yanda zai tafi daidai."

"Kuma fa haka ne cheri. Yanzu an makara ne?"

Shiru ya yi yana laluben lambar Khalil a wayarshi. Bayan ya dauka ya tambaye shi ko akwai wani expert da ya sani mai video editing.
"Eh akwai kuwa don shi editing din films ma yake yi. Bari in kira shi Allah Ya sa he is less busy. In fada masa zuwa da asuba muke son shi."

"Yawwa Khalili. Please try your very best ka ga mun samu abun nan. Hakan zai kara taimaka ma shari'ar nan."

"Alright Yaya Ameer in shaa Allahu za a yi. Kawai ka tura min su ta whatsapp in ya so ko da ba mu samu wancan din ba sai a nemi wani."

"Zan turo maka audio din. Video kuma da wayar Meerah za ka gan shi."
Ameer ya fada hade da yanke wayar. Ameerah ta tura ma Khalil videon wayarta duk da tana da nauyi sosai don kusan minti talatin ce, Ameer ma ya tura nashi.

"Daddy ya ce gobe a Abujar za mu hadu. Na yi na yi da shi ya fada min halin da ake ciki ya k'i, amma dai ya tabbatar min da cewa a gobe komai zai zo karshe da izinin Allah. Da confidence dinshi fa yake magana."
Ya karasa zancen da dariya.

"Akwai alamun nasara kam Yah Ameer. Ni kaina abin da nake ji yanzu sam-sam ban ji shi a waccan shari'ar ba. Ka san fa waccan haka nan na shige ta ba ni da komai a hannu sai addu'a. Amma a yanzu ka ga muna da manya-manyan hujjojin da in shaa Allahu ko da su kadai za mu iya samun nasara."

"Can't wait for tomorrow."
Ya fada hade da rungume Ameerah tsam-tsam a jikinsa.
"Amma dai ana gama shari'a ai za ki dawo gida ko? Am missing you there wallahi."
Ya fada yana dan yamutsa fuska.

"Kai cheri kullum fa muna tare a nan."
Ta yi murmushi tana wasa da yatsunshi.

"Ke ma fa kin san da bambanci baby. A nan iyakacina jinyarki. A can kuma..."

Sai ya yi shiru yana kokarin zira hannunshi a cikin rigarta. Da sauri ta rike hannunshi tana fadin
"Yah Ameer kar fa a shigo, kuma ka san Saddam duk sadda ya ga dama shigowa kawai yake yi."

Bai daina zira hannun nashi ba ya ce
"To sai me? Shi ma ai ya kusa hawa wannan sahun ya gane irin abin da muke ji."

"A'a ni dai. To Ammi kuma fa? Ka san za ta iya zuwa ta kawo min kunu at any time."
Ta fadi tana turo baki.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now