Page 39

176 13 0
                                    


Page 39

Shirye-shiryen biki sun kankama sosai, bangaren amare kuwa sun sha gyara irin na 'yan Sudan, Hajiya Amna da kanta ta zo ta gyara amaren da kayan kamshinta SUDANESE SCENTS. Kamshi ne irin mai kama fata, mai shiga cikin jiki sosai. Babu wanda zai gitta ta inda suke ba tare da ya shaki daddad'an kamshin nasu ba.
(Masu son Sudanese Scents tun daga kan turaren wuta, turarukan wanka, kulacca da sauransu su tuntubi Amna a lambar wayarta +234 902 780 3248).

Ita dai Ameerah kallo ne kawai nata, komai sai an ce mata ta yi sannan take yi. Kullum da dare sai ta sha kukanta ta gode wa Allah kafin bacci ya dauke ta. Ciwon kai kuwa da shi take kwana da shi take wuni, ga yawan kuka ga karancin bacci su ne suka hadu wuri guda suka sanya mata ciwon kan.

Sun je sun yi rabon invitation ita da Husna, ba wasu mutane masu yawa ne suka kai mawa ba, kawayen karatunta ne kawai sai su Sarah. Har gidan Bahijja ta je ta kai mata. Lokacin da Bahijja ta duba IV din cewa ta yi

'Gaskiya Ameerah ba ki da kirki. Yanzu za ki yi aure shi ne sai da ya rage kwana sha daya sannan zan sani? Aminci bai ce haka ba.'

Murmushi kawai Ameerar ta mata, ta haka ne ta fahimci cewa ba don tana so za ta yi auren ba, da alama rashin sanin madafa ne ya sanya za ta yi.

Tana zaune a daki ta yi nisa da tunani Sumayya ta shigo, wayarta ta nuna mata cikin farin ciki tana fadin
"Duba ki gani Aunty, wannan decoration din ya yi kyau ko?"

Ta dai dora idonta a kan screen din wayar, amma Allah Ya sani ba wani gani ta yi ba.
Ta daga mata kai da murmushi ta ce
"Eh ya yi sosai ma."

Murmushi ita ma Sumayyar ta yi da fadin
"Na kunshinmu ne har an yi."

Ido Ameerah ta kwalalo cikin mamaki ta ce
"Ke Sumayya wannan wane irin d'oki ne haka tun saura kwana uku har an yi decoration?"

"Aunty ni din fa ban san yanda aka yi ba, yanzu kawai ya turo min wai har an yi."
Ta fadi tana dan turo baki.

"Allah Ya shirya ku ke da Marwan din. Saukinku ma ba open place ba ne ai da iska ya gama bata shi kafin ranar."

"Eh kam a hall ne gaskiya."

"To barkanku."
Ameerah ta fada tana jawo wayarta da ke ringing.

Sunan Bahijja ta gani a rubuce ya sa ta gaggauta dauka.

"Kawata amarya."
Bahijja ta fada cikin sigar tsokana.

"To yasin zan yi zagi."

"Ki yi mana."

"Kawai dai babu kyau zagi ai da na babbanka shi."

Suka yi dariya su duka.

"Ina ta jiran ku fa."

"Wallahi Husna nake jira Bahijja, da ta zo in shaa Allahu za ki gan mu."

"To ai na san halin amare ne, idan suka shiga rububi ma sai su manta da wani zancen. Ga shi na hana diyarku zuwa school saboda ita ma mu je a yi mata saloon din."

"Kai! Gaskiya Bahijja ba ki da M. Yanzu diyar tawa ce za ki kai a saka cikin dryer dan tsabar zalunci?"

Dariya sosai Bahijja ta yi kafin ta ce
"Yo ai ta saba in dai wannan ce. Kar ki damu ai da hand dryer aka saba yi mata amfani."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now