Page 47

227 19 0
                                    


Page 47

Daga Ameer din har Labiba mutuwar zaune suka yi. Su khadija kuwa ba su san abin da ya faru ba suna daga can kusa da tv stand suna kallo.

Ita kuwa Ameerah ko a jikinta, sai ma dadi da ta ji saboda karantar damuwar da ta yi a fuskar Labiba, gwara ita ma din ta ji kwatankwacin abin da take ji tunda suka shigo gidan.

Freezer ta bude babu komai a cikinta ta mayar ta rufe, sannan ta bude gefen fridge, sauran namansu na jiya ne kadai a ciki sai lemu da ruwa da ke jere. Ta hau nazarin ta ina ma za ta fara tunda ko kayan miya ba ta da shi. A take wata dubara ta fado mata. Sauran danderun jiya ta ciro daga fridge din ta ajiye a gefe.
Sannan ta duba cikin kayan gararta akwai dakakken yaji da su kuka, daddawa, kubewa da dauransu. Dakakken yajin ta bude ta debi kadan ta zuba a cikin tukunya, ta zuba mai ma kadan sannan ta sheka ruwa a ciki ta kunna gas din.
Curry da maggi kadai ta zuba dan saboda pasta ba ta son yawan spices. Bayan ruwan ya tafasa ta kakkarya taliyar ta zuba a ciki, ta dandana komai ya ji sannan ta rufe.
Danderun ta saka a microwave ta yi warming dinta kamar a lokacin ne aka dafa ta.
Taliyar na dahuwa ta debi daidai tasu ita da Ameer a cikin wani makimancin plate mai dan zurfi, sannan ta raba danderun kashi biyu ta zuba musu rabi, ta dauki fork guda biyu ta nufi parlor.

Har a lokacin Labiba da Ameer sun kasa cewa komai, shi kam baki daya ma kunya ce ta kama shi, saboda cin fuskar da Ameerar ta yi mata.

"Cheri ga shi na kammala saura ci."
Ta furta tana satar kallon Labiba da ta yi kasak'e tana jin da na sanin zuwa gidan ma duka.
Sannan ta mayar da dubanta ga su Khadija da suka dage gardamar abin da za a yi next a Jodha Akbar, ta ce
"Fauzah ku je kitchen ku zuba abinci."
Ta sake kallon Labiba murmushi na kwace mata ta ce
"Hajiya Labiba idan za ki ci favorite food din Yah Ameer ga shi can na kammala."

Gyada kai Labiba ta yi cikin sanyin murya ta ce
"Alhamdulillah."
Tana mikewa.
Khadija da Fauzah ta kalla ta ce
"Zan koma gidan Umma. Sai kun zo."

Ameer ya yi gaggawar dakatar da ita ta hanyar fadin
"Ina kika sani da za ki tafi ke kadai? Ban yarda ba, ki jira su gama ku tafi tare kamar yanda kuka zo."

A tare Labibar da Ameerah suka kalle shi, kowacce da tunanin da take yi.

Ya daga mata kai yana kallon ta,
"Ba ki san yanda duniya take abun tsoro ba yanzu? Waye ya fada miki Nigeria daya take da Canada? Ki jira su gama ku tafi tare, it's an order!"

"Yah Muhammad..."

"I insist."
Ya fada yana janye dubanshi daga gare ta.

Ameerah kuwa mutuwar zaune ta yi, wani irin takaici na lullube zuciyarta, tana jin cewa idan ba ta bar falon ba to zuciyarta za ta iya bugawa. Ya fi kowa sanin ta, ya san tana da zafin kishi a kanshi.

Abincin da ba ta tsaya ta ci ba kenan fuuuuu ta wuce daki.

Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin rigimar Ameerah. Bai ma san ta inda zai fara rarrasarta ba. Amma dai rarrashinta abu ne mai sauki a kan Labibar ta tafi bayan babu inda ta sani a garin.

Shiru ya ratsa tsakaninsu sai Khadija da Fauzah da suka nufi kitchen. Taliyar suka zuba a makimancin tray sannan suka dora danderun kazar a kai, Khadija ta dauki fork guda uku ta bi bayan Fauza.

"Aunty Labiba sauko ga abincin."

Kai kawai ta gyada musu alamun ba za ta ci ba.
"Ke dan Allah Aunty Labiba ba ki fa ci komai ba banda tea din safe da kika sha. Haba mana. To ko shinkafar za ki ci?"

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now